Kamfanin ƙera jiragen sama marasa matuƙa na Turkiyya, HAVELSAN, ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar haɗin gwiwa tare da Hukumar Masana'antu ta Larabawa ta Masar (AOI), ɗaya daga cikin manyan masana'antu a Afirka, don haɗin gwiwar samar da jiragen sama marasa matuƙa, ciki har da BAHA, BULUT, da BOZBEY.
Wannan yarjejeniya ta ƙara wani sabuwar haɗin gwiwa ga nasarorin fitar da kayayyaki na HAVELSAN, wanda tsawon shekaru ya bayar da mafita a fannoni masu muhimmanci kamar manhajoji na tsaro, fasahohin sarrafa kansa, tsarin kwaikwayo da horo, hanyoyin sarrafa umarni, da kuma tsaron intanet.
A karkashin wannan haɗin gwiwar dabarun, za a gudanar da shigarwa da kuma haɗin gwiwar samar da jiragen sama marasa matuki masu sarrafa kansu.
Yarjejeniyar za ta samar da mafita mai araha da inganci ga yankin, tana amsa bukatun Masar da sauran ƙasashen Afirka, tare da ƙarfafa dangantakar masana'antu tsakanin Turkiyya da Masar.
“Muna farin cikin yin aiki tare da abokiyar haɗin gwiwa mai ƙarfi kamar AOI. Wannan haɗin gwiwar za ta ƙara ƙarfin samar da kayayyaki na cikin gida kuma za ta ba mu damar shiga kasuwar Afirka da ƙarfi, tare da kawo fasahar jiragen sama marasa matuƙa masu sarrafa kansu zuwa yankin,” in ji Babban Manajan HAVELSAN Mehmet Akif Nacar a jawabinsa yayin bikin sanya hannu a farkon makon nan.
‘Babban mataki na samar da kayayyaki’
“A matsayinmu na babban mai taka rawa wanda ke bayar da mafita masu inganci, amintattu, kuma na zamani a duniya, za mu ci gaba da haɓaka manyan fasahohi da ƙara daraja ga kasuwannin yankin,” ya ƙara da cewa.
A nasa ɓangaren, Shugaban AOI, Manjo Janar Mukhtar Abdullatif, ya kuma bayyana cewa ƙwarewar HAVELSAN a fannin fasaha za ta haɗu da ƙarfin samarwa na AOI don tallafa wa hangen nesa na tsaro da fasaha ta Masar.
“Wannan haɗin gwiwar ba kawai babban mataki ne ga samarwa ba, har ma ga samun 'yancin fasaha da kuma dorewar fitar da kayayyaki,” in ji Abdullatif.
A matsayinsa na wanda ke da ƙwarewa mai yawa a fannin fasahohin sarrafa kansu da jiragen sama marasa matuki, HAVELSAN na bayar da mafita da aka tabbatar da ingancinta a fannin tare da jiragen sama na yaƙi marasa matuƙa na BAHA, BULUT, da BOZBEY.
Wadannan ƙwarewar suna bai wa HAVELSAN damar samun matsayi mai ƙarfi a kasuwannin duniya kuma suna ba shi damar faɗaɗa zuwa yankuna masu faɗi tare da sabbin haɗin gwiwa.
Tare da wannan yarjejeniya, HAVELSAN zai ba da damar aiwatar da mafita masu inganci, amintattu, da kuma masu sauƙin saye a kasuwar Afirka.