Wani bidiyo da ke yaɗuwa a shafukan sada zumunta tun ranar 18 ga watan Agusta ya nuna wasu Yahudawa ‘yan-kama-wuri-zauna suna kafa tuttocin Isra’ila tare da sanya allunan alama a ƙasa a wani lamari da suka ayyana a matsayin gina sabon matsuguni a kusa da garin Alonei Habashan da ke kan iyaka.
An ga yara, waɗanda suka fi manya yawa a bidiyon suna ta tafa hannu da rawa da murnar kafa abin da suka kira matsagunin “Nave Habashan” a cikin ƙasar Syria, wanda a yanzu ke ƙarƙashinikon sojojin Isra’ila.
Ƙungiyar mutanen sun kira kansu da suna “Bashan Pioneers” – wani sunan Tuddan Golan da ya samo asali daga injila da kuma kudancin Syria, tare da sanar da aniyarsu ta kasancewa a yankin har “zuwa wani lokaci mai tsawo.”
Leah Shefer, ɗaya daga cikin ‘yan-kama-wuri-zaunan, ta shaida wa tashar talabijin ta Channel 7 cewa tana da ‘yancin “shiga da kafa matsuguni” tare da cewa a ƙarshe sojojin Isra’ila za su samu iko da Syria.
“A zamanin Sarki David (Annabi Dauda), mun zauna a nan,” ta yi ikirari, tana mai cewa ƙasar wajen “gadon” kakannin kakanninta ne.
Sojoji, waɗanda suke kula shingayen bincike tara a kudancin Syria tun bayan faduwar gwamnatin Assad, daga baya sun kawar da ƙungiyar ‘yan-kama-wuri-zaunan, duk da cewa Shefer ta ce “suna matuƙar goyon bayan faɗaɗar ƙasar Isra’ila.”
“Isra’ila na yin abu kamar sangartacciya. ‘Yan-kama-wuri-zauna sun samu cikakkiyar damar tunzura Falasɗinawa, da Siriyawa da ‘yan Jordan,” kamar yadda Yousef Alhelou, wani Bafalasɗine mazaunin London mai shirya fina-finai ya shaida wa TRT World.
“Ba a bin da muke gani a nan sai filayen da babu kowa na ƙsarmu da ke kiranmu mu dawo mu zauna,” in ji Shefer.
“Muna kira ga gwamnatin Isra’ila da ta kawar da maƙiyanmu daga dukkan yankunan Bashan ta kuma bar mu mu zauna a cikinsu.”
A cewarta: “A ƙarshe, (Sojojin Isra’ila) sun shaida mana cewa ya kamata mu fita don kar mu shiga cikin matsala, kuma mun bi abin da suka ce.”
‘Zalinci na ƙarfafa wa ‘yan-kama-wuri-zauna gwiwa’
Fafutukar ‘yan-kama-wuri-zauna tana ƙara ƙarfi tun bayan da Isra’ila ta ƙaddamar da yaƙinta a Gaza a watan Oktoban 2023.
Isra’ilawa masu tsattsauran ra’ayi suna matsa lamba don a kori Falasɗinawa daga Gaza ta yadda Yahudawa ‘yan-kama-wuri-zauna za su koma can su zauna.
“Abin da ke ƙarfafa waɗannan ‘yan-kama-wuri-zaunan shi ne batun cewa Isra’ila na jin daɗin yin zalinci. Wannan jerin take dokokin ƙasa da ƙasa ne,” in ji Alhelou.
Ya zargi Bezalel Smotrich da Itamar Ben Gvir, ministocin Isra’ila biyu masu tsattsauran ra’ayi a gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu, da tunzura ‘yan-kama-wuri-zauna wajen neman "gina “sabbin garuruwa” a wajen ƙasar Isra’ila.
A watan Disamban 2024, wani gungun ‘yan-kama-wuri-zauna sun tsallake Isra’ila daga kan iyakar arewaci don shiga Labanon a ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar masu tsaurin ra’ayi, wadda ke ikirarin cewa kudancin Labanon na Yahudawa ne.
Ƙungiyar ‘yan-kama-wuri-zaunan sun tsallaka zuwa wani sashe na Lebanon wanda a yanzu haka yake ƙarƙashin ikon sojojin Isra’ila a wata yarjejeniyar tsagaita wuta mai rauni da aka cim ma tsakanin Isra’ila da Hezbolla, a cewar ƙungiyar ‘yan shi’a ta Lebanon.
“Dukkan abin nan na faruwa ne saboda goyon bayan da Amurka ta ke bayarwa marar iyaka. Turai da duka sauran duniya suna adawa da burin ƙwace matsugunai da faɗaɗawa da mamaya,” in ji Alhelou.
Mummunan burin son Faɗaɗa Ƙasar Isra’ila
Burin son “Faɗaɗa Ƙasar Isra’ila,” ya samo asali ne daga aƙidar Yahudawa masu tsattsauran ra’ayi ‘yan Zionist, wanda suke alaƙanta asalinsa daga injila suna mai cewa burin ya haɗa da mamaye Gabar Yammacin Kogin Jordan da wasu sassan ƙasar Jordan da Lebanon da ma Syria.
A yayin da ake bai wa abin fassara daban-daban, an fi yawan alaƙanta kalmar da fafutukar ‘yan-kama-wuri-zauna da kuma tsare-tsaren Isra’ila masu tsattsauran ra’ayi da ke da nufin ɗabbaƙa mulkin Zionist a dukkan ƙasashen da suke ɗaukarsu a matsayin tsohon yankin Isra’ila.
Isra’ila tana yawan doka misali da bayanan injila don tabbatar da ikirarinsu a kan yankunan Larabawa.
A taƙaice dai, Netanyahu ya kawo hujjoji na addini a bayanansa don kare yaƙin ƙare dangin da yake yi a Gaza, wanda ya kashe fiye da Falasɗinawa 62,000 a wata 22.
An ayyana mazaunan Isra’ilawa da ƙananan ƙauyukan da suke ƙwacewa a Gabar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, a matsayin haramtattu a ƙarƙashin Yarjejeniyar Geneva ta Huɗu.
Tun bayan mamaye Gaɓar Yammacin Kogin Jirdan da aka yi a shekarar 1967, Isra’ila ta gina aƙalla matsugunai 141 a kan filayen da ta sace.
Yawan ƙananan ƙauyukan da suka ƙwace ba tare da izinin gwamnati ba da ake ɗauka a matsayin haramtattu ƙarƙashin dokar Isra’ila guda 224. Akwai Yahudawa ‘yan-kama-wuri-zauna 700,000 da ke zaune a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Ƙudus.
Gaza ta durƙushe sosai saboda zalincin Isra’ila tun 7 ga watan Oktoban 2023. Amma Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye na ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan-kama-wuri-zauna da kutsen sojoji a watannin baya bayan nan, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama da jikkatar wasu.
Yawaitar matsugunan Yahudawa ‘yan-kama-wuri-zauna da ababen more rayuwarsu kamar irinsu tituna da shingayen binciken soji, na taƙaita zirga-zirgar Falasɗinawa, lamarin da ke jawo raguwar damarmakin samun ayyukan yi da kuma daƙile harkokin kasuwanci.
“An yi biris da duk wasu kiraye-kiraye na a dakatar da waɗannan haramtattun matsugunan. Ana ɗaukar Falasɗinawa tamkar ba mutane ba a tsawon shekarun nan 70,” in ji Alhelou.