TURKIYYA
2 minti karatu
Shugaban Turkiyya Erdogan ya isa China domin halartar taron SCO
Wannan ce ziyara ta farko da Erdogan ya kai ƙasar China cikin shekaru biyar kuma tana zuwa ne a yayin da ake samun kyakkyawar alaƙa tsakanin Ankara da Beijing.
Shugaban Turkiyya Erdogan ya isa China domin halartar taron SCO
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Mai Ɗakinsa Emine Erdogan China. / AA
kwana ɗaya baya

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya isa birnin Tianjin na ƙasar China ranar Lahadi domin halartar taron Shugabannin Ƙasashen Ƙungiyar Haɗin Kai ta Shanghai wato Shanghai Cooperation Organisation (SCO) karo na 25 a matsayin baƙo na musamman.

Shugaba Erdogan ya sauka a filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa da ke Beijing inda ya samu tarba daga Ministan Ƙasa na China Ley Haycao, da Jakadan Turkiyya a Beijing Selcuk Unal da wasu jami’an ofishin jakadanci.

Erdogan zai halarci liyafar cin abincin dare da shugaban China Xi Jinping zai haɗa wa shugabannin da ke halartar taron na Shugabannin Ƙasashen Ƙungiyar Haɗin Kai ta Shanghai.

Shugaban Turkiyya zai gabatar da jawabi a wurin taron wanda za a soma ranar Litinin, kamar yadda Shugaban Sashen Watsa Labarai na Gwamnatin Turkiyya Burhanettin Duran ya sanar tun da farko.

Erdogan zai kasance a China daga ranar 31 ga Agusa zuwa ranar 1 ga watan Satumba.

Wannan ce ziyara ta farko da Erdogan ya kai ƙasar China cikin shekaru biyar kuma tana zuwa ne a yayin da ake samun kyakkyawar alaƙa tsakanin Ankara da Beijing.

Kazalika a lokacin taron, Erdogan zai yi tattaunawa da Shugaban China Xi Jinping game da alaƙa tsakanin ƙasashen biyu, da sauran shugabannin da kehalartar taron.

Waɗanda suka yi masa rakiya zuwa Tianjin sun haɗa da Mai Ɗakin Shugaban Ƙasar Turkiyya Emine Erdogan, Ministan Harkokin Ƙasashen Waje Hakan Fidan, Ministan Makamashi da Albarkatun Ƙasa Alparslan Bayraktar, Ministan Baitulmai da Kuɗi Mehmet Simsek, Ministan Tsaron Ƙasa Yasar Guler, Ministan Masana’antu da Fasaha Mehmet Fatih Kacır, Ministan Cinikayya Omer Bolat, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar AK Party Halit Yerebakan, Mataimakin Shugaban MHP Ismail Faruk Aksu, Daraktan Hukumar Leƙen Asiri ta MIT Ibrahim Kalin, Shugaban Sashen Watsa Labarai na Gwamnatin Turkiyya Burhanettin Duran, Shugaban Masana’antu Tsaro Haluk Gorgun, da Babban Hadimin Fadar Shugaban Ƙasa Hasan Dogan.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us