NIJERIYA
3 minti karatu
‘Yan Nijeriya sun biya N2.57b a matsayin kuɗin fansa a cikin shekara ɗaya: Rahoto
Masu garkuwa da mutane a Nijeriya sun buƙaci zunzuruntun kuɗi har Naira biliyan 48 a matsayin kuɗin fansa amma sun samu Naira biliyan 2.57 (kimanin dala miliyan 1.66) a cikin shekara ɗaya, a cewar rahoton kamfanin tsaro na SBM.
‘Yan Nijeriya sun biya N2.57b a matsayin kuɗin fansa a cikin shekara ɗaya: Rahoto
'Yan Nijeriya sun biya Naira biliyan 2.57 (kimanin dala miliyan 1.66) ga masu garkuwa da mutane a cikin shekara daya / AP
28 Agusta 2025

Aƙalla mutane 4,722 ne aka yi garkuwa da su a wurare 997 a faɗin Nijeriya tsakanin watan Yulin 2024 zuwa Yuni 2025, yayin da aka kashe mutum 762 a hare-hare da ke da alaƙa da hakan, a cewar wani sabon rahoto da kamfanin tsaro na SBM Intelligence ya fitar a ranar Laraba.

Rahoton, wanda aka yi wa take da “The Economics of Nigeria’s Kidnapping Industry”, ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun buƙaci zunzuruntun kuɗi har Naira biliyan 48 a matsayin kuɗin fansa amma sun samu Naira biliyan 2.57 (kimanin dala miliyan 1.66) a cikin shekara ɗaya.

Duk da cewa akwai giɓi mai yawa tsakanin neman kuɗin fansa da kuma samun kuɗi na halak, rahoton SBM ya bayyana cewa kuɗaɗen fansa sun mayar da ƙungiyoyin ta’addanci zuwa ga masu iko, inda suke amfani da kuɗaɗen da suke samu wajen mallakar makamai, da ƙara dabaru, da kuma ɗaukar ma'aikata.

Yankuna da aka fi garkuwa da mutane

Yankin Arewa-maso-Yamma a Nijeriya ne lamarin ya fi shafa, inda aka samu rahoton wurare 425 (42.6%) da kuma mutane 2,938 (62.2%) da aka yi garkuwa da su.

Jihar Zamfara ce ke kan gaba da mutane 1,203, sai Kaduna da kuma Jihar Katsina.

Saɓanin wannan adadin, rahoton SBM ya ce yankin Kudu-maso-Yammacin ƙasar na da kaso mafi ƙanƙanta na aika-aikar masu garkuwa da mutane, inda aka samu kashi 5.3 cikin 100 da kuma kashi 3 cikin 100 na waɗanda abin ya shafa.

Rahoton ya kuma yi nuni da cewa mafi yawan sace-sacen jama'a da ake yi ko kuma garkuwa da mutum fiye da biyar na faruwa ne galibi daga yankin Arewa.

Kana a wasu lokutan ɓarayin kan tilasta wa mazauna ƙauyuka ko ma mutanen da suka yi garkuwa da su yin aikin gonaki da ma'adinai na 'yan fashin har sai lokacin da aka fanshe su.

Tattalin Arzikin Sana’ar satar Mutane

SBM ya bayyana sata ko kuma garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa a matsayin wani tsarin tattalin arziki ga ‘yan ta’adda, inda suke yin shi cikin tsari kamar na kasuwanci ta hanyar yarjejeniya, da hanyoyin sadarwa, da kuma amfani da raunin tsarin tsaro na ƙasa.

Rahoton ya nuna cewa a shekarar 2022, masu garkuwa da mutane sun tara kuɗi da ya kai N653.7m a matsayin kuɗin fansa wato (kimanin $1.13m). Ƙana ya zuwa shekarar 2025, sun karɓi N2.57b wanda ya kai dala miliyan 1.66, hakan ya nuna yadda hauhawar farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar kuɗin ƙasar suka shafi tattalin arzikin karɓar kuɗin fansa.

An nemi kuɗaɗe masu yawa daga yankin Kudu-maso-Kudu na ƙasar, inda aka buƙaci kuɗin fansa da ya kai biliyan N30 a jihar Delta, yayin da yankin Arewa maso Gabas kuma ya fitar da mafi yawan kuɗaɗen da aka tabbatar, inda aka biya kudin fansa da ya kai Naira miliyan 766 don sakin Mai Shari’a Haruna Mshelia, wanda aka ce an biya wani ɓangare na ƙungiyar Boko Haram.

Duk da hare-hare da farmakin da sojoji da jami’an ‘yan sanda suke kai wa kan ‘yan ta’addan na ɗan wani lokaci ne kawai, yayin da yunkurin gwamnatin na hana biyan kuɗin fansa ya ci tura, sakamakon rashin zaɓi da iyalai ba su da shi wanda ya wuce na biya kuɗin fansa.

Kamfanin SBM ya yi kira da a samar da wasu tsare-tsare na ƙasa waɗanda suka hada ayyukan tsaro da leken asiri na matakin al’umma da tallafi na tattalin arziki, da kuma sa ido kan yadda ake tafiyar da kuɗaɗen fansa da ake biyan masu garkuwa da mutane.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us