Bayanai kan ƙwallon kaɗanya da gwamnatin Tinubu ta hana fitarwa ƙasashen waje daga Nijeriya
NIJERIYA
4 minti karatu
Bayanai kan ƙwallon kaɗanya da gwamnatin Tinubu ta hana fitarwa ƙasashen waje daga NijeriyaGa wasu bayanai masu muhimmanci game da ƙwallon kaɗanya da muka tattaro, musamman daga shafin Nigeria Export Academy, wato wata cibiyar horarwa kan fitar da kayayyaki ƙasashen waje daga Nijeriya.
Ƙwallon kaɗanya abu ne mai muhimmanci da ake buƙatarsa sosai a duniya / Getty Images
6 awanni baya

Wataƙila kuna da tarin tambayoyi kan batun ƙwallon kaɗe,wanda Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da haramta fitar da shi daga ƙasar, saboda rashin daidaton da ya ce ya dabaibaye harkar.

A wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya ce: “Mu muke samar da kashi 40 cikin 100 [na man kaɗe] a duniya, duk da haka muna samun ƙasa da kashi 1 cikin 100 na darajarsa a kasuwannin duniya da ya kai dala biliyan 6.5.”

Ga wasu bayanai masu muhimmanci game da ƙwallon kaɗanya da muka tattaro, musamman daga shafin Nigeria Export Academy, wato wata cibiyar horarwa kan fitar da kayayyaki ƙasashen waje daga Nijeriya.

Ƙwallon kaɗanya, wanda ake yawan kiransa da “zinzaren mata”, Shugaba Tinubu kuma ya kira shi “koren arzikin Nijeriya”,  abu ne mai muhimmanci sosai a fannin noma na Nijeriya, sannan yana ba da gudunmawa matuƙa gaya ga tattalin arzikin ƙasar.

Da shi ne ake samar da man kaɗanya, wanda ake amfani da shi ta ɓangarori daban-daban.

Sannan a matsayinta na ƙasar da ke kan gaba waje samar da irin ƙwallon kaɗanya a duniya, Nijeriya na taka muhimmiyar rawa a kasuwancinsa a faɗin duniya.

Ƙasashen da ake kai ƙwallon kaɗanya daga Nijeriya

Ƙwallon kaɗanya abu ne mai muhimmanci da ake buƙatarsa sosai a duniya saboda yadda ake samar da mayuka da kayan kwalliya da kuma wasu nau’ukan abinci da shi.

Ƙasashen da aka fi kai ƙwallon kaɗanyar Nijeriya sun haɗa da Amurka da Birtaniya da Jamus da Kanada da Japan, da Poland da Rasha da kuma Koriya ta Kudu. 

Matakin Nijeriya a kasuwancin ƙwallon kaɗanya a duniya

Nijeriya ce take samar da kashi 45 cikin 100 na jumullar yawansa da ake samarwa a duka faɗin duniya.

An fi yin noman kaɗanya a yankunan arewacin ƙasar, kuma Jihar Neja ce kan gaba wajen samar da shi, sai Kwara da Kogi da Kebbi da kuma Kaduna.
Nijeriya ce ta fi kowace ƙasa samar da shi a duniya, inda take samar da metrik tan 500,000 duk shekara.

Miliyoyin mata ne suke aiki da hada-hada a fannin noman ƙwallon kaɗanya a ƙasar.

Me ya sa Tinubu ke so a dakatar da fitar da ƙallon kaɗanya?

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce ya ɗauki matakin dakatar da fitar da ƙwallon kaɗanyar ne saboda rashin daidito da ake samu a kasuwancinsa a ƙasashen duniya, ta yadda ƙasar ba ta cin cikakkiyar gajiyar harkar.

A wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya ce: “Mu muke samar da kashi 40 cikin 100 [na ƙwallon kaɗanya] a duniya, duk da haka muna samun ƙasa da kashi 1 cikin 100 na darajarsa a kasuwar duniya da ta kai dala biliyan 6.5.”

“Daga yanzu rashin daidaiton ya zo ƙarshe. Na amince da dakatar da fitar da ƙwallon kaɗanya na tsawon wata shida bisa shawarar kwamitin da ke bai wa Shugaban Ƙasa shawara game da harkar abinci, domin samar da shi ga masu sarrafa shi a cikin gida da samar da ayyukan yi da kuma kare wani fannin da kashi 95 na masu aiki a ciki mata ne,” in ji shugaban.

“Wannan nasara ce ga manomanmu da matanmu da ma Nijeriya. Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima zai yi aiki da masu ruwa da tsaki a lamarin domin faɗaɗa ikon sarrafa [ƙwallon kaɗanyar] cikin sauri da kuma tabbatar da cewa wannan sauyin zai kawo wadata,” a cewar Shugaba Tinubu.

Shi ma Mataimakin Shugaban ƙasa Shettima ya ce haramcin na wucin gadi zai bai wa Nijeriya damar matsawa daga matsayinta na mai fitar da ƙwallon giginya zuwa na mai fitar da sarrafaffun kayayyakin da ake samarwa daga gare shi zuwa kasashen duniya.

“Abu ne da ya shafi bunkasa masana’antu da kawo sauye-sauye a yankunan karkara, da ƙarfafa mata da kuma fadada matakin kasuwancin Nijeriya a duniya,” in ji Mataimakin Shugaban Ƙasar yayin sanarwar a fadar gwamnati da ke babban birnin tarayya Abuja.

Manufar ta gajeren lokaci, in ji shi, ita ce don ganin kuɗaɗen da Nijeriya ke samu daga cinikin ƙwallon kaɗanya sun ƙaru daga dala miliyan 65 zuwa dala miliyan 300 a duk shekara.

Amma masana sun ce ana sa ran kasuwancin ƙwallon kaɗanya zai ƙru saoda yawan amfani da ake yi da shi wajen haɗa kayan kwalliya da abinci, don haka Nijeriya tana da damar da za ta faɗaɗa kasuwarta don cin moriyar wannan harka.

Bayanai sun ƙiyasta cewa buƙatar ƙwallon kaɗanya zai ƙaru da kashi 4 cikin 100 a duk shekara a faɗin duniya, kuma akwai ɗimbin damarmaki.

Kazalika ƙwararrun na cewa Nijeriya za ta iya faɗaɗa fitar da ƙwallon kaɗanyar zuwa ƙarin wasu ƙasashen waje ta yadda hakan zai amfani gwamnati da ma masu nomansa.

 

 

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us