An buɗe babban bikin harkokin fasaha, jiragen sama, da sararin samaniya na Turkiyya, Teknofest.
Bikin, wanda zai mayar da hankali kan harkokin teku yana gudana a Istanbul, kuma zai nuna ƙarfin sojin ruwa da sabbin fasahohin ƙasar.
Wannan taron na kwanaki huɗu, wanda aka yi wa taken “Blue Homeland”, ya fara ne ranar Alhamis a Rundunar Kera Jirgin Ruwa ta Istanbul.
Kamfanin Anadolu na aiki a matsayin abokin ƙawancen sadarwa a duniya. Duk da cewa bikin ya fara ranar Alhamis, jama'a za su iya halartarsa daga ranar 30 zuwa 31 ga Agusta.
Ana sa ran Shugaba Recep Tayyip Erdogan zai halarci bikin a ranar farko.
Gasar da aka shirya a cikin wannan taron ta hada da tsarin karkashin ruwa mara matuki, rokokin karkashin ruwa, da kuma motocin ruwa masu cin gashin kansu.
Sojojin Ruwa na Turkiyya suna nuna wasu daga cikin jiragen ruwansu na zamani, kamar TCG Anadolu, jirgin ruwan yaƙi mai saukar jiragen sama, TCG Istanbul frigate, TCG Burgazada corvette mai yaƙi da jiragen ƙarƙashin ruwa, TCG Orucreis frigate, TCG Nusret mai dasa bama-bamai, tare da jiragen ƙarƙashin ruwa na TCG Sakarya da TCG Hizirreis.
Baya ga fasahar soja, Teknofest Blue Homeland yana nuna nune-nunen tarihin harkokin ruwa da al'adu, fasahar Kama-da-wane mai hulɗa, da kuma jerin tarukan ilimi.
Bayan wannan taron, babban taron Teknofest zai gudana daga ranar 17 zuwa 21 ga Satumba a Filin Jirgin Sama na Ataturk na Istanbul.