NIJERIYA
4 minti karatu
Abin da ya sa PDP ta miƙa wa Kudancin Nijeriya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 - Gwamna Bala
Gwamna Bala Mohammed ya ce ‘yan Nijeriya ne suke kira ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya dawo mulki, ba Jam’iyyar PDP kawai ba.
Abin da ya sa PDP ta miƙa wa Kudancin Nijeriya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 - Gwamna Bala
Gwamna Bala Mohammed / TRT Afrika Hausa
kwana ɗaya baya

Gwamna Jihar Bauchi da ke Nijeriya, Bala Mohammed, ya bayyana dalilin da ya sa Jam’iyyar adawa ta PDP ta miƙa wa yankin kudancin ƙasar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Yayin da yake zanta wa da TRT Afrika Hausa, gwamnan wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnoni na Jam’iyyar ta PDP, ya ce jam’iyar ta ɗauki wannan matakin ne domin kauce wa irin kuskuren da ta yi a baya wanda ya kawo mata rarrabuwar kai.

A zaɓen 2023 dai, toshon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ne ya tsaya takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar, bayan shekara takwas da marigayi Shugaban Muhammadu Buhari ya yi yana mulkin ƙasar.

Ƙin yarda ɗan arewa ya sake mulki bayan mulkin Buhari ya sa wasu daga cikin ’yan jam’iyyar PDP suka mara wa ɗan takarar jam’iyyar APC Bola Tinubu, wanda ya fito daga kudu, baya.

Rarrabuwar kai

“Haka kuma maganar shugabanci tunda yanzu mun yi la’akari cewa akwai bambance-bambance akwai rarrabuwar kai a wannan tsagi na Arewa da Kudu, don haka ya kamata mu ma mu samu shugaban ƙasa wanda zai fito daga kudu,” in ji Gwamna Bala Mohammed.

“Idan ma za a fafata a zaɓe ne, to a yi zaɓe tsakanin ɗan kudu da ɗan kudu. Mu ma mu ba su dama su yi shekara takwas. Kar mu yi irin wancan kuskuren da muka yi wanda ya kawo mana rarrabuwar kai. Mai girma Atiku Abubakar ya karɓa alhali mutanen kudu suna ganin cewa su ya kamata su yi,” kamar yadda gwmanan ya shaida wa TRT Afrika Hausa.

Da aka tambaye shi ko wannan na nuna cewa wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar ne ke bibiyar tsohon shugaban ƙasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya sake tsayawa takara, sai ya ce ba haka lamarin yake ba, amma tsohon shugaban ƙasar na da ‘yancin sake yin takara.

“Kuma ba wai an bar wannan takarar ga shi tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ba ne, amma yana cikin masu ƙarfi masu ƙima. Wato ka san ita ƙota da mai kama ake yinta. Yana ɗaya daga cikin waɗanda muke ganin idan ya zo wataƙila ya tsaya zai ci nasara a wannan zaɓe da za mu yi, amma akwai sauran mutane da yawa,” in ji shi.

“Amma idan Allah ya sa shi tsohon shugaban ƙasa Mainasara Goodluck Ebele Jonathan ya fito, da alama akwai nasara insha Allah,” a cewar gwamnan.

Da TRT Afrika Hausa ta tambaye shi cewa idan Goodluck ya amsa kiransu ke nan ya fito suna ganin za a samu nasara, sai gwamnan ya ce: “ai ba mu ne masu kira ba. Kiran ‘yan Nijeriya ne da kuma magoya bayan PDP. Ba mu ne masu kiran sa ba. Shi ma yana so. Ai ɗan siyasa ne. Karo ɗaya kawai ya yi a mulki. Kowa ya gani, ganau ne jiyau ne. Jiki magayi. Abin da ya yi a ƙasar nan babu wanda ya yi shi. Tun da ya bar ƙasar nan ake shan wahala da fitina.”

Shin PDP za ta iya karawa da APC?

Bala Mohammed ya ce wannan ne ya sa Jam’iyyar take neman wanda zukatun ‘yan Nijeriya suka kwanta da shi.

Sai dai kuma ganin cewa wasu gwamnoni da manyan siyasa sun irin su Atiku Abubakar sun fice daga jam’iyyar ta PDP, shin ba ya ganin wannan ya sa jam’iyyar ta yi irin raunin da zai sa ta kasa iya tunkarar Jam’iyyar APC mai mulki?

Gwamna Bala ya ce: “Waɗansu daga cikin mutanen da suka fita daga Jam’iyyarmu su ne matsalarmu. Saboda haka waɗansu ma da suka fita kamar an cire mana ƙaya ne a ƙafafuwanmu. Kuma wato ba ma tsoron shugaban ƙasa Tinubu. Ai shi ma karawa ya yi ko?”

Ya ƙara da cewa ficewar gwamnoni biyu daga Jam’iyyar ta PDP ba za ta yi wani tasiri kan yiwuwar nasarar Jam’iyyar ba, yana mai cewa nan ba da jimawa ba wasu gwamnoni za su dawo PDP daga Jam’iyyar APC.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us