Kimanin kashi 63 cikin 100 na mutanen Faransa suna son a rusa Majalisar Dokokin Ƙasar tare da neman a sake sabon zaɓe, in ji ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a da kamfanin IFOP ya yi wa gidan talabijin ɗin LCI TV ranar Laraba, yayin da Firaminista Francois Bayrou ke ƙoƙarin kare gwamnatin ta ‘yan tisraru.
Ƙuriar jin ra’ayin jama’a ta IFOP ta ji ra’ayoyin mutum 1,000 ta hanyar intanet ranar 26 ga watan Agusta.
Bisa ga dukkan alamu za a kayar da gwamnatin ‘yan tsiraru ta Bayrou a watan gobe bayan manyan jam’iyyun adawa— daga masu ra’ayin riƙau zuwa ra’ayin ‘yan mazan jiya — suka ce ba za su goya masa baya ba a zaɓen amincewa wanda Bayrou ya sanar da cewa za a yi zaɓen ranar 8 ga Satumba, kan shirye-shiryensa na rage kasafin kuɗi sosai.
Dorewar gwamnatinsa ta dogara kan zaɓen amincewa kan rage Yuro biliyan €44 daga kasafin kuɗi wanda ya haɗa da soke hutun ƙasa na kwanaki biyu da dakatar da kuɗin tallafi, matakan da suka jawo rashin amincewa na mutane da yawa.
Rashin tabbas na siyasa ya yi tasiri kan kasuwar hannayen jari na Faransa a wannan makon.
Boris Vallaud, wanda ke jagorantar ‘yan adawa masu ra’ayin gurguzu a majalisar dokokin ƙasar, ya bayyana wa gidan talabijin na BFM TV cewa Faransa na buƙatar sauya tafiya, kuma wannan na nufin sauya Firaminista.