NIJERIYA
2 minti karatu
Jami'an tsaron Nijeriya sun kama shugabannin ƙungiyar 'yan ta'adda ta Ansaru, Abu Barra da Mamuda
"Nijeriya ta daɗe tana neman waɗannan mutanen biyu ruwa-a-jallo, haka kuma 'yan ta'adda ne da ƙasashen duniya ke nemansu," a cewar Malam Nuhu Ribadu.
Jami'an tsaron Nijeriya sun kama shugabannin ƙungiyar 'yan ta'adda ta Ansaru, Abu Barra da Mamuda
Abu Barra da Mamuda na cikin manyan 'yan ta'adda na Ansaru da duniya ke nema, a cewar Nuhu Ribadu / Nigerian Government
16 Agusta 2025

Hukumomin tsaro a Nijeriya sun kama manyan shugabannin ƙungiyar ‘yan ta'adda ta Ansaru mai alaƙa da Al-Qaeda, a cewar mai bai shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro.

Malam Nuhu Ribadu , wanda ya jagoranci shugabannin tsaro na ƙasar wajen gudanar da taron manema labarai a ranar Asabar a Abuja, ya ce an kama Mahmud Muhammad Usman (Abu Barra) da Abubakar Abba (Mahmud Al-Nigeri/Malam Mamuda).

“Ina mai farin cikin shaida muku cewa mun yi nasarar kammala aikin yaƙi da ta’addanci mai cike da hatsari da tattara bayanan sirri, wanda ya kai mu ga kama manyan shugabannin ƙungiyar da aka fi sani da Ansaru, wato reshen Al-Qaeda da ke Nijeriya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa an kama mutanen biyu ne tsakanin watan Mayu zuwa watan Yulin 2025, yana mai cewa kamun nasu ya zama sanadiyar wargajewar cibiyar bayar da umarni ta ƙungiyar Ansaru.

"Nijeriya ta daɗe tana neman waɗannan mutanen biyu ruwa-a-jallo, haka kuma 'yan ta'adda ne da ƙasashen duniya ke nemansu," a cewar Malam Nuhu Ribadu.

Abu Barra, wanda ake kira da “Sarkin Ansaru,” shi ne babban mai kula da lamuran ƙungiyar a faɗin Nijeriya kuma shi ne ya kitsa garkuwa da mutane da dama da kuma ɗaukar nauyin hare-haren ta’addanci da yawa.

Shi kuma Mamuda ya samu horo ne a ƙasar Libya a tsakanin 2013 zuwa 2015 a ƙarƙashin wasu ‘yan bindiga na ƙasashen Masar da Tunisia da Aljeriya da suka ƙware wajen amfani makamai da nakiyoyi.

Malam Nuhu Ribadu ya ce mutanen biyu sun kitsa hare-hare da dama, ciki har da harin da aka kai a gidan yari na Kuje da ke Abuja a 2022 da da hari a wajen haƙar ma'adinin yuraniyom a Jamhuriyar Nijar da garkuwa da wani Bafaranshe mai suna Francis Collomp a Katsina da yin awon gaba da Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar Uba a shekarar 2019 da sace Sarkin Wawa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us