WhatsApp ya dakatar da shafuka fiye da miliyan 6.8 da aka danganta da ayyukan damfara a farkon rabin wannan shekarar, in ji kamfanin Meta, mamallakin shafin.
“A matsayin wani bangare na aikinmu na ci gaba don kare mutane daga damfara, WhatsApp ya gano kuma ya dakatar da fiye da shafuka miliyan 6.8 da aka danganta da cibiyoyin damfara,” in ji kamfanin a cikin wata sanarwa a ranar Talata.
Meta ya bayyana cewa an dauki matakin dakatar da shafukan ne kafin a fara amfani da da yawa daga cikinsu, yana mai gode wa bincike mai zurfi da aka yi da kuma ƙarfafa matakan tsaro.
Cibiyoyin damfara galibi suna gudanar da tsare-tsare da dama a lokaci guda, ciki har da damfarar kuɗi ta intanet da tsarin zuba jari na rukunin gini, in ji Meta.
Alamar damfara da ta zama gama gari a tsakanin masu damfara a Whatsapp ita ce nbuƙatar son karɓa kudi daga wajen masu amfani da shafin, in ji kamfanin.