SIYASA
13 minti karatu
Yayin da bango ya fadi: Me ake nufi da zama uba a Gaza
A Gaza, da kowane dare ke zuwa da sabon ta’addanci, mahaifi na nufin gwagwarmayar kare yaransa daga sharrin duniyar da ke ruguzo wa a kansu.
Yayin da bango ya fadi: Me ake nufi da zama uba a Gaza
Amid the rubble of Gaza, a father carries the weight of protection he can no longer promise / AP
5 awanni baya

Na yi rayuwa cikin yaƙe-yaƙe da yawa a Gaza, tun daga ƙuruciyata har zuwa yau. A baya, yaki kamar bako ne da ba a so ya zo ya tafi, kuma ya bar tabo da yawa.

Lokaci ya warkar da wasu daga cikin waɗannan tabbai, yayin da wasu suka ci gaba da kasancewa masu raɗaɗi kuma ba za a iya goge su ba. A lokacin kowane yaƙi, na kasance cikin inuwar tsoro da firgita: tsoro na asali, tsoro ga iyaye da ’yan’uwana, da tsoro ga dangi da abokai na kusa.

Amma yanayin ya canza sosai a 2017 lokacin da na zama uba a karon farko. Tsoro ya daina zama cikin yin shiru a zuciyata; ya zama duk mai mamaya. A yau, a matsayina na uban yara uku, ina ɗauke da wannan tsoro ninkin ba ninkin, saboda yarana suna ganina a matsayin mai ba su kariya, na gamsu cewa zan iya kare su daga ta'addancin da suka fara fahimta.

A wannan lokacin, ya zama wajibi na in amsa manyan tambayoyin da suke yi min. Sun kasance suna sane da al'amura masu rikitarwa da yaƙi ya ​​haifar: tambayoyi na rayuwa da mutuwa, na hatsari da aminci, na zama da tafiya, na ƙwaƙwalwa da mantuwa.

Sun tsinci kansu ba zato ba tsammani a kewaye da sauti da hotuna masu ban tsoro, sun makale a wani lungu da babu hanyar fita, ba su da ikon hana abin da ke faruwa.

Rawar da uba ke taka wa a falsafa da yaki

Shekaru da dama da suka gabata, makaho mawaki kuma masanin falsafa dan kasar Syria Abu al-Alaa’ al-Ma’arri (973–1057) ya koka da wata matsala ta ɗabi’a da ke jin ina kusantar ta a yanzu: shin za mu kawo yara cikin duniyar zalunci da tashin hankali?

Al-Ma’arri ya rasa ganinsa tun yana yaro, kuma ya shafe yawancin rayuwarsa a keɓe a garinsu mai suna al-Ma’arra. Wani mai tunani mai tsattsauran ra'ayi, abin sha'awa dmuka mau wuyar sha’ani, ya ƙi amince wa da yawancin tarurruka da aka yi a zamaninsa, yana kalubalantar addini, al'ada, har ma da ainihin haihuwa. A kan kabarinsa, ya ce a rubuta waɗannan kalmomi: “Wannan laifin mahaifina ne a kaina, ba kuwa zan yi wa kowa irin sa ba.”

A wajen sa, samun ‘ƴa’ƴa ba kyauta ba ne, tsagwaron zalunci ne, haka kawai a yanka wa wasu kazar wahala da ba dole ba.

Ya bayar da hujjar cewa jinkai na gaskiya yana cikin ƙin kawo ƙarin rayuka cikin duniyar da ke nutsewa cikin muni da ɗacin rayuwa. A kallo na farko kalamansa ba su yi ba, har ma sun zama na son kai. Sai dai kuma, akwai tsantsar ɗabi'a a cikin su, tunani game da duniyar da ke ƙara fada wa cikin halaka.

Hangen Al-Ma’arri ya tsaya gaba ɗaya ga ra’ayin gargajiya game da mahaifi: uba a matsayin garkuwa, majiɓincin rayuwar ‘ya’ya, da kuma mai tarbiyyantarwa, tushen aminci da mallaka.

Shekaru da yawa, na riƙe kalmominsa a raina tare da shiga tsakai mai wuyar girmamawa da tsoro.

A matsayina na mai son yara, na kasance, kuma har yanzu ina sha'awar ra'ayin ajje iyali. Amma duk da haka ina tunanin ba zan samar da iyali a irin wannan mummunan wuri, kuma hakan zai fi zama matakin nuna jin kai.

Duk da haka, watakila saboda irin wannan ilhami, na sami kaina a cikin nisantar samar da iyali da haihuwa. Wannan lamari ne mai daɗi - amma mai haramta wa mutum abubuwa da yawa.

Don haka, bayan ’yan shekaru da yin aure, na sami kaina a matsayin mahaifin yara uku. Iyakar abin da zai yiwu, na yi ƙoƙari na zama uba da ke iya auke dukkan nauyin da ke kan mahaifi. Hakan ya yiwu tare da ci gaba da kasancewa har zuwa lokacin da aka fara yaki, a lokacin da aka lalata dukkan siffoin da na ke da su na matsayin mahaifi.

Yakin ya sake fasalin matsayin mahaifi ga ni da kuma ’ya’yana, ya kawar da dukkan rawar da aka saba taka wa tare da barin mu da sabuwar rawa marar dadi.

Taka rawa a matsayin mahaifi a loakcin yaki

Wata guda bayan yaƙin, mun fuskanci tashin bama-bamai mafi girma a kusa da gidanmu da ke birnin Hamad, Khan Younis. Wannan daren shi ne jarabawar zaluntar mahaifi ta farko a idanun yarana.

Tashin bam din ya fara ne kwatsam da tsakar dare, lokacin da wasu abubuwan fashe wa da dama suka haskaka birnin da haske kalar ja da ruwan dorawa. Sautin ya girgiza bangon ɗakin kuma ya jefa tsoro a zukatanmu. Muka fake a wata maboya a gidanmu, tsoro ya kama mu.

Babban yarona, Baraa ɗan shekara takwas, yana karkarwa, tare da makyarkyata da labba jajaye. Ya rike ni yayin da jikinsa ke kara yin sanyi. Wannan ba kawai tsoro ne na wucin gadi ba, amma an gama firgita yaro da bai san komai ba sai tabbacin gidanmu da muryata.

Duk da haka ban iya kwantar masa da hankali ba, ko ma na shawo kan tsoro na game da shi. Na yi ƙoƙarin nuna masa cewa muna cikin aminci, kuma bama-bamai ba su da kusanci kamar yadda ake gani. Amma ta yaya zai yarda da ni lokacin da bango ya girgiza, lokacin da kamshin abubuwan fashewa ya cika iska, lokacin da ya ga hasken fashewar ya bayyana a cikin tsoro a idanuna, ya ji ni ina karkarwa kamar shi?

Na ji kamar na zama wanda ke ƙoƙarin shawo kan wuta cewa ruwa ba zai kashe ta ba. Amma duk da haka na damu zai mutu sabod ata’addanci. Don haka na gaya masa: “A cikin ’yan sa’o’i kaɗan, rana za ta fito, kuma da zarar ta fito za mu bar gidan mu tafi wani waje mai tsaro sosai.” Baraa ya fara rokon ganin rana ra fito da wuri.

Da gari ya waye Bara'a ta tuna min cewa muna bukatar mu bar gidan kuma yana son zuwa wani wurin daban.

Yayin da yake roƙon rana da ta yi sauri ta fito, na fada wa kaina cewa na yi kuskure, na yi rashin hankali, da son kai don in haifi ’ya’ya a nan, a wannan yanki na duniya da aka yanke wa hukuncin kisa.

Kuma yadda na zama babu wani katabus a yanzu: na gaza gamsar da shi cewa ni uba ne da zan kare shi daga mutuwa, na kasa bayyana masa irin rikicin da zai fuskanta tun yana da ‘yan shekaru a duniya. Wanne irin kuskure ne haka, Kuskuren da ba za a yafe ba.

Wannan daren ya kawo babbar matsala kan matsayina na mai ba shi kariya a zciyarsa. Sannan ni ma ya lalata tunanina na matsayin uba.

Don gyara wannan tunani marar kyau, ko da dan kadan, na yanke shawarar cewa dole ne mu gudu kafin bama-bamai su matso kusa, kafin yarana su sake shaida wani daren mai ban tsoro irin wannan. Na yanke wannan shawarar ba don na yi imanin cewa zan iya samar mu da tsaro ba, kawai sai don ina kokarin neman yafiya saboda kawo su cikin wannan wahala.

Ba zan iya bayar da tabbacin wannan shawarar za ta yi nasara ba. Amma hakan ya zama hanyar guje wa jin na aikata laifi a lokacin da na kalli idanun ’ya’yana, da fargabar da ta lullube su, a lokacin da suka fahimci ba ni da wani ikon ba su kariya.

Ta haka ne aka fara raba mutane da matsugunansu, inda muka gudu saboda tsoron me yaran za su fuskanta, zuwa wuraren da nake tunanin za su fi aminci.

Burodi ba wai litattafai ba

Yunwa ta farko a Gaza ta fara ne a watan Nuwamban 2023. Garin fulawa ya bace daga kasuwanni, gidajen burodi sun rufe, an kuma wawashe abinci daga rumbun ajiyar UNRWA, wanda ke dauke da tan da dama na garin fulawa.

Lokacin da na sami nasarar siyan buhun sata guda ɗaya na garin fulawa a kan farashi mai yawa, sai na ji kamar na mallaki wata taska.

Mun fuskanci wani baƙin farin ciki mai cike da kaskanci da rudani, domin fulawa kaɗai ba za ta iya yin burodi ba, kuma ba mu da wata hanyar suya, bayan iskar gas ɗin dafa abinci ba ta samu wa.

Dole ne muka gasa burodi ta hanyar amfani da tandar laka, irin tandar gargajiya da mazauna karkara ke amfani da ita. Ire-iren wadannan tanda sun zama ruwan dare a ko’ina, kuma matan kauyen, cikin ruhin hadin kai da karamci, suna gasa burodi bisa sharadin cewa iyalan da ke son burodin su ba da mai, kamar katan-katan ko littattafai.

A wani yammaci, matata ta kalli rumfuna da na gina shekaru da yawa kuma ta ce a hankali: “Ciyar da yaran yanzu ya fi yi musu karatu.” Maganar ta kasance kamar mari a fuska: Ban taɓa tunanin dakin karatuna zai zama wajen gasar yara masu fama da yunwa ba.

Gaskiya ta bayyana a gabana karara. Idan aka kwatanta da yunwar ’ya’yana ke fuskanta a lokacin wannan yaƙin, to sai a ce abubuwan da ke cikin littattafan ɗakin karatu na ba su da amfani. Na kidimu tare da tsorata game da yanayin da tsinci kaina a ciki. Ta yaya abubuwa suka kawo haka da sauri?

Babu zaɓi da yawa, amma ko ta yaya, na sami nasarar shawo kan matsalar da na tsinci kaina a ciki. Wannan wata jarrabawa ce mai cike da kalubale.

Wasu na iya tunanin cewa na yi fushi saboda babu abin da ya fi muni sama da a ce ka kasa kawar da yunwar da yaranka ke ji.

Ko da yake na sami isasshen man da zan gasa wa yaran burodi, ba tare da na kona littatafai na ba, lamarin ya kasance wani tabo na farko a tunanina na matsayin uba.

Yanzu an fara samun matsaloli manya. Na taɓa zama uba da yake tunanin zai iya ceton ’ya’yansa daga yunwa, ba tare da barin yaƙin ya lalata masa ruhi, tunani, ko wanzuwar sa ba.

Raunin rawar da mahaifi ke taka wa

A watan Disamban 2023, bayan motocin sojoji sun shiga Khan Younis, na yanke shawarar cewa dole ne mu gudu tare da yaran, bayan da na yi wa kaina alkawarin ba zan sake jefa su cikin mummunan ta'addancin da tabbas zai biyo bayan wadannan tankunan yakin ba.

Muka nufi zuwa Rafah. A darenmu na farko a can, ina ƙoƙarin rufe idanuna don barci, sautin numfashi da minshari tare da tari sun cika ɗakin.

Basil, dan ƙaramin su, yana fama da matsananciyar mura kuma da ƙyar yake iya numfashi. Fuskarsa tayi jajawur, zazzabin ya tashi zuwa wani yanayi mai tsanani da sanya damuwa.

Karfe daya na dare, na zauna kusa da shi ina kokarin kwantar masa da hankali, don na dan rage radadin da ke damun sa. Na rike shi a hannuna ina tafiya gaba da baya a daki,ina kokarin kwantar masa da zafin zazzabin amma ban samu nasarar cim ma hakan ba.

Numfashinsa ya takure, na fara ganin wani irin tsoro a idanunsa wanda ban saba gani ba. Na ji rashin samun taimako da kadaici sun cika cikina, kamar bakin gajimare.

"Da a ce ina Khan Younis, kusa da mahaifiyata, da ta san abin da za ta yi," na gaya wa kaina. “Da a ce ina kusa da ’yan’uwana, ko kuma aƙalla a wurin da zan san inda zan nemi taimako!”

Na ji karyewar uba da na zaci na zama irin sa. A nan, a tsaka da yaƙi, ni ba mai jibintar lamarin yarana ba da nake marmarin zama hakan.

Amma duk da haka babu wani zabi illa ci gaba. Na fita daga dakin na shiga wata doguwar hanya da mutane da yawa ke kwace: wani mutum dan shekara talatin, da dattijo biyu, da wasu samari. A hankali na matso kusa da wani mutum na talatin da wani abu na tashe shi a hankali.

Ya bude ido a hankali yana rada min "Mene ne?"

"Ɗana ba shi da lafiya," na ce masa. "Yana tari da yawa, yana da zazzabi mai zafi, kuma yana fama da wahalar numfashi. Za ku iya taimaka min?"

Ya yi kokarin tada kansa gaba daya. "Gaskiya, ban san abin da zan iya yi ba, amma jira… bari in tayar da Abu Bayan, shi ma'aikacin harhada magunguna ne kuma zai iya taimaka wa," in ji shi.

Muka tashe shi tare. Abu Bayan kamar mutum ne mai natsuwa, annashuwa, mai siffar mutunci mai sanyaya zuciya. Tashi ya yi daga kan gadonshi ya ce "Lafiya me ke faruwa da yaron?"

Nayi masa bayanin abinda ke faruwa, ya gyada kai cikin fahimta. Sai ya ce, “Ba ni da maganin da ya dace, amma dau ku dakko wannan hodar ku rika shafawa a kafarsa, sai a sha wannan kwayar maganin, a raba biyu, sai a narkar da rabi a cikin cokali daya na ruwa, a yi kokarin ba shi ya sha, hakan zai taimaka, in sha Allahu.

Na dauki maganin na koma zuwa ga Basil. Kusa da shi na zauna na fara yin abin da Abu Bayan ya ce na yi. Abin da nake tunani a lokacin shi ne: “Shin Basil na gani na yadda nake so ya gan ni, a matsayin uba da zai iya kāre shi? Ko kuwa yaƙin ya ɓata wannan matsayin?”

Amma duk da haka na yi tunanin cewa ko a lokacin rauni na, ina ƙoƙarin zama mai taimaka masa. Wataƙila ba zan iya ba shi magani ko aminci ba. Ba ni da dukkan amsoshi, amma ina da ƙauna, kasancewa da shu, da nuna dagiya — ƙananan ginshiƙai bayar da kāriya a cikin duniyar da duk wani abu ke ruguje wa.

A wannan yaƙin, An ruguza ginshiƙan zama mahaifi, kuma sifar uba da ta daɗe tana jan hakali a al'adunmu ta wargaje.

A yanzu mahaifi ba wai wani bijimi zai iya jurewa ya bayar da kariya daga hatsari ba ne, a’a ya zama wanda aka tsayar a tsakanin tsoro da rauni, a tsakanin wanda kamar ba shi da ‘ya’ya da jin cewa yana da nauyin da ya kasa cika wa.

Matsayin uba a nan ba ya nufin rainon yara kaɗai. Har ila yau, ƙwarewa ce mai zurfin gaske, wanda dole ne mutum ya fuskanci ci gaba da rushewar kansa, a inda kuma halayya da radadi suka hadu waje guda, kuma buri da hakika suka ci karo da juna.

A cikin wannan mugun gwaji, uban ya ƙunshi ma'anar ƙauna da sadaukarwa. Duk da raunin da yake da shi, yana ƙoƙarin ƙirƙirar sabuwar rayuwa ga 'ya'yansa daga toka na lalacewa. A cikin zuciyarsa yana amsa tambayoyin rayuwa, mutuwa, da ma'ana, a cikin duniyar da babu aminci kuma gaba tana shuɗewa.

Matsayin mahaifi, a yanzu, ba ya ƙunshi ayyukan yau da kullun ba ne kawai: a maimakon haka ci gaba ne na tunani da wahala, da kuma neman wani ɗan haske a cikin duhun duhu.

An fara buga wannan labarin tun asali da Larabci a shafin 7iber.com  kuma Samuel Bollier ya fassara shi zuwa Turanci.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us