Jaririn goggon birin da aka saka wa suna "Zeytin", wanda aka gano a filin jirgin sama na Istanbul, a kan hanyarsa zuwa Thailand daga Nijeriya a 2024, na shirin komawa Nijeriya bayan an yi jinyarsa ya kuma farfado a gidan kula da namun daji da ke Polonezköy, Turkiyya.
Babban daraktan Hukumar Raya Gandun Daji na Turkiyya (DKMP) Kadir Çokçetin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa an gano Zeytin ne a filin jirgin saman Istanbul a kan hanyarsa ta zuwa Thailand daga Najeriya, a watan Disambar 2004.
Çokçetin ya bayyana cewa Zeytin ya shiga ran jama'a ba kawai a Turkiyya ba, har ma da duniya baki daya, inda ya ce ana sa ido sosai a kansa a duniya, musamman ma Majalisar Dinkin Duniya da Sakatariyar Yarjejeniyar Kasa da Kasa kan Nau'o'in Dabbobin daji da ke fuskantar barazanar bacewa (CITES).
Çokcetin ya bayyana cewa bayan bincike, kungiyoyi sun kwace jaririn goggon birin, saboda wadanda suke dauke da shi ba su da takardun CITES.
Ya ce an kula da Zeytin kuma an duba shi a cikin yanayi mai kyau da ba shi kariya. "Lokacin da aka same shi, yana cikin firgici sosai, ya gaji, yanzu kuma kamar yadda kuke gani, ya murmure, ya yi kyau sosai, ya fara buga kirjinsa, yana kokawa da masu tsaronsa," a cewar Çokcetin.

‘Zeytin na shirin komawa Nijeriya’
Ya kara da cewa Zeytin na da tsayin santimita 62 a lokacin da ya zo, yanzu kuma ya kai santimita 80. "Yana da nauyin kilogiram 9 a lokacin da ya iso, amma yanzu ya kai kimanin kilo 16. Yana cikin koshin lafiya, kuma an zaba masa sunan Zeytin ne bisa zabin 'yan kasa."
Shugaban na hukumar kula da gandun daji ta Turkiyya ya ce hukumomi Nijeriya sun nemi a mayar da Zeytin gida a hukumance.
“Saboda ya zo daga Nijeriya, dole ne a mayar da shi can idan har kasar da ya fito ta bukaci hakan, kamar yadda yarjejeniyar kasa da kasa ta tanada. Nijeriya ta rubuto mana bukatar hakan a hukumance,” a cewar Çokcetin.
Ya kara da cewa “wannan tsari ya dauki wani lokaci bayan da muka yi nazari kan ko za a kula da shi a can yadda ya dace. Yanzu da muka samu bukata a hukumance da kuma alkawuran ba shi cikakkiyar kulawa, za mu yi duk wani shiri na mayar da Zeytin zuwa Nijeriya nan da jimawa ba."
Çokcetin ya bayyana cewa ana kula da lafiyar Zeytin a kai a kai, inda ya ce, "Mun ji dadin zuwansa da kuma ganin yadda ya murmure, amma kuma ya zama wajibi mu tura shi gida. Da zarar an kammala cike dukkan ka’idoji, zai kama hanyar Nijeriya tare da hadin gwiwar kamfanin jirgin saman Turkiyya."