Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino ya yi tir da cin zarafin launin fata da aka yi wa ɗan wasan gaban Bournemouth ɗan asalin Ghana, Antoine Semenyo, yayin wasan Gasar Firimiya ta Ingila, abin da ya sa aka dakatar da wasan na ɗan lokaci.
Wannan cin zarafin da ake zargi ya faru ne a lokacin buɗe kakar wasa ta 2025-2026 a filin wasa na Anfield, inda Liverpool ta doke AFC Bournemouth da ci 4-2, duk da cewa Semenyo ya zura ƙwallaye biyu.
Infantino ya bayyana a shafukan sada zumunta cewa, "Ba za a amince da cin zarafin launin fata da aka yi wa Antoine Semenyo na AFC Bournemouth ba, wanda ya sa aka dakatar da wasan Gasar Firimiya da suka yi da Liverpool FC a Anfield. Ba za a lamunci wariyar launin fata ko wani nau'in wariya ba a ƙwallon ƙafa."
Ya kuma tabbatar da cewa FIFA za ta ci gaba da ɗaukar matakai kan wannan batu, yana mai cewa, "Za mu ci gaba da bayar da cikakken goyon baya ga Semenyo… domin tabbatar da cewa an samar da matakan hana irin wannan abu, kuma an ɗauki matakai don kawar da wariya daga ƙwallon ƙafa."
An kama wanda ake zargi
An kama wani mutum mai shekaru 47 daga Liverpool, wanda aka saki kan beli bayan an tuhume shi da laifin cin zarafin launin fata a bainar jama'a, kamar yadda 'yan sandan Merseyside suka bayyana a ranar Litinin.
A ƙarƙashin sharuɗɗan belinsa, ba zai iya halartar kowane irin wasan ƙwallon ƙafa da aka tsara a cikin Burtaniya ba, kuma ba zai kusanci filin wasa da nisan mil guda ba.
Binciken 'yan sanda kan wannan lamari yana ci gaba.
'Yan-sanda sun ƙaddamar da bincike kan laifin ƙiyayya bayan korar wani ɗan kallo mai shekaru 47 daga filin wasan, saboda muzanta ɗan wasan Bournemouth ɗan asalin Ghana.
Babban jami'in 'yan sanda, Kev Chatterton, ya jaddada cewa, "'Yan sandan Merseyside ba za su lamunci kowace irin wariya ba."
Chatterton ya ƙara da cewa, "Muna ɗaukar irin wannan lamari da muhimmanci sosai, kuma a irin wannan yanayi za mu nemi takardar hana shiga filayen wasa tare da haɗin gwiwar kulob ɗin, kan waɗanda suka aikata laifin."
Semenyo, mai shekaru 25, wanda ya zura dukkan ƙwallayen Bournemouth guda biyu, daga baya ya bayyana ƙarin cin zarafin launin fata da ya fuskanta a intanet, inda ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, "Yaushe wannan zai tsaya?"
Goyon baya
‘Yan wasan Bournemouth sun yi wa Semenyo jaje, sannan an karanta saƙon adawa da wariya ga taron jama'a a cikin filin wasan na Anfield bayan an tashi tafi hutun rabin lokaci.
Haka kuma, hukumar Firimiya ta ce za ta binciki lamarin tare da bayar da cikakken goyon baya ga ɗan wasan da kuma ƙungiyoyin biyu.
A cikin wata sanarwa, Liverpool ta ce ta samu labarin zargin kuma tana Allah-wadai da "wariya da nuna bambanci a kowane nau'i."
"Kulob ɗin ba zai iya yin ƙarin bayani ba saboda zargin da aka yi a daren yau yana ƙarƙashin binciken 'yan sanda, wanda za mu bayar da cikakken goyon baya," in ji sanarwar a daren Juma'a.