Majalisar Dokokin Turkiyya ta amince da wani kudiri mai tsauri da ke yin Allah wadai da Isra’ila kan faɗaɗa mamayar da take yi wa Gaza da kuma kisan kare-dangin da take yi wa Falasɗinawa.
A cikin sanarwar da ta fitar, majalisar ta bayyana cewa: “Muna kira da a dakatar da Isra'ila daga kasancewa mamba a Majalisar Dinkin Duniya da sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa har sai ta dakatar da manufofinta na kisan kare dangi.”
Kudirin ya kuma yi kira ga dukkan majalisun dokoki na kasa da su yanke duk wata alaka ta soja da kasuwanci da Isra'ila, tare da daukar matakan cire takunkumin da aka kakaba wa Falasdinu.
Sanarwar ta fito ne a karshen wani zama na musamman da mjalisar ta yi kan halin da ake ciki a Gaza.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya yi jawabi a zaman, inda ya yi wa 'yan majalisar bayani kan matsalar jin kai da ake fuskanta a Gaza.
Ya zargi Isra'ila da aikata laifuka a Gaza inda ya bayyana su a matsayin “daya daga cikin mafi munin shafuka a tarihin bil'adama.”
“Isra'ila ta shafe shekaru biyu tana aikata laifin kisan kare dangi a Gaza, tana watsi da darajar bil'adama a idon duniya,” in ji Fidan.
A watan Nuwamban bara, Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, da tsohon Ministan Tsaronsa, Yoav Gallant, bisa zargin aikata manyan laifuka da laifukan cin zarafin bil'adama a Gaza.
Haka kuma, Isra'ila na fuskantar shari'ar kisan kare dangi a Kotun Duniya kan yakin da take yi a wannan yankin.