KIMIYYA DA FASAHA
3 minti karatu
Afirka za ta iya zama 'kan gaba a fannin sabunta makamashi': Sakatare Janar na MDD
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce Afirka na buƙatar ƙarin kuɗaɗen rangwame da kuma ƙarfin bayar da lamuni daga bankunan raya ƙasa da dama.
Afirka za ta iya zama 'kan gaba a fannin sabunta makamashi': Sakatare Janar na MDD
Sakare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci a kara yawan hannu jari a hanyoyin magance sauyin yanayi. / Reuters
8 awanni baya

Afirka na da duk abin da ake buƙata don zama "kan gaba a fannin sabunta makamashi", in ji Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres a ranar Alhamis, yayin da ya yi kira da a ƙara zuba jari a fannin makamashi mara gurɓata muhalli a faɗin nahiyar da ke da albarkatun ƙasa masu ɗimbin yawa.

Guterres ya yi wannan jawabi ne, a wani taron raya ƙasa na kwanaki uku da aka gudanar a ƙasar Japan wanda ya samu halartar shugabannin ƙasashen Afirka, inda Tokyo ke ƙokarin maye gurbin China a daidai lokacin da ƙasashen Afirka ke fama da matsalar basussuka sakamakon raguwar tallafin da ƙasashen yammancin duniya ke bayarwa, da kuma rikici da sauyin yanayi.

“Dole ne mu haɗa kuɗi da fasahar ƙere-ƙere ta yadda albarkatun ƙasa na Afirka za su amfani jama’ar nahiyar, kana dole ne mu gina wani sashe na makamashi mai inganci tare da sabunta masana’antu a faɗin nahiyar,” in ji Guterres a yayin taron Tokyo na ƙasa da ƙasa kan ci gaban Afirka (TICAD).

“Makamashi mara illa a Afrika yana rage farashin makamashi, yana iya kawo sauyi a hanyoyin tattalin arziki tare da rage gurɓatacciyar iskan Carbon ga kowa.’’

China ta zuba jari sosai a Afrika cikin shekaru 10 da suka wuce, inda kamfanoninta a can suka ƙulla yarjejeniyoyi na ɗaruruwan biliyoyin dala don ba da gudunmawar ayyukan sufurin jiragen ruwa da layin dogo da tituna, da sauran ayyuka a ƙarƙashin shirin samar da ababen more rayuwa na duniya na Beijing.

Sai dai batun ba da lamuni yana zama wani ƙalubale, kana ƙasashe masu tasowa suna fama da lodin basussuka na China da saura masu ba da lamuni masu zaman kansu na ƙasa da ƙasa, kamar yadda Lowy Institute, wata cibiyar nazari ta Australia, ta bayyana a watan Mayu.

Kazalika ƙasashen Afrika sun fuskanci raguwar tallafin da ƙasashen yammacin duniya ke bayarwa, musamman saboda ruguza Hukumar Raya Ƙasashen Duniya ta Amurka (USAID) da Shugaba Donald Trump ya yi.

Guterres ya yi gargaɗi kan haka a jawabin da ya yi a birnin Yokohama na tashar jiragen ruwa na ƙasar Japan da cewa, "kar bashi ya ruguza ci gaba" Afirka na bukatar ƙarin kuɗaɗen rangwame da kuma ƙarfin bayar da lamuni daga bankunan raya ƙasa da dama.

Ya kuma buƙaci a ƙara saka hannayen jari a hanyoyin magance sauyin yanayi.

"Afrika na da duk abin da ake buƙata don zama nahiya mai ƙarfi a fannin sabunta makamashi mai tsafta, tun daga hasken rana na sola da iska zuwa ma'adanai masu muhimmanci da ke samar da sabbin fasahohi," in ji shi.

Waɗanda suka halarci taron na TICAD sun haɗa da shugaban Nijeriya Bola Tinubu, da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da shugaban Kenya William Ruto.

Shugaba Ruto ya wallafa a a shafinsa na X cewa, Kenya na tattaunawa da wani kamfanin ƙera motoci na ƙasar Japan Toyota don samar da motocin “e-mobility” guda 5,000 a matsayin wani ɓangare na “ƙoƙarin da ƙasar ke yi na amfani da tsaftace makamashi”.

A jawabinsa na buɗe taron a ranar Laraba, firaministan ƙasar Japan, Shigeru Ishiba, ya bayyana shirin horar da mutane 30,000 a fannin ƙirƙirarriyar basira ta AI a Afirka cikin shekaru uku, tare da yin nazari kan manufar haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin Japan da Afirka.

Kafin a fara taron, Ishiba ya kuma fitar da sanarwar wani shirin gaba da zai haɗa kasashen Afrika da ƙasashen yankin tekun Indiya.

Shugaba Tinubu da Ramaphosa, su ma sun bayyana a shafin X cewa suna son canja akala daga ƙarɓar tallafi zuwa haɗin gwiwar zuba jari.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us