Alƙalin Amurka Frank Caprio, wanda aka saka wa suna "alƙalin da ya fi kirki a duniya", ya rasu yana mai shekaru 88 a duniya bayan ya sha fama da kansar tumburƙuma.
Wani saƙon da aka wallafa a shafinsa na Instagram ya tabbatar da mutuwarsa ranar Laraba, yana mai bayyana cewa alƙalin ya mutu ne bayan "doguwar jarumta da fama da kansar tumburƙuma."
"Mai Shari’a Caprio ya yi tasiri a rayuwar miliyoyin mutane ta hanyar aikinsa a zauren kotu da ma waje. Yadda yake jan mutane jiki da ban dariyarsa da kuma kirkinsa sun yi tasirin da ba za a iya mantawa ba ga duk wanda ya sanshi," in ji saƙon.
"Za a rinƙa tunawa da shi a matsayin alƙalin da ake girmamawa da miji wanda ya sadaukar da kai da baba da kaka da kakan kaka da kuma aboki."
Kwana ɗaya kacal kafin ya rasu, ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Instagram inda yake neman mabiyansa su saka shi a addu’o’insu yayin da yake fama da kansa.
"Yayin da nake ci gaba da wannan yaƙi mai wuya, addu’o’inku za su sa na ji daɗi," in ji Caprio a saƙonsa.
"Sai dai kuma, na samu koma-baya, kuma na koma asibiti," in ji shi, yana magana game da dawowar kansar.
"Ina neman ku tuna da ni a cikin addu’o’inku. Ni mai matuƙar imani ne game da ƙarfin addu’o’i."
Tarihin tausayi
Caprio, wanda aka haifa a Rhode Island a shekarar 1936, ya bar tarihin jinƙai da kuma ayyukan kirki da ba za a iya ƙirgawa ba har ma a wajen kotu.
Gaba ɗaya cikin tarihin aikinsa, ya nuna tausayi da fahimta, inda a yawan lokuta yakan rage ko kuma ɗauke tara ga mutanen da ba za su iya biya ba.
Gwamnan Jihar Rhode Island Dan McKee ya fitar da wata sanarwa domin miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan alƙalin.
"A matakin ɗan’adam, ya kasance aboki da ya fuskanci rashin lafiyarsa cikin jarumta, kuma zan yi kewarsa sosai. Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalansa da masoyansa a wannan mawuyacin lokacin," in ji McKee.
"Alƙali Caprio ba wai kawai ya yi wa jama’a hidima da kyau ba ne, ya kuma ja jama’a a jiki ta wata hanya mai ma’ana, kuma mutane ba su da zaɓi illa su mayar da martani da ƙauna da tausayi. Ba mai shari’a ba ne kawai — ya kasance wata alama ta tausayi a kotu, yana mai nuna mana abin da zai iya yiwuwa idan aka haɗa alƙalanci da jinƙai."
Caprio ya fito a wani shiri da ya samu shiga cikin shirye-shiryen da za su iya samun kyautar Emmy mai suna "Caught in Providence," daga shekarar 2018 zuwa shekarar 2020.
A cikin shirin, Caprio yakan saurari ƙarraraki kan tuhume-tuhume sannan ya nuna halin dattako yayin da ya tunkari waɗanda ake zargin da tausayi.