AFIRKA
2 minti karatu
Dakarun RSF na Sudan sun kashe gomman mutane a wani sansanin 'yan gudun hijira a Darfur
A makon jiya dakarun RSF sun kai hari a Abu Shouk inda suka kashe fiye da mutum 40, a yayin da suke yunƙurin ƙwace Al Fasher, wuri na ƙarshe da sojojin ƙasar suke da ƙarfi a yankin Darfur.
Dakarun RSF na Sudan sun kashe gomman mutane a wani sansanin 'yan gudun hijira a Darfur
Wata matashiya da ke gudun hijira a sasanin Zamzam bayan dakarun RSF sun kai hari a ƙauyen Tawila / Reuters
17 Agusta 2025

Dakarun rundunar Rapid Support Forces (RSF) sun yi luguden wuta a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke yankin Darfur da ke yammacin Sudan, inda suka kashe aƙalla mutum 3, cikinsu har da ƙananan yara da wata mace mai juna biyu, a cewar wata ƙungiyar bayar da agaji ta likitoci.

Kazalika luguden wutar da dakarun Rapid Support Forces suka yi sansanin Abu Shouk da ke kusa da Al Fasher, babban birnin lardin North Darfur, ya yi sanadin jikkatar mutum 13, a ceewar ƙungiyar likitoci ta Sudan Doctors Network a wata sanarwa da ta fitar.

Luguden wutar da dakarun suka yi ranar Asabar shi ne irinsa na biyu da suka kai hari a sansanin a ƙasa da mako ɗaya.

Ƙungiyar Resistance Committees da ke Al Fasher, wadda ke bibiyar yaƙin da ke faruwa a yankin, ta ce dakarun RSF sun kwashe awanni da dama suna “lguden wuta babu ƙaƙƙautawa” tun da sanyin safiya. A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce dakarun sun kuma lalata wurare da dama da ke sansanin da ma yankunan da ke maƙwabtaka da shi.

Kawo yanzu rundunar RSF ba ta ce komai game da wannan batu ba.

Abu Shouk yana ɗaya daya cikin sansanoni biyu da ‘yan gudun hijira suke zama a wajen Al Fasher. Dakarun na RSF sun sha kai hare-hare a sansanonin, ciki har da wani babban hari da suka kai a watan Afrilu inda kashe kashe ɗaruruwan mutane tare da tilasta wa dubbai tserewa daga yankin.

Duka sansanonin biyu na Abu Shouk da Zamzam na fama da matuƙar ƙarancin abinci da tamowa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us