Dalilan da suka sanya Kamaru ba za ta manta da yaƙin da Faransa ta ƙi ambata ba
AFIRKA
10 minti karatu
Dalilan da suka sanya Kamaru ba za ta manta da yaƙin da Faransa ta ƙi ambata baMusgunawar da Faransa ta yi a lokacin gwagwarmayar neman ‘yancin kan Kamaru ta samar da tabon zaluncin mulkin mallaka da har yanzu ake muhawara a kai, kar ku damu da jinkirin Shugaba Emmanuel Macron wajen amincewa da sun aikata ta’annatin.
Kamaru ta fuskanci mulkin mallaka daga Jamus, Faransa da Ingila na tsawon shekaru.
9 awanni baya

A daren 10 ga Disamba, 1956 dakarun Faransa suka far wa kauyen Ekite na yankin Sanaga da ke lardin Littoral na Kamaru.

Ya zuwa asuba, fararen hula 500 sun mutu. Maza, mata ko yara, masu kisan ba su nuna bambanci ba a tsakaninsu.

Lamarin shi ne, kamar yadda Farfesa Hamadou Adama na Jami'ar Ngaoundere ya bayyana, "kisan kiyashin da ya fi kowane bayyanuwa" a yakin da Faransa ta yi a Kamaru ba tare da ayyana hakan ba.

Amma duk da haka, shekaru da yawa, wannan kisan gilla da sauran ta'addanci marasa adadi sun kasance a binne a cikin ma'ajiyar bayanai, kuma wata katuwar katanga ta mahukunta na musanta afkuwar lamarin.

Yarda da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kwanan nan game da "tashe-tashen hankula masu yawa" da Faransa ta aikata a Kamaru, ya sake fama raunukan da ba su warke ba.

Fahimtar zurfin waɗannan tabunna na buƙatar nazarin yadda ƙasa mai dadaddiyar wayewa da mutane dabam-daban, ta zama fagen yaƙi na ɗaya daga cikin yaƙe-yaƙe na mulkin mallaka.

Ƙasar da aka rarraba

Kafin Turawan mulkin mallaka su rarraba ta, Kamaru ta kasance mazaunar manyan wayewa a Afirka - Daular Kanem-Bornu, Daular Sokoto da Masarautar Adamawa.

Ƙasar na da kabilu fiye da 250, da suka hada da Bamileke, Bamoun, Bassa, Douala, Ewondo, Bulu, Maka, Pygmy da Kirdi.

A karshen karni na sha takwas da sha tara, wannan matattar al'adu daban-daban ba tare da ankarewa ba ta fada hannun mulkin mallaka da kacalcala ta tsakanin kasashen Jamus, Birtaniya da Faransa.

“Mulkin Turawan mulkin mallaka ya ta’allaka ne a kan falsafar da ta ginu a kan kin ‘wasu’ da kuma wayewa da al’adun da wani ya mallaka,” in ji Dokta Gassim Ibrahim na Cibiyar Bincike kan Tarihi, Fasaha da Al’adun Musulunci, yana mai bayyana falsafar ‘yan mulkin mallaka da ta ba su wannan nasara.

"Mulkin mallakar da aka yi wa Afirka ya samo asali ne ta hanyar tunanin kabilanci da ke nuna nahiyar a matsayin wacce ba ta da tarihi, ta yadda za ta tabbatar da mulkin mallaka a karkashin tsarin assasa wayewar Turai da ake ganin ita ce ta fi kowacce."

Jamus ta kafa iko a yankunan gabar tekun Kamaru a shekara ta 1884, wanda ya zo daidai da babban taron Berlin wanda aka kira don ƙirƙirar tsarin mulkin mallaka da cin gajiyar nahiyar.

Yayin da Jamus ta yi ta matsawa cikin ƙasa, sannu a hankali, yankin Adamawa ya ci gaba har zuwa 1901 kafin shi ma ya fadi gaba daya.

Biritaniya da Faransa sun shiga rarraba yankin ba da daɗewa ba, suna amfani da aikin mishan a matsayin makami. Faransa ta yada darikar Katolika yayin da Biritaniya ta yada addinin Furotesta na addinin Kirista.

Cin nasara kan Jamus ta sha a yakin duniya na farko ya sake fasalin teburin mulkin mallaka. A 1918, sojojin Birtaniya da na Faransa sun mamaye yankin kuma suka raba ganima.

Yayin da Faransa ta dauki kashi hudu cikin biyar na yankin, ciki har da kudu maso gabas, Biritaniya ta yi ikirarin kashi daya bisa biyar a bangaren yamma.

Sanarwar London ta watan Yulin 1919 ta tsaga wannan bangare a hukumance. Shekaru uku bayan haka, Majalisar Dinkin Duniya ta bai wa Biritaniya da Faransa ikon mallakar rabonsu a yankin.

Birtaniya ta raba yankinta zuwa Arewacin Kamaru da Kudancin Kamaru, tana gudanar da su tare da Najeriya. Faransa ta kafa hedkwatar mulkin mallaka a Yaoundé.

Bayan yakin duniya na biyu, tsarin ya ci gaba a karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya, amma iyakoki na wucin gadi sun ci gaba da wanzuwa.

"A Kamaru, Jamusawa sun raba yankin zuwa Gabas da Yammacin Kamaru, bisa ga muradunsu ba tare da la'akari da harkokin cikin gida ba," Dr Ibrahim ya shaida wa TRT Afrika.

Tsarin Faransa ma mai rusa kasa ne. "Wadannan manufofin sun haɗa ayyukan nuna wariya, danniya, da kuma tashe-tashen hankula da nufin sanya ƴan asalin ƙasar su shiga cikin ra'ayin ƙasƙantar da al'adunsu, sannan aka tursasa s rungmar tsarin rayuwa da wayewar Faransa tare da nuna su ne mafi girma," in ji Dr Ibrahim.

Bullar kishin kasa

Shugabanni irin su Félix-Roland Moumié da Ruben Um Nyobè su ne a sahun gaba wajen fafutukar yaki da wariyar launin fata da mulkin mallaka, inda suka kafa kungiyar hadin kan al’ummar Kamaru (UPC) a shekarar 1948 don daukar fitilar gwagwarmayar.

Um Nyobè ya kai gwagwarmaya zuwa matakin kasa da kasa. "A shekara ta 1952, ya yi jawabi a Majalisar Dinkin Duniya don yakar Faransanci a Kamaru. Moumié ya bi wannan layi," in ji Farfesa Hamadou Adama na Jami'ar Ngaoundere.

Yayin da da farko yunkurin bai taka doka ba, cin zalin da Faransa ke yi ya tilasta wa masu kishin kasa daukar makamai. Martanin Faransa shi ne shirya kisan gillar da aka yi wa Nyobé a shekara ta 1958 da kuma kashe Moumié a Geneva da wani jami'in leken asirin Faransa William Bechtel ya yi.

Daga 1956 zuwa 1961, yakin kudu da yammacin Kamaru ya cyi ajalin rayukan dubunnan mutane.

Kamar yadda sabon rahoton da aka fitar ya bayyana, "A bangaren Faransa, yakin Kamaru ya kasance wani babin da ba a san ko wane lokaci ba ne a batun tuna wa da mulkin mallaka. A bangaren Kamaru kuma, yakin ya bar tabon da ba zai gogu ba.”

Faransa ta nada Ahmadou Ahidjo a matsayin Firaminista a shekarar 1958. Lokacin da Faransa ta Kamaru ta ayyana ‘yancin kai a ranar 1 ga Janairun 1960, Ahidjo ya zama shugaban kasa na farko.

Duk da haka yakin ya ci gaba, inda sojojin Faransa ke bayar da goyon baya ga ayyukan yaki da mayakan UPC.

Max Bardet, tsohon matukin jirgin da ya yi aiki a Kamaru daga 1962 zuwa 1964, ya shaida yadda ake kai wa mutanen Bamileke hari cikin tsari.

Sojojin Faransa sun yi ruwan bama-bamai a kan kauyuka, inda suka tilastawa dubban daruruwan mutane shiga sansanonin ‘yan gudun hijira tare da azabtar da su.

Hatta mata da yara ba su tsira ba. Wadannan ta'asa an boye su cikin tsarin da Faransa ta tsara.

Bayyana gaskiya

Faransa ta yi amfani da dabaru da dama don boye ta'addancin yakin daga al'ummomin Faransa da Kamaru.

Farfesa Jacob Tatsitsa na Jami'ar Ottawa a Kanada ya yi bincike kuma ya yi rubuce-rubuce sosai game da tsarin rufa-rufar.

"Da farko, a shekarar 1955, musamman bayan da Faransa ta sha kaye a Indochina, ta yanke shawarar koya wa Kamaru darasi kan yakin juyin juya hali, wani tsari da za a aiwatar da shi na haramta gwagwarmayar 'yan kishin Kamaru," in ji shi.

Sanarwar da Roland Pré ya bayar, wanda aka nada  babban kwamishinan Kamaru a shekarar 1954,  ta bayar da izinin kafa gidajen jaridu da za su yaba wa gwamnatin Faransa yayin da ake rainawa da wasa da gwagwarmayar neman ‘yancin kai.

A wani bangare na dabarun, an rufe yankunan da ake yaki ga 'yan jarida. Kadan da suka samu dama su ne wadanda ke da hannu a cikin ayyukan sirri na Faransa.

Bayan samun ‘yancin kai, a tantancewar ta ci gaba sosai, in ji Tatsitsa.

Duk wanda aka samu da takardun da ke goyon bayan jam’iyyar UPC, yana fuskantar kamawa da dauri a karkashin abin da ake kira dokar hana zagon kasa.

Takaddamar ta ci gaba har zuwa Faransa daga baya, tare da dakatar da littafin Main basse sur le Cameroun na Mongo Beti sakamakon nazarinsa cikin tsanaki da suka kan halin da ake ciki a Kamaru.

Tatsitsa ta ce "'Yancin cin gashin kai a baki kawai na nufin an kawar da duk wani abu da ‘yancin ya kamata ya samu, saboda Faransawa sun kutsa kai cikin duk wani mukami na mulki."

Tsarin da aka rarraba al’umma a kai

Tabon zamanin mulkin mallaka na ci gaba da yaduwa a fadin kasar Kamaru.

Lokacin da ‘yan Kudancin Kamaru suka kada kuri’ar raba gardama a watan Fabrairun 1961 don hadewa da Jamhuriyar Kamaru (lokacin da Arewacin Kamaru ya koma Najeriya), kasar ta gaji tsarin mulkin mallaka masu cin karo da juna.

Gabashin Kamaru ya ɗauki al'adun Faransanci, harshe, doka da ilimi. Yammacin Kamaru ya ɗauki kwatankwacin na Birtaniya.

"Duk da cewa yankunan Kamaru biyu sun hade a karkashin tsarin tarayya, abubuwan da suka gada na mulkin mallaka da suka gada kuma suka nemi kiyayewa sannu a hankali sun zama tushen rikici," in ji Dr Ibrahim.

Sauya wa daga tarayya zuwa tsarin hadewa waje guda a 1972 ya shaida yadda yawancin masu magana da Faransanci - kusan kashi 80% na yawan jama'a - suna aiwatar da manufofin haɗaka kan tsiraru masu magana da Turancin Ingilishi.

"Wannan matsalar ta kara ta'azzara a tsawon lokaci kuma, a shekarar 2016, ta rikide zuwa gwagwarmayar daukar makami karkashin jagorancin al'ummar Anglophone da ke neman cikakken 'yancin kai. Har zuwa yau, ba a magance wannan matsalar da aka shigo da ita kasar daga waje ba," in ji Rues Dr Ibrahim.

Ko bayan janyewar Faransa a hukumance, masu ba Faransa shawara sun kasance like a cikin gwamnatin Kamaru, sojoji da 'yan sanda, wadanda ke samun goyon bayan masu hadin gwiwa na cikin gida. An boye mutuwar dubunnan dubbai da gangan.

Sauraron diyya

Yayin da  amincewar Macron ya karya shiru na shekaru da yawa daga hukumomin Faransa, har yanzu matsalar na kara ruruwa a kunnuwan 'yan Kamaru da yawa.

Tatsitsa ta ce "Ga 'yan Kamaru, wannan amincewar ta zo a makare kuma ba ta cika ba, saboda kalmar 'biyan diyya' ba ta cikin wannan wasiƙar.

Har yanzu muna jiran neman bayyana afuwa da biyan diyya, sa'an nan kuma a buɗe rumbun adana bayanai, a ƙididdige shi kuma a bayar da shi ga duk masu bincike.

Dr Therence Atabong Njuafac, wanda ke da digiri na uku a fannin alakar kasa da kasa da kimiyyar siyasa da kuma take matsayin shugabar kungiyar ‘Humanity Helping Hands Cameroon’ mai taimaka wa mutane, ta yi nuni ga hadin baki a wannan bangare na tarihin kasar da ya rage a binne.

“Shugabanninmu na da alaka mai karfi da kasar Faransa, kuma ga dukkan alamu suna hada kai ta bangarori da dama, har yanzu Faransa na da sauran aiki a cikin kasar, hatta kudaden mu ana buga su ne a Faransa, don haka za ka iya bayyana yadda har yanzu kasashen biyu ke da alaka da juna. "Wataƙila talakawa sun yi fushi da Faransa, amma ba gwamnati ba."

Adama ta yi magana game da wasiƙar Macron inda ta ce ta bar "ɗanɗano mai ɗaci" maimakon waraka.

"Faransa ba ta magance batun biyan diyya ba, ba tabo batun adalci ba. Wasikar na kokarin boye bayan ne tare da samun iko kan batun baki daya.”

Amma Dr Ibrahim na ganin wannan lokacin a matsayin wata dama. "Bayan kalaman na Macron, na yi imanin cewa lokaci ya yi da za a sake duba tarihin gwagwarmayar Kamaru da turawan mulkin mallaka na Faransa, ta hanyar komawa wurin adana kayan tarihi," in ji shi.

Ko da yake dai ba a amsa wasu tambayoyi masu mahimmanci ba. "Shin masana tarihi da masu bincike za su yarda su bankado wadannan ma'ajiyoyin bayanan?

Kuma ita kanta Kamaru za ta kyale da karfafa irin wannan aiki?" Dr Ibrahim ya tambaya cikin mamaki.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us