Mai yiwuwa wata rana ku ji labarin ana iya shan miyar agushi, wadda ake yawan amfani da ita a Nijeriya, a Duniyar Wata ko Duniyar Mars, bayan da aka tura agusin sararin samaniya aka zagaye duniya da shi tsawon kwana bakwai.
An tura ‘ya’yan agushin zuwa Tashar Ƙasa da Ƙasa da ke sararin samaniya (International Space Station) ta hanyar harba su a wata roka daga cibiyar Hukumar Bincike Kan Sararin Samaniya ta Amurka, NASA ta Kennedy Space Center a Florida a wannan watan, a wani shiri na nazarin yadda agushin zai kasance a sararin samaniya.
"Manufar ita ce, a cikin shekaru masu zuwa, idan mutane suna rayuwa a Duniyar Wata ko Mars, kuma suna buƙatar shuka abinci ... to abincin da ya samo asali daga Afirka zai kasance cikin wannan jerin," in ji Temidayo Oniosun, wanda ya zaɓi agushin don wannan tafiya.
"Don haka, ko a cikin shekaru 50 masu zuwa, idan 'yan Afirka suna rayuwa a Duniyar Wata, muna son su kasance suna shuka da dasa egusi," in ji dan kasuwar na Nijeriya, wanda ya kafa kamfanin bincike mai suna Space in Africa.
An sanya ‘ya’yan agushin ne a cikin wasu gwangwanaye na musamman aka sa a cikin roka ta Crew-11 sannan aka harba a ranar 1 ga Agusta tare da wasu nau’ukan tsirran na tarihi daga Costa Rica da Guatemala da Armenia da Pakistan.
‘Agushin yana bayyana tarihinmu’
Wani masanin kimiyya daga Jami’ar Florida, Wagner Vendrame, wanda ke cikin masu binciken wannan shiri, ya ce nan gaba, 'yan sama jannati za su bukaci nau’ikan abinci masu kyau fiye da abincin da aka sarrafa sosai da ake amfani da su a yanzu a sararin samaniya.
"Samun damar shuka kayan lambu kamar latas, tumatir, ko kankana a sararin samaniya ba wai kawai yana da muhimmanci ga abinci mai gina jiki da lafiya ba, har ma yana da tasiri a ƙwaƙwalwa, idan mutum ya ci agushi na ainihi maimakon wasu abubuwa da aka sarrafa," in ji shi.
Oniosun, wanda ya tattaro ‘ya’yan agushi daga kasuwanni a jihar Oyo ta kudu maso yammacin Nijeriya, ya ce zabin ya samo asali ne ba kawai saboda abincin yana gina jiki ba, har ma saboda al’adu da ma’anar tarihi.
"Kusan kowa a Nijeriya yana cin agushi, har ma da wasu mutane a wasu kasashen Yammacin Afirka da kuma 'yan Afirka a kasashen waje, don haka wannan (shiri) wani abu ne da za su iya danganta kansu da shi," in ji shi.
"Agushi shi ne tsiron da ke bayyana labarinmu."
‘Ya’yan agushin da aka yi shawagi a sararin samaniya a yanzu ana rarraba su ga masu bincike. Vendrame ya ce za a ajiye agushin a ɗakunan gwaje-gwaje na musamman don nazarin sauye-sauyen ƙwayoyin halitta da suka faru yayin da ake shawagi da agushin a sararin samaniya.
"Ta hanyar duba sauye-sauyen da suka faru da cikin tsirran, za mu iya gano - shin wadannan tsirrai har yanzu suna nan yadda suke? Za su ci gaba da bayar da irin wannan matakin na abinci mai gina jiki ga 'yan sama jannati?"