Maryam Bukar Alhanislam: 'Yar Nijeriyar da ta zama jakadiyar zaman lafiyar MDD ta farko a duniya
Maryam Bukar Alhanislam: 'Yar Nijeriyar da ta zama jakadiyar zaman lafiyar MDD ta farko a duniya
Maryam, wadda aka fi sani da Alhanislam ta samu wannan matsayi wanda shi ne irinsa na farko a karkashin shirin zaman lafiya da tsaro na MDD a wani biki da aka gudanar a hedikwatar majalisar da ke New York a ranar Juma’a.
31 Yuli 2025

A wani gagarumin matsayi ga Nijeriya da kuma nahiyar Afirka suka samu a fagen samar da zaman lafiya a duniya, Majalisar Dinkin Duniya ta naɗa fitacciyar matashiyar nan mai baiwar fasaha da waƙar baka, Maryam Bukar Hassan a matsayin jakadiyar zaman lafiya ta duniya.

Maryam wadda aka fi sani da Alhanislam ta samu wannan matsayi wanda shi ne irinsa na farko a karkashin shirin zaman lafiya da tsaro na MDD a wani biki da aka gudanar a hedikwatar majalisar da ke New York a ranar Juma’a.

Mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Afirka, Ms Martha Pobee ce ta bayyana sanarwar a bainar manyan jami'an majalisar da jami'an diflomasiyya, da kuma masana al'adu daga sassan duniya.

Wace ce Maryam Bukar Hassan?
An haifi Maryam Bukar Hassan, wacce aka fi saninta da Alhanislam a shekarar 1996, kuma ‘yar asalin garin Biu ce na jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Ta yi karatun firamare da sakandare a Nijeriya, sannan ta yi karatu a fannin Fasahar Sadarwa a Jami’ar Radford da ke kasar Ghana.

Kazalika, ta yi fice wajen nishadantarwa da fadakarwa da zafafan waƙoƙin baka ta hanyar amfani da fasaha.

Ta gina wa kanta suna a matsayin mai fafutukar zaman lafiya da ƙarfafa gwiwar matasa, da kare hakkin mata da yara mata, da kuma kokarin tabbatar da adalci a zamantakewa a fadin Afirka.

Ayyukanta sun samu karɓuwa a wajen masu sauraro a fadin duniya, inda ta samu kyakkyawar shaida.

Jakadiyar zaman Lafiya ta MDD ta farko

Wannan shi ne karon farko da aka taba irin wannan naɗi a karkashin shirin zaman lafiya da tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, matakin da ke nuna yadda hukumar ke ƙara ba da muhimmanci ga kokarin samar da zaman lafiya karkashin jagorancin matasa da mata.

Duba da wannan sabon matsayi, ana sa ran Maryam za ta yi tafiye-tafiye da gabatar da shirye-shirye, da kuma shiga cikin al'ummomi - musamman matasa - a tattaunawa game da batutuwan da suka shafi zaman lafiya, da cuɗanya da kuma samar da waraka a yankuna masu fama da rikici.

Nijeriya ta haska a idon duniya

Nadin nata ya zama wani abin alfahari ga Nijeriya, inda hakan ya sanya kasar a sahun gaba a fannin diflomasiyya da neman zaman lafiya.

Shugabanni da manyan ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki, irinsu tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Farfesa Yemi Osinbanjo da Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya Bukola Saraki da mataimakiyar shugaban MDD Hajiya Amina J. Mohammed sun nuna farin cikinsu tare da taya Alhanislam murnar samun wannan matsayin da suka ce ta cancanta.

Kazalika, hakan wani ci gaba ne ga masu baiwar fasaha da ƙirƙira da ke aikin hada fasaha da gwagwarmaya.

Saƙonta

Saƙonta na bege da ƙarfafa gwiwa ne musamman ga matasa wadanda galibi ke jin radaɗin rikice-rikice ko kuma koma bayan tashin hankalin duniya.

"Zaman lafiya ba rashin rikici ba ne, amma kasancewar adalci, da mutunci, da murya ne. Ta hanyar wakar baka, za mu gina gadoji da wasu za su gina bango." a cewar saƙon da Maryam Bukar ta wallafa a shafinta na Instagram.

Matakin Gaba
A yayin da nauyin wannan matsayi mai cike da tarihi ya rataya a kafadarta, Maryam Bukar za ta hada kai da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya, da gwamnatoci, da kungiyoyin jama'a, domin tabo batutuwan da suka shafi cin zarafin mata zuwa tsattsauran ra'ayin matasa, ta hanyar amfani da wakokin baka a matsayin dandalinta na kawo sauyi.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us