Babban Bankin Ghana, (BoG) ya dakatar da lasisin cinikin kuɗaɗen ƙetare na bankin UBA reshen ƙasar Ghana.
Wata sanarwar da bankin ya fitar a shafinsa na X ya bayyana cewa dakatarwar za ta kai wata ɗaya daga ranar 18 ga watan Satumbar shekarar 2025 bisa dokar cinikin kuɗaɗen ƙetare na shekarar 2006.
Sanarwar ta ce an ɗauki wannan matakin ne sakamakon keta dokokin kasuwar cinikin kuɗaɗen ƙetare da bankin ya yi a lokaci da dama.
“UBA Ghana ya aiwatar da ayyukan tura kuɗaɗe ba tare da izini ba da waɗannan kamfanonin biyan kuɗi: Halges Financial Technologies da Cellulant Limited da kuma Flutterwave Inc., a madadin kamfanonin tura kuɗi- Top Connect da Taptap Send da Remit Choice da kuma Afriex,” in ji sanarwar.
Bankin ya ƙara da cewa ya dakatar da dukkan haɗin gwiwa da UBA ke yi da kamfanonin tura ko biyan kuɗi.
Har ila yau Babban Bankin na Ghana ya yi shelar dakatar da hulɗar haɗin gwiwa na kamfanonin tura kudi daga ƙetare irin su Tap Send da Top Connect da Remit Choice da Send App da kuma Afriex sakamakon keta dokokin tura kuɗi daga ƙetare na ƙasar.
Kazalika bankin ya kuma yi kira ga kamfanonin da ke cikin kasuwar ƙuɗaɗen ƙetaren ƙasar su bi dokoki da ƙa’iɗojin kasuwar sau da ƙafa.
Bankin ya yi gargaɗin hukunta duk wanda ya bijire wa dokokin kasuwar kuɗaɗen ƙetare na ƙasar.