Matatar mai ta Dangote ta ƙaryata rahoton da ke cewa za ta iya rufe matatar mai na tsawon watanni biyu zuwa uku, kamar yadda mai magana da yawun rukunin kamfanin na Dangote Anthony Chiejina ya bayyana rahoton a matsayin "tsantsar ƙarya" wadda ba ta da tushe balle makama.
A wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar, ya bayyana cewa, ‘‘akwai yiwuwar rufe sashen matatar man kamfanin wadda ke samar da ganga 650,000 a kowace rana tsawon watanni biyu zuwa uku saboda yin wasu gyare-gyare, yana mai ambato shawarar da masana'antar IIR Energy da ke sa ido kan makamashi ta bayar.
A cewar rahoton, tun daga ranar 29 ga watan Agusta aka yi ikirarin rufe sashen matatar man bayan da aka samu matsala ta kwararar mai daga ɓangaren tace man masana’antar.
Kazalika rahoton ya ƙara da cewa, matatar za ta yi ƙoƙarin sake soma aikin tace mai na ganga 204,000 a kowace rana daga 20 ga watan Satumba, amma manyan gyare-gyare da kuma sauya wasu kayan aiki ka iya sanyawa a rufe ta tsawon wasu watanni.
Da yake mayar da martani kan rahoton, Anthony Chiejina, ya bayyana ikirarin a matsayin "labarin karya," kana ya aza ayar tambaya kan dalilin da ya sa Reuters zai yi amfani da kalmar ‘yiwuwa’ idan har yana da tabbaci kan shirin rufewar matatar, kamar yadda ya shaidawa jaridar Punch a ranar Lahadi.
Kamfanin dillancin labaran Reuters dai ya bayar da rahoton cewa ana sa ran rufe sashen kamfanin Dangote na RFCCU na aƙalla makonni biyu.
Matatar mai ta Dangote, wadda ta soma sarrafa ɗanyen mai a watan Janairun 2024, ta sauƙaƙa harkokin mai na cikin gida tare da da kawo cikas ga harkar cinikayyar fitar da man fetur daga ƙasashen Turai zuwa yamma.
Kazalika kasuwancin fitar da man fetur daga ƙasashen Turai da Birtaniya zuwa Nijeriya ya ragu daga ganga kusan 200,000 a shekarar 2024 zuwa kusan 120,000 a watanni shidan farko na wannan shekara ta 2025, a cewar kafar tattara bayanai ta Kpler.
Haka kuma, matatar ta yi jigilar hanyoyin man fetur guda biyu zuwa gabar tekun Gabas ta Amurka, kuma ana sa ran isarsu yankin New York nan gaba a cikin wannan wata,
Hakan na zama wani gagarumin ci gaba ne, inda masu sa ido kan masana'antu ke bibiyar lokacin da matatar za ta samar da mai da zai yi gogayya da na Amurka.