WASANNI
1 minti karatu
Leverkusen ta sallami kocinta Erik Ten Hag bayan jagorantar wasa uku kacal
Leverkusen ta sallami kocinta Erik Ten Hag bayan jagorantar wasa biyu kacal a kakar Bundesliga ta bana, da ƙarin wasa guda kafin nan.
Leverkusen ta sallami kocinta Erik Ten Hag bayan jagorantar wasa uku kacal
A kakar Bundesliga ta bana, Ten Hag ya jagoranci buga wasanni biyu ne kawai, inda aka doke su a na farko, sannan suka yi canjaras a na biyu. / AP
kwana ɗaya baya

Bayer Leverkusen ta Jamus ta kori sabon kocinta Erik ten Hag sakamakon rashin nuna tagomashi a aikinsa.

Leverkusen ta sanar a hukumance cewa ta sallami Erik Ten Hag bayan wani mataki da shugabancinnin ƙungiyar suka zartar ranar Alhamis da ta gabata.

Ten Hag wanda ɗan asalin Netherlands ne ya samu wannan labari a sirrance yayin wani taro da shi a safiyar Litinin.

Tsohon kocin Manchester United da Ajax, Ten Hag ya je Leverkusen ne a Mayun da ya gabata, kuma ya jagorance su buga jimillar wasanni uku kacal tun bayan zuwansa.

A kakar Bundesliga ta bana, kocin ya jagoranci buga wasanni biyu ne kawai, inda aka doke su a na farko, sannan suka yi canjaras a na biyu.

Sabon koci

Majiyoyi daga kulob ɗin na Jamus na cewa matakin korar Erik Ten Hag na zuwa ne bayan jami’an Bayer Leverkusen sun yi bitar ƙwazon kulob ɗin tun zuwan kocin.

A yanzu dai Leverkusen za ta mayar da hankali wajen neman wanda zai ja ragamar ƙungiyar yayin da gasar Bundesliga ta fara ɗaukar saiti.

Za a jira ganin wanda zai yi riƙon-ƙwarya kafin zuwan sabon koci a wasannin da ke zuwa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us