Rwanda, tare da hadin gwiwar hukumar kula da hanyoyin mota da gadoji ta China (CRBC), ta kƙddamar da wata motar tasi mai tashi sama da ke aiki da lantarki, in ji sanarwar da gwamnati ta fitar.
Matakin ya sake tabbatar da matsayin kasar na cibiyar gwaji da aiwatar da fasahar kere-kere, in ji sanarwar da Ma’aikatar Samar da Kayan More Rayuwa ta fitar.
Ta hanyar haɗin gwiwa da kamfanin CRBC da ya kwara a duniya a fannin injiniyanci, Rwanda na da manufar gina sabon tsarin zamantakewa da zai tabbatar da sufurin sararin samaniya don rage cunkoson ababen hawa, haɗa al'ummomi waje guda da kuma samar da tsarin sufuri mai dorewa.
"Rwanda na ci gaba da gina makomarta inda biranenmu suka fi hade wa da juna kuma tattalin arzikinmu ya fi bunkasa ta hanyar samar da hanyoyin sufuri na zamani," in ji Ministan Samar da Kayan More Rayuwa Jimmy Gasore.
Abin misali
Ya yi tsokaci da cewa haɗin gwiwar na assasa tushe mai ƙarfi don kawo sabbin fasahohi da ƙwarewa.
"Ta hanyar haɗin kai a kan wannan mota mai tashi mai tarihi, ba wai muna nuna makomar sufurin jiragen sama ba ne kawai, muna nuna sadaukarwarmu wajen tsarin sufurin sama na zamani kuma mai tsaro,” in ji shi.
An shirya gwajin tashin motar tasi din kirar EHang EH216-S mara matukin mai samfurin eVTOL a wajen Babban Taron Sufurin Jiragen Sama na Afirka da aka gudanar a ranar Alhamis a Kigali babban birnin Rwanda.
Gwajin tashin motar na da manufar nufin samar da nazariyya abar misali da koyi ga masu ruwa da taki da mahukunta a nahiyar, wanda irin ta ce ta farko a Afirka.
Tana jan hankali zuba jari
Huang Qilin, babban daraktan ofishin CRBC na kasar Rwanda, ya ce hadin gwiwa da kasar, wata shaida ce ta yadda kamfanin ke kokarin samar da mafita ga Afirka.
Huang ya ce, "Duba ga girmanmu a duniya da karfin aikin injiniyancinmu, muna fatan yin aiki tare da kasar Rwanda don bunkasa tattalin arzikin kasar tare da samar da sabbin tsare-tsare don samun ci gaba a duk fadin nahiyar."
A cewar mahukunta, Rwanda na da burin jawo hankalin abokan zuba jari da fasaha zuwa kasuwannin hada-hadar zirga-zirgar jiragen sama da ke tasowa, wanda zai ɗora kan tarihin nasarar da ta samu na hidimar kawo jirage marasa matuka.
EHang, wanda aka ce shi ne kamfanin da ya zama jagora a duniya a fasahar sufurin sararin samaniya a birane, ya yi haɗin gwiwa tare da CRBC don faɗaɗa ayyukansa a kasuwannin duniya.