Ɗan Nijeriya ya kafa tarihi bayan ya gabatar da shirye-shiryen rediyo mafi tsawo a tarihi
RAYUWA
3 minti karatu
Ɗan Nijeriya ya kafa tarihi bayan ya gabatar da shirye-shiryen rediyo mafi tsawo a tarihiGeorge Iniabasi Essien, wanda aka fi sani da Mighty George, ya shafe awa 105 yana gabatar da shirye-shirye a wani gidan rediyo a Jihar Akwa Ibom.
Ya gudanar da wannan shirye-shiryen ne a gidan rediyon Comfort FM 95.1 da ke Uyo, Jihar Akwa Ibom, daga ranar 27 ga Afrilu zuwa 1 ga Mayu. / Others
21 Agusta 2025

Wani mai gabatar da shirye-shiryen rediyo daga Nijeriya ya kafa sabon tarihi a duniya ta hanyar gabatar da shirin rediyo mafi tsawo a tarihi.

George Iniabasi Essien, wanda aka fi sani da “Mighty George” a wajen masu sauraron sa, ya gudanar da shiri na kai tsaye tsawon awa 105, kamar yadda Guinness World Records ya tabbatar.

Ya gudanar da wannan shirye-shiryen ne a gidan rediyon Comfort FM 95.1 da ke Uyo, Jihar Akwa Ibom, daga ranar 27 ga Afrilu zuwa 1 ga Mayu.

Mutumin mai shekara 43 ya samu damar hutawa na tsawon minti biyar a duk bayan kowace awa guda da ya gabatar da shirin nasa.

“Na yi wannan ne domin yin bikin cika shekaru 20 a harkar rediyo kuma na saka Jihar Akwa Ibom da Nijeriya a taswirar duniya. Wannan ahi ne tarihi na farko da mutum ɗaya ya kafa Akwa Ibom a karon farko kuma shi ne na farko a ɓangaren watsa labarai da radio a Nijeriya,” kamar yadda ya shaida wa kundin Guinness World Records.

“Na ji wani irin farin ciki da ba zan iya misaltawa ba da cikar buri a lokacin da na kafa tarihi, musamman ma kasancewa shi ne yunkurin mutum ɗaya na farko da ya yi nasara a jihar.”

George shi ne shugaban shirye-shirye a Comfort FM, kuma yana aiki a matsayin mai ɗora murya (voice actor) da kuma aikin shela a filin wasa na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasa ta Nijeriya.

Ya shafe shekaru takwas yana aiki a Comfort FM, inda yake gabatar da shirin “Comfort Breakfast Fiesta” daga karfe 5 na safe zuwa 10 na safe, tare da wasu shirye-shiryen wasanni da tsara sauran shirye-shiryen gidan rediyon.

A lokacin da ya kafa wannan tarihin, George ya yi hira da mutane daban-daban game da rayuwarsu da sana’o’insu. Ya karbi baƙuncin mutane 80 a cikin studio, sannan ya yi hira da wasu 20 ta waya.

Sun tattauna kan batutuwa daban-daban kamar wasanni, kayan ado, siyasa, shugabanci, da kuma al’amuran yau da kullum.

Da farko, ya shirya gudanar da shirin na tsawon awanni 90, amma ya ci gaba har zuwa awanni 105, har sai da gajiya ta jiki da ta kwakwalwa suka sa shi dakatarwa.

George ya ce ya fuskanci matsaloli da dama yayin wannan yunkuri. Ya yi fama da matsalolin fasaha, rashin jin dadi, rashin samun baƙi a wasu lokuta, har ma da wani mai shiga shirin ba tare da izini ba wanda ya yi barazanar lalata dukkan yunkurin sa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us