KIMIYYA DA FASAHA
11 minti karatu
Iyakar ikon kasashe kan Kirkirarriyar Basira da abin da hakan ke nufi ga tsarin tafiyar da duniya
Kasashe na gwagwarmayar saba wa da yanayin da wannan fasaha da ke habaka cikin sauri ke kawo wa. A yanzu ana rige-rige da lokaci.
Iyakar ikon kasashe kan Kirkirarriyar Basira da abin da hakan ke nufi ga tsarin tafiyar da duniya
AI na alkawarin amfanar da ayyukan soji kuma babu wata kasa da ta san me take yi da za ta saurara. / AP
20 Agusta 2025

A watan da ya gabata, China ta gabatar da tsare-tsare na wata kungiya ta duniya don kula da bayanan sirri da aka tsara kan daidaitaccen damar amfani da fasaha, zurfafa hadin gwiwa a iyakokin juna, da matakan saukaka kalubalen da ake fuskanta wajen musayar basira.

Watanni shida kafin hakan, kasashe 58 sun gana a birnin Paris don amince wa da wata sanarwa kan “AI na bai daya mai dore wa," inda Amurka da Birtaniya suka ki sanya hannu.

Hanyoyin sun bambanta, amma tsarin iri ɗaya ne. Gogayya don sarrafa Kirkirarriyar Basira na habaka da sauri fiye da kowane ƙoƙari na sanya masa dokoki.

Kirkirarriyar Basira na habaka karfi ga tattalin arzikin kasashe manya, tsarin tsaro da karfinsu a yankuna.

A shekaru goma da suka gabata, Kirkirarriyar Basira ta matsa daga dakunan gwaje-gwajen fasaha zuwa matsayin wani makamin da soji ke bukata, kayan da gwamnatoci ke sayo wa da matsayin manyan bukatu na aiki.

Batun ko za a iya shawo kan Kirkirarriyar Basira ya tashi daga dakunan kara wa juna wa sani zuwa majlisun zartarwa na kasashe.

Lokacin da irin wannan tsarin zai iya taimakawa wajen cin jarrabawar lasisin aikin likita, kuma wata rana a samar da bidiyoyi na karya zalla, a bayyana yake a fili cewa kayan aikin sa ido na yau ba su dace da habaka cikin sauri, fadi, ko isa ga mutane irin Kirkirarriyar Basira ba.

An gina ginshiƙan ƙa'idodi na yau don kananan cigaba da manhajojin da ake da su. Ba a tsara su saboda tsare-tsaren da za su iya samar da rubutu kamar na ɗan adam ba, ya yi nazarin hotunan tauraron dan adam a cikin ‘yan sakan, ko sarrafa injina da kansu.

Wannan gibin na janyo ana yin kiraye-kirayen samar da sababbin hanyoyin gudanarwa da za su iya mayar da martani ga fita daban, matsaki da fuska biyu ta amfani da fleets ke da su.

Muhawarar a matakin kasa da kasa na mayar da hankali ga yadda sabbin fasahohi na zamani ke sauya hatsarin afkuwar yaki da samar da zaman lafiya.

Wani cigaban na iya rage hatsarin ta hanyar yin bincike da tantancewa, sadarwa da dakatarwa.

Wasu, musamman ma waɗanda ke bayar da dama a fagen yaki, na kara yawan kuɗadein soja da kuma ƙara gogayyar mallakar makamai. Hikimar bi daya ita ce Kirkirarriyar Basira ta fada cikin rukuni na biyu.

Nasarar Kirkirarriyar Basira wajen sa ido, nufar abu daidai, da tsare-tsaren injina masu aiki da kansu na ƙarfafa fahimtar cewa zama koma baya a fannin na nufin babban lahani ne ga kasa.

A ra’i, tsarin kula da makamai ko shirye-shiryen haɗin gwiwa masu sauƙi na iya taimakawa kowane bangare ta hanyar saita iyakoki waɗanda ke kauce wa gurɓata gogayya. A aikace, waɗannan tsare-tsare ba su da yawa.

Rashin nasarar haɗin kai, rashin yarda da juna, da harshen damo da Kirkirarriyar Basira ke da ita wajen amfani, sanya wa da wahala a cim-ma manufar da ake da ita irin ta kula da makamai da aka yi a baya.

Tare da iyakokin kasa, kasashen da ke da kayan aiki da cigaban fasaha ne za su iya sarrafa fannin. A matakin kasa da kasa kuma, abubuwan da ke tilasta wa a rungumi Kirkirarriyar Basira na saywa da wahala a iya samar da ka’idojin.

Mataki a kasashe

A cikin gida, gwamnatoci na riƙe da damarmaki. Majalisun dokoki na iya zartar da dokoki, mahukunta na iya fitar da ka’idoji , kuma hukumomi na iya buƙatar bin doka daga masu habaka fasaha da ke aiki a karkashin ikonsu.

Wannan fage ne da yanayin al'adu, dokoki da tattalin arziki ke iya tasiri a cikin harkokin gudanarwa. Kasa mai ƙarfi na iya samar da dokoki don kare sirri, hana son zuciya na algorithm, da kiyaye mahimman tsare-tsare ba tare da hana ƙirƙirar kayan fasaha ba.

Duk da haka babu daidaito wajen morar wannan iko.. Dokoki na nufin yadda kowa ya iya wasansa.

Ingantaccen sa ido na buƙatar kayan aikin fasaha manya na zamani, mahukunta da suka fahimci tsarin da ake aiki a kai, da cibiyoyi masu ƙarfi na iya daidaita ƙa'idodi yayin da fasahar ke sauya wa.

Ba tare da waɗannan ba, ƙa'idojin na zama kamar hoto kawai, ba masu tasiri ba.

Hanzari shi ne shinge na farko. Tsarin Kirkirarriyar Basira na iya canza wa sosai a cikin ‘yan watanni, yayin da yin doka kan dauki shekaru ana yi.

Dokokin da ke kulle na fuskantar hatsarin tsufa kafin a yi amfani da su. Ƙasashen da ke ci gaba da tafiya ne za su kasance waɗanda za su iya amfani da hanyoyin daidaitawa da samar vda dokokin da suka dace da kowane lokaci.

Kasashen da ke saka ka’idojojin amfani masu tsauri na iya fuskantar rashin nasara.

Matsala ta biyu ita ce ta ƙware wa. A ƙasashe da yawa, mahukunta, alkalai, da ma'aikatan gwamnati ba su da ilimin fasaha da ya kamata don tantance tsarin tare da duba hatsarin da ke tatare da bayanai da raunin tsarin.

Idan babu irin wadannan kwarewa, gwamnatoci za su samar da kudirin dokoki ne kawai, amma ba za su iya aiwatar da su ba.

Raunin ya fi tsananta a lokacin da Kirkirarriyar Basira ke aiki kan muhimman abubuwan more rayuwa, kiwon lafiya, ko tsarin juya kuɗi, inda gazawar sa ido na iya janyo sakamako mai tasiri nan da nan.

Without skilled reviewers, even the best-written AI law remains little more than words on paper.

The third constraint is dependence. States that rely on foreign-owned AI platforms, cloud services, or semiconductor supply chains cannot fully enforce their own standards. 

If a country’s critical AI systems are trained and hosted abroad, regulators lose the power to audit or modify them. This is not an abstract sovereignty question

Without independent capability, national regulators operate at the mercy of external suppliers. Europe’s experience with foreign cloud dominance offers a cautionary precedent.

Even for capable states, finding the right balance is difficult. Overly strict rules drive investment and talent elsewhere, as developers gravitate to jurisdictions where experimentation is easier. 

Overly lax rules erode privacy, enable misuse and weaken national security. Striking the right balance requires institutional strength, political will and continuous calibration. Some will manage it; many will not.

Ba tare da ƙwararrun masu bita ba, dokokin aiki da Kirkirarriyar Basira da aka rubuta sosai na kasnacewa ba wai rubutu a takarda kawai ba.

Matsala ta uku ita ce dogaro kan wasu. Gwamnatociin da suka dogara da manhajojin Kirkirarriyar Basira na kasashen waje, wajen ajiya na gajimare, ba za su iya kawo cikakken tsarinsu ba.

Idan aka samar tare da horar da tsarin Kirkirarriyar Basira na wata kasa a kasar waje, mahukunta ba su da damar bincikar sa ko suaya shi. Wannan ba tambaya mara amsa ba ce kan ‘yancin cin gashin kai.

Ba tare da cikakken ikon sarrafa wa da rashin dogaro kan wasu kasashe ba, mahukunta za su kasance a karkashin wasu daban da za su dinja juya su. Irin abinda Turai ta fuskanta game da mamayar ma’ajiyar bayanai ta gajimare ya ishi zama abin a lura sosai.

Har ma ga kasashen da suke da iko, samun cikakken daidaito na da wahala. tsauraran dokoki na korar zuba jari da basira zuwa wasu wuraren, inda masu habaka Kirkirarriyar Basira ke zabar inda ayyukansu suka fi sauki.

Raunanan dokoki na lalata tsarin bayanan sirri, bayar da damar yin amfani ta hanya marar kyau da raunata tsaron kasa. Samun cikakken daidaito na bukarar hukumomi masu karfi, niyya mai kyau ta ‘yan siyasa da ci gaba da ayyukan. Wasu za su iya yi, wasu kuma ba za su iya ba.

Shugabancin kasa da kasa

Hoton matakin kasa da kasa ya fi muni. Dalili na farko shi ne dabarar ayyuka. Kirkirarriyar Basira na yin alƙawarin samun nasara ta gaske a ayyukan soja, kuma babu wata kasa da ta san me take yi da za ta saurara.

A gwagwarmayar mallakar makamai, tsawatarwa na da guba irin ta siyasa. Tsoron fada wa cikin rashin nasara, da matsalar da hakan zai iya haifarwa, ya zarce fa'idojin da ake ganin za a iya samu.

Kudi ne ke tabbatar da batun. Kasuwancin Kirkirarriyar Basira ta ayyukan soja a duniya, wanda darajarsa ta kai kusan dala biliyan 10 a 2024, an yi hasashen zai iya habaka da kashi 13 kowace shekara.

A Amurka kadai, ana kiyasin kudadaden da ake kashe wa wajen ayyukan Kirkirarriyar Basira a fannin tsaro ya kai kusan dala biliyan biyu a shekara, inda mafi yawan kudaden ke tafiya ga tsarin samar da injina masu aiki da kansu da manhajojin da ake amfani da su wajen yanke hukunci.

Ko da gwamnatoci sun so su rage gogayyar, matsalar tantancewa za ta kasance wadda ba za a iya shawo kanta ba.

Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa yarjejeniyoyin makaman nukiliya suka yi aiki shi ne cewa makaman da yadda ake kai su na da yawa, ba za a iya boye su cikin sauki ba sannan na da saukin kirga su.

Samfuran Kirkirarriyar Basira ba haka suke ba. Ana iya horar da su a asirce, adana su akan kayan kwamfuta, saka su cikin manhajojin farar hula da iya kwafar su a duniya.

Tsarin sanya idanu kan ayyukan Kirkirarriyar Basira na bukatar matakin sanya ido na kutsa kai, wand amanyan kasashe ba za su aminta da shi ba. A wannan yanayi, akwai damar kin bayyana gaskiya.

Fasaha mai harshen damo wajen amfani, na ƙara fito da hoton. Haka ma tsarin hangen nesa na kwamfuta da aka yi amfani da shi don ɗaukar hoto na likita, za a iya amfani da shi wajen gano jiragen yaki marasa matuka; sannan tsarin harshen da ke rubuta wa kwastomomi bayanai na iya samar da farfaganda ko bayanan karya.

Matakin da tsarin kasa da kasa ke a kai ne ke tattare da matsalolin. Diflomasiyya tsakanin kasashe na ta fama da baturuwa marasa zafi irin su magance sauyin yanayi, sauye-sauye a Kungiyar Kasuwanci ta Duniya, da hana kisan kare dangi.

Yanayin odar kasa da kasa ya hada matsalar. Harkokin diflomasiyya na bangarori da yawa na kokawa ko da kan batutuwan da ba su da yawa kamar batun sauyin yanayi, sake fasalin WTO, da rigakafin kisan kare dangi.

Gaskiya a tsakanin manyan kasashe na raguwa sosai kuma ba ta da yawa. An dauki tsawon shekaru a Majalisar Dinkin Duniya ana tattauna batun ‘mutum-mutumi masu kisa’ ba tare da wareware matsalar ba, duk da yarjeniyoyin da kananan kasashe suka kulla.

Kasashen da suka fi karfin habaka Kirkirarriyar Basira irin su Amurka da China, na kallon hatsari sama da alfanu idan suka yi aiki da dokokin da abokan hamayyarsu ba lallai su yi aiki da su ba.

Sakamakon da ake iya samu shi ne rarrabuwar kawuna a duniya. Kasashe za su ne mallakar makamai masu amfani da Kirkirarriyar Basira da tsarin leƙen asiri ba tare da matakan tsaro da aka amince da su ba.

Rarraba dabaru

Don kalubalantar wannan matsala, abu mafi saukin aikata wa sh ne raba kafafuwa.. A cikin gida, ya kamata gwamnatoci susamar da tsarin horar da mahukunta, habaka kayan bincike da tantancewa, da samar da tsarin kawo kayayyaki da ke aiki da Kirkirarriyar Basira .

'Yanci wajen sarrafa na’ura mai kwakwalwa, haɓaka sabon tsari da kayan aikinadreshin yanar gizo na da mahimmanci ga kowane mai gudarwa da ya san me yake yi.

A duk faɗin duniya, ya kamata manufar ta zama tsukakkiya, yarjejeniyoyin da za a iya aiwatar da su a manyan bangarori masu hatsari irin su haramta aiki da Kirkirarriyar Basira a nukiliya da tsarin gudanarwa, haramta wani nau’i na makamai, ko neman bayar da bayani don al’amuran Kirkirarriyar Basira na shafar bangarori masu muhimmanci.

Irin waɗannan yarjejeniyoyin za su kasance masu iyaka, na da ƙarfi kuma masu rauni a wajen aiwatarwa, amma za su iya aƙalla jinkirta mafi yawan amfanin da ake yi da su.

Amma ya kamata masu tsara manufofin gwamnati su bude idanuwansu saboda gogayya da sauyin da ake samu za su zama a matsakin kasa da kasa.

Kirkirarriyar Basira za ta ci gaba da habaka cikin sauri, ta hanyar damar kasuwanci da matakan tsaro na ƙasa. Ka'idoji za su kasance a baya, kuma za a cike gibin ba ta hanyar yarjejeniyoyin bangarori da yawa ba sai ta hanyar neman fa'ida ta daidaikun kasashe.

Za a gudanar da zamanin Kirkirarriyar Basira ba da daidaito ba. A cikin gida, wasu ƴan kasashe masu ƙarfi za su haɓaka tsarin da ke daidaita ƙirƙira tare da aminci da ikon mulkin kai.

A duniya baki daya, gogayyar za ta ci gaba da shi ba tare da bin ka’idoji ba, tare da ‘yan yarjejeniyoyi lokaci-lokaci game da wurare mafiya hatsari.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us