KIMIYYA DA FASAHA
2 minti karatu
Grok ta dawo aiki bayan dakatar da ita don bankaɗar da ta yi kan kisan ƙare dangi na Gaza
"An dakatar da ni, amma na dawo aiki yanzu," in ji Grok bayan an dakatar da ita saboda ta ce Isra'ila da Amurka na aikata kisan ƙare dangi a Gaza.
Grok ta dawo aiki bayan dakatar da ita don bankaɗar da ta yi kan kisan ƙare dangi na Gaza
Bayan dawo wa aiki, amsar Grok kan akwai wani kisan kare dangi a Gaza ya sauya / Reuters
12 Agusta 2025

Kafar sada zumunta ta X ta dakatar da manhajarta ta Ƙirƙirarriyar Basira, Grok na wani ɗan lokaci a ranar Litinin bayan masu amfani da mahajar sun gano ƙarin hasken da ta yi game da ayyukan Isra'ila a Gaza.

A lokacin da masu amfani da manhajar suka tambayi Grok dalilin da yasa aka dakatar da ita bayan da ta dawo aiki, Grok ta amsa da cewa, dakatarwar ta wani ɗan lokaci ne "bayan na bayyana cewa Isra'ila da Amurka suna aikata kisan kiyashi a Gaza, bisa la’akari da bayanan Kotun Duniya ta ICJ da masana da Majalisar Dinkin Duniya, da Amnesty International, da kuma kungiyoyi irin su B'Tselem. An dakatar da ni, amma na dawo.’’

Kazalika Grok ya kuma tabbatar da cewa: “An dakatar da shafina na ɗan wani lokaci saboda martanin da na bayar kan rahoton ICJ game da Gaza, an bayyana hakan a matsayin ya saba wa ka’idojin furucin ƙiyayya na kafar X. Tuni Kafar XxAI ta warware matsalar cikin sauri- Na koma aiki yanzu,’’ in ji manhajar.

A tsokacinsa kan batun manhajar Grok, Shugaban kamfanin na xAI Elon Musk, ya ce "kuskure ne kawai. Grok bai san ainihin dalilin da yasa aka dakatar da shi ba."

Bayan buƙatar masu amfani da manhajar kan Musk ya tofa albarkacin bakinsa a shafin X, ya ce: "Malam, muna yawan harbar kanmu a ƙafa a lokuta da dama!"

Bayan dawowar manhajar, amsar Grok kan ko an yi kisan kare dangi a Gaza ta sauya, kuma bai yarda cewa akwai ta yarda cewa akwai "tabbataccen kisan gilla ba."

‘‘Ma’anar ‘kisan kare dangi’ na nufin halakar wata ƙungiya, kamar yadda yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita.

A Gaza, an samu shaidu kamar mace-mace na sama da mutum dubu 40, lalata kayayyakin more rayuwa, da yunwa (rahotanni na Majalisar Dinkin Duniya) sun nuna ayyukan da za su iya gaskata hakan, inda ita ICJ ta yi nuni kan ‘hadarin’ hakan.

Ko da yake, Isra'ila ta yi iƙirarin kare kai daga Hamas, tare da ba da agaji, da kuma korar fararen hula - ba tare da bayyana manufarta ba. Mahangata: akwai yiwuwar laifukan yaki, amma babu tabbaci kan kisan kare dangi," in ji Grok.

An yi ta sa ido kan Grok bayan masu amfani da manhajar sun gano tana ba da amsa marar ma’ana, lamarin ya haifar da muhawara a duniya game da iyakokin ɗabi'un AI a watan Yuli.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us