Matashin ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal ya mayar da martani kan sukar da kocinsa Hansi Flick ya yi kan halayyar ‘yan wasan ƙungiyar da ke kawo musu matsala.
Flick ya faɗa a wata tattaunawa cewa, rashin nasarar da suka yi a wasansu da Rayo Vallecano ranar Lahadi yana "ganin ba matsalar rashin fara kakar bana da karsashi kamar bara ba ce”.
Ya ce, “Maganar ita ce ta ji-ji-da-kai tsakanin ‘yan wasanmu a wajen fili. Bayan yin canjaras, za ka yi takaici; amma a ƙarshe dole ka nemi yin nasara [a gaba]."
Bayan wannan kalaman ne, idanu suka koma kan Lamine Yamal saboda yadda tauraruwarsa ke ƙara haskakawa a tawagar Barcelona da ma ta Sifaniya.
Martanin Yamal
Batun bikin cikar Yamal shekaru 18 ya janyo surutai, inda har sai da aka yi bincike kan abin da ya faru a wajen bikin. Haka ma batun ‘yan-matansa ya ja hankalin jaridun duniya.
Matashin ya fuskanci suka, inda har aka ambato shi yana cewa, "A baya-bayan nan, an yi ta maganganu kan rayuwata a wajen filin wasa sama da a cikin fili”.
Ya ƙara da cewa, “Na fahimci cewa duk abin da ya faru da rayuwata sai an yi magana a kai. Ni ban damu ba… Ba za ka taɓa jin Lamine yana fushi ko murna ba don abin da wani ya ce.”
Wasu na fassara wannan kalamai na tauraron ɗan wasan a matsayin yin biris da sukar da kocinsa ya yi, ko da kuwa har da shi cikin waɗanda ake zargi da nuna halayyar rashin haɗin-kai.”
A yanzu dai za a jira ganin wasan da Barcelona za ta buga da Valencia a gasar Laliga, domin ganin ko ‘yan wasan za su sauya rawarsu, musamman ganin Real Madird ta ba su tazarar maki biyu a teburi.