Manufar bai ɗaya ta tsare harshe ta hade kawunan al’ummar Songhay-Zarma-Dendi
Manufar bai ɗaya ta tsare harshe ta hade kawunan al’ummar Songhay-Zarma-Dendi
Al’ummar Songhay-Zarma-Dendi na gudanar da taro kowacce shekara a kasashen yankin Sahel daban-daban, suna amfani da damar harshensu na bai daya a matsayin jigon tsira, hadin kai da dabbaka al’adu. Nijar ce ta karbi bakuncin taron 2025.
25 Agusta 2025

Tarihi na kanannade da harsunan da suka mutu, kowanne kan zama kukan mutuwa ga al’ummar da ta rasa muryarta, sannan tare da hakan, wtakila a samu wani abu mai muhimmanci da zai taimaka wajen tsirar harshen.

Mutanen Songhay-Zarma-Dendi, da ke warwatse a yankin Sahel na Afirka, sun san abin da ake nufi da riko da harshensu a a yayin da duniya ke fama da lalacewar al'adu.

Maimakon su jira bacewar harshensu baki daya, suna taru wa duk watan Agusta a wata ƙasa daban don yin bayani, murna da tsara dabaru game da harshensu.

Babban birnin Nijar, Niamey, ya karbi bakuncin taron shekarar 2025 a watan Agusta, inda aka dinga yin kai kawo na tsawon kwanaki biyu, inda harsuna suka kasance tushen bikin al’ada da jigon magance matsalolin yankin da dama.

Farfesa Mamoudou Djibo, masanin tarihi kuma ɗan siyasa a Nijar, wanda ke jagorantar kwamitin shirya taron, yana ganin waɗannan tarukan suna da mahimmanci fiye da kiyaye al'adu.

"Wannan taron al'adu na kasa da kasa na da manufar, sama da komai, hada dukkan al'ummomin harsunan yankin Songhay-Zarma-Dendi.

Muna gayyatar dukkan al'ummomi domin hakan na da muhimmanci wajen fahimtar alakar da ba mu sani ba," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

"Gano wa da nuna tausayi na iya zama sanadin hadin kai, hakan na iya taimakawa wajen samar da abin da muke kira 'Amana', ko kuma wani nauyi da dawainiya da suka rataya a wuyan mutane. Cika nauyin 'Amana' na nufin wajibi ne mutane su mutunta da kuma hada kai tare, wanda hakan kuma yana bayar da gudunmawa ga hadin kan kasa."

Batun ya wuce na harshe kawai

Tushen yare na al'ummar Songhay-Zarma-Dendi ya bazu a kasashen Nijar, Burkina Faso, Mali, Benin, Ghana, Cote d'Ivoire, Sudan, Najeriya, da yankin Tab na kudancin Aljeriya.

Ga mutanen waɗannan yankuna daban-daban, taron na shekara-shekara yana bayar da manufa guda biyu na raya harshensu ta hanyar amfani da aiki tare da samar da dandamali don magance matsalolin zamantakewa da siyasa da muhalli.

Yayin da taron ya mayar da hankali kan harshe, yana kuma ƙarfafa kyakkyawar tattaunawa kan ƙalubalen zamantakewa da siyasa da al'adu da ke fuskantar mutanen Songhay-Zarma-Dendi.

Shugabanni masu tunani daga sassa daban-daban na gudanar da bita da kara wa juna sani a cikin harsunansu na asali, inda suke tattauna batutuwan da suka hada da ta'addanci a yankin Sahel da bukatar kiyaye muhalli da kuma yanayin da muhallin ke ciki.

"Al'ummomin da ke fuskantar hare-haren ta'addanci na yau da kullum sun fi dace wa wajen taimakawa hukumomi wajen neman mafita. Dole ne masana su shiga cikin neman mafita," in ji Farfesa Djibo.

"A daya daga cikin tarukan da muka shirya, mun tattaro wakilan shugabannin kasashen kungiyar AES (Kawancen Kasashen Sahel) don samar da hanyar da ta dace ta bai wa hukumomin siyasa sahihin bayanai a hakikanin lokaci, da baiwa gwamnatin tsakiya damar daukar matakan dakile yiwuwar kai hare-hare."

Mahalarta masu shekaru daban-daban sun kammala taronsu tare da ingantattun shawarwari ga mahukuntan gwamnatoci kan ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.

Sabbin matakan a yayin da ake samun cigaba

Taron na Songhay-Zarma-Dendi ya samo asali ne daga kasar Mali a farkon wannan karni, lokacin da aka gudanar da bikin fasaha da al'adu na kasa da kasa na Sonrhaï (FIASC) a garin Gao.

Ko a lokacin da arewacin Mali ke fuskantar tashin hankali, an gudanar da musayar al'adu a Bamako da kuma birnin Ouagadougou na Burkina Faso da ke makwabtaka da kasar.

A shekarar 2020 ne birnin Niamey ya so ya fara karbar bakuncin taron, amma barkewar annoba da babban zabe a Nijar ya sa babban birnin kasar ya jira har zuwa wannan shekarar.

Taron yana haɓaka jin daɗin ƙabila iri guda, harshe da alaƙar al'adu.

A cewar shahararren marubucin nan dan kasar Kenya Ngugi wa Thiong'o, wanda ya shahara da daina rubutu da turanci daga baya a cikin aikinsa domin ya inganta harshensa na asali na Gikuyu, harshe shi ne ruhin al'adar da ''ba za a bar ta ta mutu ba''.

Mutanen Songhay-Zarma-Dendi sun zaɓi su ci gaba da raya harshensu domin su rayu.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us