Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Isra’ila na so ta faɗaɗa shirinta na kisan ƙare-dangi a Gaza amma mahukunta a Ankara za su ci gaba da yaƙi da wannan shiri tare da haɗin gwiwa da Pakistan.
A yayin da yake ganawa da Firaministan Pakistan Shahbaz Sharif ranar Lahadi a birnin Tianjin na ƙasar China, Erdogan ya ce matsayin Turkiyya irin na Pakistan ne na yaƙi da kisan ƙare-dangi da Isra’ila take yi, a cewar wata sanarwa da Sashen Watsa Labarai na Gwamnatin Turkiyya ya wallafa a shafin sada zumunta na NSosyal.
"Shugaba Erdogan ya jaddada cewa Isra’ila tana neman faɗaɗa shirinta na kisan ƙare-dangi a Gaza, inda ya ce Turkiyya tana da ra’ayi iri ɗaya da Pakistan na yaƙi da kisan ƙare-dangi, sannan ya bayyana cewa ƙasashen biyu za su ci gaba da yin aiki tare ta hanyar haɗin gwiwa," in ji sanarwar.
Kazalika ƙasashen biyu sun tattauna kan alaƙar da ke tsakaninsu da lamuran da suka shafi yankinsu da ma na duniya baki ɗaya.