Ɗan wasan Napoli, Romelu Lukaku ya samu rauni a cinyarsa yayin wasan sada-zumunta da Olympiacos, kafin fara gasar Serie A ta Italiya.
Raunin zai tilasta masa tafiya jinyar watanni uku har zuwa Nuwamba, kamar yadda Napoli ta tabbatar a wata sanarwa.
Sanarwar ta ce, "Sakamakon raunin da ya samu yayin wasa da Olympiacos, an yi wa Romelu Lukaku gwaje-gwaje a asibitin Pineta Grande Hospital, wanda ya bayyana babban rauni a ƙashin cinyarsa ta hagu. Ɗan wasan tuni ya fara samun kulawa kuma zai samu shawar likita kan tiyata."
An yi wa ɗan wasan ɗan asalin Belgium gwajin likita a asibitin Pineta Grande Hospital, kuma rahotanni sun nuna ya samu babban rauni a ƙashin cinyarsa.
Lukaku dai yana da babban tasiri a ƙungiyar Napoli a baya-bayan nan ƙarƙashin koci Antonio Conte, wanda a baya sun yi aiki tare a Inter.
Madadin Lukaku
Sai dai wannan na zuwa ne yayin da Napoli ta riga ta sayar da wasu ‘yan wasan gabanta, kamar Giovanni Simeone da Giacomo Raspadori.
Yayin da ya rage kwanaki 13 kafin rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa na bazarar nan, yanzu ƙungiyar za ta yi hanzarin neman wanda zai maye gurbin Romelu Lukaku.
A farkon bazarar nan Napoli ta ɗauko aron Lorenzo Lucca daga Udinese, amma dogaro kan sitiraika ɗaya ba zai gamsar da muradun ƙungiyar a kakar bana ba.
Napoli za ta fara wasan farko na kakar 2025-26 na Serie A ranar Asabar 23 ga Agusta a gidan Sassuolo, inda za ta yi ƙoƙarin fara kare kambin Serie A da ta ci a kakar bara.