Kocin Liverpool, Arne Slot ya yi iƙirarin cewa ƙungiyarsa ce mafi nuna gaskiya a gasar Firimiya ta Ingila.
Rahotannin sun ambato Slot na cewa, "Idan akwai kungiya ɗaya a [Firimiya] lig da a ra’ayina ita ce mafi gaskiya yayin wasa..., kuma wadda ‘yan wasanta ba sa taɓa yin langwai kuma ba sa taɓa jan lokaci da sauran shegantaka, to mu ne [Liverpool]”.
Slot ya ce ya yi imanin ‘yan wasansa suna da gaskiya saboda ba sa faɗuwa ba tare da dalili ba, sai idan an musu ƙeta.
Kocin ya ce wani lokacin ‘yan wasan nasa sukan nuna gaskiya da yawa, har ba sa ribatar lokacin da aka musu ƙeta, don samun bugu ko don a hukunta abokan adawarsu.
Ya ba da misali da wasan kofin Community Shield da Liverpool ta kara da Crystal Palace, inda aka riƙe Florian Wirtz, amma bai faɗi ƙasa ba.
Ra’ayin masu sharhi
Amma masu sharhi sun ce duk da iƙirarin na Arne Slot, jadawalin nuna ɗa’a yayin wasa na kakar bara bai nuna Liverpool na kangaba a wajen nuna gaskiya ba.
Misali, a bara Manchester City ce ƙungiyar da ta fi ƙarancin samun yalon kati na gargaɗi (56), yayin da ita Liverpool ta zo ta huɗu a ƙarancin yalon katin da katuna (64) a Firimiya.
A fannin jan kati kuwa, ‘yan wasan Liverpool sun samu biyu ne, wanda ya sa suka zama cikin ƙungiyoyi biyu da suka fi kowa yawan jan katin a gasar.
Wannan ƙididdiga ta nuna cewa Liverpool ce ƙungiya ta shida a fannin ɗa’a ko nuna gaskiya yayin wasa a kakar bara, duk da cewa babu ƙididdiga kan ƙungiyar da ta fi faɗuwar ƙarya.