SIYASA
5 minti karatu
Majalisar Ƙoli Kan Sha’anin Tsaro ta Iran na nufin sauyin ƙarfin iko game da yaƙi
Bayan yakin kwanaki 12 da ta fafata da Isra’ila, Iran ta kafa wata sabuwar majalisar kula da harkokin yaki da ta bayar da karfin umarni ga sojoji ga na hannun daman babban jagora, matakin da ke da tasirin daidaiton zaman lafiya a yankin.
Majalisar Ƙoli Kan Sha’anin Tsaro ta Iran na nufin sauyin ƙarfin iko game da yaƙi
Figures close to Khamenei, seen here in images on display in Tehran, will form the core of Iran’s newly established defence council (AP). / AP
6 Agusta 2025

A cikin shiru da tsanaki amma cke da yin tasiri, Iran ta samar da Majalisar Koli ta Tsaro, cibiyar harkokin yaƙi wacce ke sake fasalin yadda ƙasar ke yanke shawarari kan ayyukan soji.

Sabuwar hukumar da aka kafa a wannan watan, ba ruwan ta da majalisar ministocin shugaban kasa da kuma majalisar koli ta tsaron kasa ta farar hula, inda ta bayar da ikon gudanar da aiki kai tsaye a hannun manyan sojoji daga sassa daban-daban na rundunar sojin Iran.

Sojojin sun hada da dakarun kare juyin juya hali, (IRGC), Sojoji, da Dakarun kudus - wadanda ke da alaka da babban jagoran kasar.

Wadannan sauye-sauyen na nuni da sake fasalin tsarin tsaron kasar Iran, wanda ke nuni da cewa a yanzu kasar na ganin kanta a cikin wani yanayi na gaggawar sha’anin soji.

Hakan na nuni da matsa wa daga matsakin d atake a kai shekarun da suka gabata, lokacin da hukumomin siyasa ke tsoma baki da shiga tsakani a harkokin soji, kafin a kai ga kololuwar madafun ikon kasar.

Kafa sabuwar majalisar ya zo ne bayan yakin kwanaki 12 da aka yi tsakanin Isra'ila da Iran a watan Yuni, wani dan takaitaccen rikici amma mummuna rikici da ya yi barna a biranen bangarorin biyu tare da ruguza wasu muhimman wurare.

Dakarun makamai masu linzami na Iran sun kai hare-hare akai-akai kan sojojin Isra'ila da cibiyoyin tattalin arziki, yayin da jiragen saman Isra'ila da ayyukanta na yanar gizo suka kai hari a cikin Iran tare da gurgunta cibiyoyin nukiliya tare da fallasa raunin da Iran ke da shi wajen tsaro ta sararin samaniya.

Ƙawo karshen yakin cikin bazata ya zo ne bayan shiga tsakanin da Amurka ta yi, da kuma kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, wanda ya tilasta wa ɓangarorin biyu tsagaita wuta.

Amma a kwanakin da suka gabata, jami'ai da manazarta a Tehran da Tel aviv duka sun yi na'am da wannan tsagaitwa: wannan ja da baya ne, ba wai dabarun zaman lafiya ba.

Tunda bindigogi suka yi shiru, kasashen biyu sun yi yunƙurin sake karfafa dakarun sojinsu.

Isra'ila ta shigo da alburusai masu fashewa da na'urorin tsaron makamai masu linzami na THAAD daga Amurka, kuma tana ci gaba da inganta hanyar sadarwar ta ta na’urorin radar.

A halin da ake ciki, Iran tana gyara na'urorin radar da cibiyoyin harba makamai masu linzami, tare da maye gurbin garkuwar makamai masu linzami da suka lalace, da kuma hanzarta kera makamai masu linzami, wanda a yanzu aka kiyasta suna kai wa 300 a kowane wata.

Majalisar Koli ta Tsaro ke ke kula da dukkan wadannan ayyuka, aan tsara ta karkashin umarni guda don kula da ayyukan soji, leken asiri da sake gina kasar.

Wannan sake gini na bayyana cewa lallai Tehran ta furta yadda aka bayyana raunin da take da shi wajen tsaro ta sama, ba wai ta bangaren kayan aiki ba, har ma da daukar matakai.

Nukiliya da farfadowar wakilci

Ta hanyar mika karfin iko ga wani wasu ‘yan tsiraru sojpji, sabuwar majalisar tana karfafa matsayin makusanta Ayatullah Khamenei.

A cewar bayanai daga Tehran, Ali Larijani ne ake sa ran zai zama sakataren Majalisar Koli ta Tsaro ta kasa, yayin da Ali Akbar Ahmadian zai kula da kunshin muhimman bayanai na musamman - aikin da ya shafi shirin nukiliyar, tsaron yanar gizo, da ayyukan soji na yankin.

Duk su biyun; Larijani da Ahmadian, ana ɗaukar su amintattun mutane ne a cikin majalisar Khamenei, inda tsawon looaci suka taka rawa a bangarorin siyasa, tsaro, da ayyukan soji.

Lokacin da wannan hade wa ta faru ba arashi ba ne. Jami’an Iran sun fuskanci tashe-tashen hankula na kisan gilla a ranar farko ta hare-haren Isra’ila, wanda ya kashe manyan jami’an soji a abin da kwararru da jama’a suka kira da an yi kutse a cikin gidan Iran.

Majalisar Koli ta Tsaro, ta hanyar tattara kunshin bayanai masu muhimmanci a tsakanin dan rukunin mutane amma wanda aka fi amince wa, na mayar da martani kai tsaye ga cin amanar tsaron.

A gefe guda, majalisar tana sake farfado da hanyar sadarwar Iran da kawayenta na yanki da kungiyoyin da ke wakiltar ta a kan iyakokin Isra'ila - daga Hezbollah a Lebanon zuwa mayakan sa kai a Syria da Gaza.

Jami’ai sun ce an yi hakan ne domin dakile hare-haren da Isra’ila ke kai wa yankin Iran a nan gaba ta hanyar kusantar da wannan barazana ga ita kanta Isra’ilan.

Isra'ila ta mayar da martani ta hanya mai kyau, ta yi gargadi a bainar jama'a cewa ta mallaki daruruwan makamai masu linzami, kuma a shirye take don hana sake bullar shirin nukiliyar Iran. Har yanzu guguwa yaki na iya kunno kai a yankin.

Sake fasalin tsaro da kwararan dabaru

Ƙirƙirar Majalisar Koli ta Tsaro tana aike wa sakonni da dama a lokaci guda.

A cikin gida, tana ƙarfafa tsaro don kalubalantar leƙen asiri kuma majalisar na daidaita ayyuka a tsakanin amintattun jami’an soji da ke da akida.

A matakin yanki, Majalisar Tsaron na bayyana shirin sake tunkarar wani yakin, ko ta hanyar gaba da gama ko ta wakilci da zagon kasa.

Daukar matakin sake bude cibiyoyin sarrafa nukiliya da Iran ta yi na nuni da cewa kasar ba ta razana ba, sai ma sake samun karfin gwiwa.

Ga Amurka da kawayenta na Turai, sabon kunshin sojojin na Tehran ya dagula kokarin neman mafita ta hanyar diflomasiyya.

Yayin da Iran ke shirin tunkarar duk wani abu da ka iya zuwa ya komo, Isra’ila ma na ci gaba da yin tata barazanar

Manazarta na nuni da cewa sulhun diflomasiyya mai bayar da nasara ga banrori biyu, wanda zai magance matsalolin tsaron Iran da kuma fargabar da kasashen yammacin duniya ke yi na karuwar makaman nukiliya, na iya zama hanya daya tilo mai dorewa don hana ganin wani sabon yaki.

In ba haka ba, yankin na fuskantar hadarin shiga fagen fama na dindindin, inda Majalisar Koli ta Tsaro ta daura dambar samar da dabarun farko na sojin Iran a shekaru masu zuwa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us