DUNIYA
8 minti karatu
Ana kai wa Musulman Birtaniya hare-haren da ba a fadar su a kafafan watsa labarai
Me ya sa Birtaniya ke kallon tuggun masu tsaurin ra\ayi kan Musulmai a matsayin karafin laifi, ba ta’addanci ba? Shiru kan Kyamar Musulunci na bayyana funafurin kafafaen yada labaran Birtaniya da martanin siyasa, da hatsarin daukar tsanar da ke kisa.
Ana kai wa Musulman Birtaniya hare-haren da ba a fadar su a kafafan watsa labarai
Ana yawan kaskantar da kai wa musulmai hari a Birtaniya, ana barin jama'a da rauni ba tare da daukar matakan da suka kamata ba. / AP
7 awanni baya

A farkon wannan shekarar, a karamin garin Greenock da ke Scotland, yaro dan shekara 17, ya dilmiye a cikin tunanin Hitler, ya shirya kona Cibiyar Musulmai ta Inverclyde, ya kulle masu ibada a ciki tare da yada kisan kiyashin kai tsaye ta yanar gizo.

Tun yana dan shekaru 13 da haifuwa ya tasirantu da ra’yoyin mai tsattsauran ra'ayi, Anders Breivik, ya kuma shigar da shi TikTok, ya kutsa kai cikin masallacin ta hanyar yin kamar yana son musulunta.

Lokacin da aka kama shi, an same shi da gwangwani na iskar gas, bindiga marar kara, da kayan aikin kunna wuta. Har ma ya shirya takardar bayyana me ya sa shi aikata hakan.

Labarin yana da sanyi, duk da haka abin da ke da ban tsoro shi ne yadda aka samu ƙarancin bayar da labarin a manyan kafofin watsa labarai na Birtaniya.

Sky News  ta bayar da rahoto game da lamarin, ciki har da kawo shaida daga shugabannin masallacin, amma yawancin sauran manyan kafafen watsa labaran ba su bayar da wani ingantaccen rahoto ba.

Makircin kisan gillar da aka yi wa musulmi a gidan ibada bai bayyana a matsayin labarin kasa ba.

Yanzu ku yi tunanin idan da a ce wanda ya aikata laifin musulmi ne, kuma wadanda aka kashe din su kasance masu ibada a coci ko majami'a.

Kanun labarai da sun yi kururuwar ta'addanci. Da ‘yan siyasa sun yi gaggawar yin kalamai game da tsattsauran ra’ayi.

Ana iya ganin bambance-bambance a wajen bayar da rahotanni a matsayin mantuwa, amma hakan dai na nufin zurfafa son zuciya.

Wannnan son kai da zabi da ake yi wajen bayar da rahotanni na ƙarfafa ra'ayin cewa Musulmai za su yi zama barazana ne, ba ai wadanda ake kai wa hari ba, kenan hakan yana nuna cewa rayuwarsu da amincinsu ba su da muhimmanci.

Haka kuma yana kara kwarin gwiwar masu tsattsauran ra'ayi idan suka ga al'umma ba ta son daukar kyamar Musulunci da muhimmanci.

Salon kaskantarwa

Lamarin Greenock ba wani keɓantaccen lamari ba ne. A Sheffield, an kama Edmund Fowler da laifin sakin berayen daji a wajen Babban Masallaci a lokuta hudu daban-daban tsakanin Mayu da Yuni.

Gidan talabijin na CCTV ya nuno shi dauke da kejin berayen, tare da sakin su a kan titin Masallacin, yayin da bayanan da aka nada ta wayar hannu suka nuna shi yana izgili da masu ibada.

Tell MAMA, wata amintacciyar ƙungiyar agaji da ke tattara bayanan nuna kyama ga musulmi a duk faɗin Ingila, ta bayyana hare-haren a matsayin "abin kunya ne ƙwarai." Duk da haka Fowler bai shiga kurkuku ba.

A Nottingham, masu ibada a wani masallacin juma'a sun sha fama da cin zarafi na kusan shekaru biyu daga wata tsohuwa farar fata da ke ihun zagin masu zuwa masallaci har ma da hana motoci barin masallaci inda take rufe hanya.

Sun kai kara a Sashen Mayar da Martani ga Nuna Kyamar Musulunci (IRU), wata ƙungiya mai zaman kanta wacce ke ba wa waɗanda suka fuskantar nuna kyama tare da karfafa gwiwa a sirrance da bayanan dokoki.

IRU ba ta samun tallafin gwamnati, duk da haka tana wakiltar mutane da dama a ɗaruruwan shari'o'i a kowace shekara, suna masu tabbatar da cewa ba a bar waɗanda abin ya shafa su kadai ba.

Ya zuwa watan Yuli, da na’urar nadar bayanai an dauki bidiyon irin wannan arangama a wajen masallacin Nottingham, inda aka kai wa ‘yan sanda shaidar bidiyo, Jami’an sun bar mutumin ya tafi inda suka gargade shi kawai.

Mahalarta masallacin sun bayyana haka a matsayin shaidar nuna wariya a hukumance, inda cin zarafin nuna kyama ya zama laifin ba a yi wa kallon wani babban laifi.

Ko da a lokacin da aka gabatar da tuhuma, rashin ganin girman laifukan nuna ƙiyayya na iya rage girman hukunci.

A Scarborough da ke Arewacin Yorkshire, an kama James Martin dan shekara 18 a wajen wata cibiyar Musulunci da ashana a aljihunsa yayin da yake ihun cin zarafi a lokacin sallar magariba. Wani alkali ya yi gargadin cewa sakamakon "zai iya zama mai muni".

Amma duk da haka BBC  ta fara gudanar da labarin tare da taken, "An ɗaure matashi a kurkuku saboda zanga-zanga a Cibiyar Islama", sai dai daga baya ta gyara shi don tabbatar da samun ashana tare da shi.

Wadannan al'amura suna bayyana yadda aka mayar da nuna kyama ba komai ba, ba wai ta hanyar nuna kyama daga daidaikun mutane ba, har da tsarin kaskantarwa daga hukumomi.

Alkaluma ba sa karya

Wannan ba wai labari ne kawai ba.

A yayin da wannan tashin hankali ya ta’azzara, al'umomin musulmi sun kasance cikin rauni da rashin samun kariya. Iman Atta, daraktar Tell MAMA ta bayar da rahoton cewa hare-hare a 2024 sun karu da kashi 73, tare da tabbatar da faruwar al'amura 5,837, wanda ke nuna lokaci mafi hatsari ga Musulmai a Biritaniya.

Kuma duk da haka, wannan karin da aka samu bai sanya kafafen yada labarai sun dinga bayar da rahotannin ba.

Ana kallon ayyukan nuna kyama ga Musulmai a matsayin ayyukan wasu daidaikun mutane, ba wai laifukan barazana ba.

A wurare irin su Inverclyde, an tilasta wa al'ummomin Musulmi su inganta tsaronsu, su saka ido kan motsi da halayyar da ba su aminta da su ba.

Bugu da ƙari, duk wannan kasancewa ƙarin nauyi, yana zubar da amana. Masu bauta dole ne su damu idan wanda ba a sani ba yana yin addu'a a gefensu zai iya zama mai kutse da mugun nufi.

Wannan wani mummunan lahani ne na tunani da zai yiwa al'ummomin da aka riga aka ware.

Har yanzu Biritaniya ba ta da cikakkiyar manufa ta kasa don magance kyamar Islama da ma irin kulawar da lamarin ke bukata.

A watan Fabrairun 2025, gwamnati ta kafa kwamiti don samar da ma'anar ƙiyayya ga Musulmi ta ƙasa.

A watan Yuli, ta nada wata kungiya mai zaman kanta ta Amintattun Musulman Birtaniya don gudanar da sabon asusun yaki da kyamar Musulmai na gwamnati.

Amma tsarinta ya kasance mai cike da haske. Kamar yadda kafar watsa labarai ta Middle East Eye  suka ruwaito, gwamnati ta hana ƙungiyar ma’aikata tuntubar Majalisar Musulmi ta Biritaniya (MCB), babbar ƙungiyar Musulmai ta ƙasar, yayin da ta bayar da izinin shigar da bayanai daga daidaikun mutane da ƙungiyoyin da ake zargi da kyamar Islama.

Masu suka dai sun ce hakan na zubar da mutuncin tsarin da ake da shi, wanda ke haifar da shakku kan ko ana sauraron matsalolin al'ummar musulmi da kansu.

Ga Musulmai da yawa, waɗannan gamayyar matsaloli na nuni ga babbar matsala mai zurfi: Ana kawai kallon Kyama ga Musulunci a matsayin karya ka’ida, amma ba a magance matsalar yadda ya kamata.

Ƙungiyoyin agaji irin su Tell MAMA da Ƙungiyar Martani Kan Kyamar Musulunci (IRU) suna ci gaba da cike gibin, suna tattara bayanan cin zarafi, bayar da goyon baya na shari'a, da kuma neman amince wa, amma suna yin hakan a kan rashin nun katabus daga gwamnati da kafafan watsa labarai.

Karfafa gwiwar masu aikata laifin

Ta hanyar rashin daukar nuna kyama ga Musulunci da muhimmanci, Biritaniya na fuskantar kasadar mayar da rayuwar Musulmai marasa muhimmanci.

Wannan na karfafa gwiwar masu aikata laifin. Hakan na baiwa masu tsarin ra’ayi sakon cewa za su iya yin abinda suka ga dama, kuma tsaron Musulmai ba fifikon kasar ba ne.

Mai yiyuwa ne Musulmi ne ake kai wa hari, amma tashe-tashen hankula na masu tsaurin ra'ayi da suka samo asali daga akidar kyamar fararen fata na barazana ga zamantakewar Biritaniya baki daya.

Yana da mahimmanci a san cewa a cikin son kashe musulmi, maharin Greenock yana da niyyar shirya wani babban ta’annati na ta'addanci.

Irin wannan ƙiyayya, wanda ba a kula da ita don magance ta, na ta girmama.

Dole ne kafafen yada labarai na Biritaniya su bayar da rahoton tashin hankali na kyamar Islama tare da nuna muhimmanci kamar na sauran nau'ikan abubuwan da suka faru na tsatsauran ra'ayi.

Hare-haren da ake kaiwa masallatai da al'ummomi sun cancanci zama fiye da bayanan gida marasa muhimmanci.

Kuma dole ne gwamnati ta sanya kyamar Islama a cikin laifukan kiyayya da dabarun yaki da tsattsauran ra'ayi, tare da tabbatar da cewa ana daukar tsattsauran ra'ayi da muhimmanci kamar duk wata barazanar masu tsattsauran ra'ayi.

Wannan ya haɗa da wadata al'ummomi tare da tallafin kuɗi na gaske, na doka, da tsaro.

A karshe, jama'a su nemi a yi musu adalci. Birtaniya ba za ta iya ci gaba da kawar da wadannan labaran ba saboda wadanda abin ya shafa musulmi ne.

Idan kasar ba ta yi la'akari da mayar kyamar Islama ba komai ba a yanzu ba, to tana cikin hatsarin farkawa zuwa wani bala'i mafi girma wanda ba za a iya yin watsi da shi ba.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us