Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce yana fatan karfafa hadin kai da Kungiyar Hadin Kan Kasashen Shanghai (SCO), inda ya kira ta da “mai wakiltar al’adar neman mafitar hadin gwiwa ga matsaloli.”
Da yake jawabi a wajen Taron Shugabannin Kasashe Mambobin SCO karo na 25 a birnin Tianjin na China a ranar Litinin, Erdogan ya bayyana kungiyar a matsayin “muhimmiya” wajen haɓaka ƙawance a fannin makamashi da samar da kayan more rayuwa.
Ya kuma yi maraba da matakan baya bayan nan da ke da manufar samar da dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kudancin Caucasia da Tsakiyar Asiya.
Taron na SCO na wuni biyu, da aka fara a ranar Lahadi, ya zama taro shekara-shekara karo na biyar da China ta karbi bakunci tun bayan kafa ƙungiyar a 2001.
Tun da fari, Erdogan ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a gefen babban taron.
'Nauyin bai-ɗaya da ke wuyanmu'
A yayin da yake magana kan rikice-rikice a duniya, Erdogan ya soki tashe-tashen hankula a Gaza.
"Babu wani uzuri na gaza dakatar da kisan gillar da aka shafe watanni 23 ana yi a Gaza, inda jarirai, yara, da tsofaffi ke mutuwa saboda yunwa," in ji shi.
Ya yi kira ga kasashen duniya da su yi amfani da Majalisar Dinkin Duniya a matsayin wani dandali na tabbatar da adalci a duniya, yana mai bayyana ta a matsayin "nauyin bai daya da ke wuyanmu" don mayar da martani ga zaluncin da ake yi wa al'ummar Falasdinu tsawon shekaru.
Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 63,500 a Gaza tun daga watan Oktoban 2023. Yakin Isra'ila ya lalata yankin da ke fuskantar yunwa.
Dangane da Syria, Erdogan ya jaddada ci gaba da bayar da goyon baya ga farfado da kasar tare da kiyaye iyakokinta da hadin kan siyasa, yana mai cewa irin wannan kokari na amfanar daukacin yankin.
Ya kuma kara nanata cewa, Turkiyya za ta yi adawa da duk wani yunkuri da ke barazana ga tsaro ko ‘yancin mulkin kasar Syria.
A karshe Erdogan ya bayyana ra'ayin Turkiyya game da manufofin ƙetare, inda ya jaddada muhimmancin tattaunawa, diflomasiyya, da hadin gwiwa bisa mutunta 'yancin kai da yankunan dukkan kasashe.
Ya bayyana muhimmancin ci gaba a fannin makamashi da haɗin kai don zaman lafiyar duniya, cigaban tattalin arziki, da cigaba mai ɗorewa.