Jami’an tsaro a Jihar Neja da ke arewa maso tsakiyar Nijeriya sun kashe ‘yan bindiga aƙalla 50 a wani ƙazamin artabu da aka yi a ƙauyen Kumbashi da ke ƙaramar hukumar Mariga.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar ta Neja, Abdulmalik Mohammed Sarkin-Daji ne ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Laraba a Minna.
A cewarsa, 'yan bindiga kusan su 300 ne suka yi yunkurin kutsawa cikin al'ummar da misalin karfe 3 na rana a ranar Talata amma rundunar Sojoji da ta jami’an rundunar farin kaya ta DSS sun tunkare su.
Ya bayyana cewa maharan sun kai hari ne a sansanin jami’an DSS da ke yankin, amma jami’an tsaro sun yi arangama da su lamarin da ya yi sanadin mutuwar maharan da dama, yayin da sauran suka tsere ɗauke da munanan raunuka.
“Ganau sun shaida min cewa daga baya an ga ‘yan bindigar suna tarwatsa gawarwakin abokansu da suka mutu, tare da kwashe su cikin buhuna kana suka tafi da su a kan babura,” in ji Shugaban Majalisar.
Sarkin-Daji ya bayyana wannan nasara a matsayin shaida da ke nuna hazaƙar jami’an tsaro da ƙwarewarsu da kuma ƙarfin makaman hukumomin tsaro, ya kuma buƙaci mazauna yankin da su ci gaba da bayar da bayanai kan lokaci don taimakawa wajen ci gaba da yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci.
Ya kuma ba da tabbacin cewa majalisar dokokin Jihar za ta ci gaba da tallafa wa ayyukan tsaro tare da yin dokokin da suka dace.