GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Turkiyya ta jaddada dakatar da kasuwanci da Isra'ila da hana jiragen ruwanta zuwa tashoshin Isra'ila
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi watsi da duk wata shawara da ta shafi korar Falasdinawa daga Gaza, ba tare da la’akari da ko wane ne ya ba da shawarar ba.
Turkiyya ta jaddada dakatar da kasuwanci da Isra'ila da hana jiragen ruwanta zuwa tashoshin Isra'ila
Fidan ya ce, suna ƙin duk wani shiri da ke nufin korar Falasdinawa daga Gaza. / AA
12 awanni baya

Turkiyya ta sake tabbatar da cikakkiyar dakatar da cinikayya da Isra'ila, inda Ministan Harkokin Waje ya sanar da cewa jiragen ruwa na Turkiyya ba za su sake samun izinin sauka a tasoshin jiragen ruwa na Isra'ila ba, kuma za a hana jiragen sama na Isra'ila damar shiga sararin samaniyar Turkiyya.

Da yake magana a wani zama na musamman na Majalisar Dokokin Turkiyya a ranar Jumma'a, Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan ya zargi Isra'ila da aikata laifuka a Gaza da ya bayyana a matsayin "daya daga cikin mafi muni a tarihi na bil'adama."

"Isra'ila tana aikata laifin kisan kare dangi a Gaza tsawon shekaru biyu, tana watsi da muhimman dabi'un bil'adama a kan idon duniya," in ji Fidan.

Ya kara da cewa, gwagwarmayar Falasdinawa da Isra'ila za ta "canza tafarkin tarihi, da zama alama ga masu zalunci, kuma ta girgiza tushen tsarin da ke rushewa."

Fidan ya yi watsi da duk wani shiri da ya shafi korar Falasdinawa daga Gaza, yana mai jaddada cewa: "Ko wane ne ya gabatar da wannan tsari, ba zai taba zama mai inganci a gare mu ba."

Ministan ya kuma yi Allah wadai da ayyukan Isra'ila a wajen Gaza, yana ambaton hare-hare a Lebanon, Yemen, Syria da Iran a matsayin "mummunan abu da ke nuna alamar ‘yar ta’addar ƙasa da ke watsi da tsarin duniya."

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us