AFIRKA
2 minti karatu
Nijar za ta taƙaita wuraren samun biza ga wasu 'yan ƙasashen Turai a wani mataki na mayar da martani
Ofisoshin jakadancin Nijar a Geneva da Ankara da kuma Moscow ne kaɗai suke da izinin bai wa ‘yan wasu ƙasashen Turai bizar shiga ƙasar Nijar.
Nijar za ta taƙaita wuraren samun biza ga wasu 'yan ƙasashen Turai a wani mataki na mayar da martani
Nijar ta takaita wuraren samun biza ga wasu 'yan ƙasashen Turai a wani mataki na mayar da martani. / TRT Afrika Français
7 awanni baya

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce za su taƙaita inda ‘yan wasu ƙasashen Turai za su iya samun bizar shiga ƙasar da ke yankin Sahel, sakamakon matsala da su ma ‘yan Nijar ke fuskanta wajen samun bizar shiga Turai daga ofisoshin jakadancin ƙasashen.

Hakan na zuwa ne bayan da Ministan Harkokin Wajen ƙasar Bakary Yaou Sangare ya koka kan yadda ‘yan Nijar ke ci gaba da tafiya zuwa ƙasashen da ke maƙwabtaka da ƙasar domin kammala ƙa’idojin samun biza, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Ministan ya ce Nijar ta gabatar da buƙatar a bai wa ofisoshin jakadancin Turai da ke Yamai izinin ba da biza a wurin, wanda a cewarsa, "ba a samu amsa ba kawo yanzu".

"Daga yanzu ofisoshin jakadancin Nijar a Geneva da Ankara da Moscow ne kaɗai ke da izinin ba da bizar shiga Nijar ga 'yan ƙasashe kamar: Italiya, da Netherlands, da Tarayyar Jamus, da Masarautar Belgium, da kuma Birtaniya," in ji Ministan.

'Ƙa'idar mayar da martani’

Wannan matakin dai na daga cikin "ƙa'idar mayar da martani", in ji shi.

Ministan ya ƙara da cewa, waɗanda ke riƙe da fasfo na aiki ƙasa da ƙasa wato ‘Diplomatic Passports’ za su iya samun biza a ofishin jakadancin Nijar da ke Brussels.

A baya dai 'yan Nijar na iya samun bizar shiga yankin ƙasashen Turai wato Schengen cikin 'yanci ta hanyar ƙaramin ofishin jakadancin Faransa da ke Yamai babban birnin ƙasar.

Sai dai a yanzu da alaƙar Nijar da tsohuwar uwargijiyarta ta yi tsami, inda hukumomi a Yamai suka ta kori jakadan Faransa da ma dakarun ƙasar, samun hakan na da wahala.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us