Ghana ta shirya domin yin bankwana da jami’an da hatsarin helikwafta ya kashe a lardin Ashanti na ƙasar a makon jiya.
Za a gudanar da jana’iza ta ƙasa ranar Juma’a a gaban fadar shugaban ƙasar da ke babban birnin ƙasar Accra, a wani taron da zai ƙunshi shugabannin Ghana da iyalan mamatan da kuma ‘yan ƙasa daga matakai daban daban domin girmama mamatan, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Ghana ya ruwaito.
Ministan tsaro Edward Kofi Omane Boamah yana cikin waɗanda za a binne ranar Juma’a.
Bayan an yi taron ibada na jana’iza, za a binne gawarwakin mutum shida da lamarin ya rutsa da su a maƙabartar soji da ke Tse Addo, kusa da sansanin Burma.
Mataimakin shugaban ma’aikatan Ghana da ke kula da gudanarwa, Stan Dogbey, ya bayyana tsare-tsaren jana’izar ta ƙasa, wanda zai ƙunshi taron ibada ta soji a ƙarƙashin jagorancin rundunar sojin Ghana.
An yi jana’izar ministan Muhalli da Kimiyya da Fasaha Ibrahim Murtala Muhammed da mataimakin sakataren tsaro na ƙasa Limuna Muniru Mohammed ranar 10 ga watan Agusta.
Waɗanda lamarin ya rutsa da su
Hatsarin na helikwafta ya yi sanadin mutuwar mutane takwas, ciki har da Ministan Tsaro Edward Kofi Omane Boamah da Ministan Muhalli da Kimiyya da Fasaha Ibrahim Murtala Muhammed.