Abin da ya sa 'yan Nijeriya ke kashe makuɗan kuɗaɗe a kiran waya da sayen data
NIJERIYA
5 minti karatu
Abin da ya sa 'yan Nijeriya ke kashe makuɗan kuɗaɗe a kiran waya da sayen dataMasu amfani da layukan MTN da Airtel a Nijeriya sun kashe jimillar kuɗi naira tiriliyan biyu da biliyan 530, a kiran waya da sayen data, daga watan Janairu zuwa Yunin 2025.
/ Getty Images

Akwai wata sara da masu karakaina a shafukan sada zumunta suke yawan faɗa, mai cewa: “Duk runtsi ka da ka zauna ba data alaji”. Alamu na nuna wannan magana tana da tasiri a Nijeriya.

Wani rahoto da ya fito a ƙarshen makon da ya wuce ya nuna cewa masu amfani da layukan MTN da Airtel a Nijeriya sun kashe jimillar kuɗi naira tiriliyan biyu da biliyan 530, a kiran waya da sayen data, daga watan Janairu zuwa Yunin 2025.

Rahoton wanda kamfanonin biyu na Airtel da MTN suka fitar, ya ce wannan adadi ya nuna cewa an samu ƙarin kashi 50.9 cikin 100 na yawan kuɗin da ku masu kiran waya da sayen data kuka kasha, daga adadin wata shidan farko na bara, 2024, inda a wancan lokacin naira tiriliyan ɗaya da biliyan 680 kacal kuka kashe.

Bari mu yi nazari mu ga me ya jawo wannan ƙaruwar kashe kuɗaɗe a sayen data da kiran waya a Nijeriya, kuma me hakan ke nufi ga tattalin arzikin aljifanku da ma na ƙasa baki ɗaya?

Su dai kamfanonin Airtel da MTN sun ce an samu wannan ƙaruwa ne ta kashe kuɗaɗe a kan sadarwa saboda sauye-sauyen da suka yi kan cajin kuɗi da suke yi, da ƙaruwar amfani da manyan wayoyin komai-da-ruwanka, da kuma ƙarfafa zuba jari da su kamfanonin ke cigaba da yi a fadin Nijeriya.

Bayanin masana 

A tattaunawar da muka yi da Injiniya Yakubu Kasim Yakubu, wani ƙwararre da ya daɗe yana aiki a fannin sadarwa a Nijeriya, ya ce yayin da har yanzu a arewacin Nijeriya kuɗin da ake kashewa wajen kiran waya ya fi na data yawa, a kudancin kasar, an fi kashe kuɗi a sayen data fiye da kiran waya.

Sai dai Injiya Yakubu ya shaida wa TRT Afrika cewa, wannan ƙaruwar da aka samu ta kashe kuɗaɗe a fannin sadarwa na da alaƙa da wayewar da mutane ke ƙara yi duk rana a ƙasar, da kuma damarmakin amfani da waya da intanet, inda ya ba da misali da abubuwa uku kamar haka:

Na farko, akwai batun kasuwanci da cinikayya, inda a yanzu wahalhalun rayuwa kamar su tsadar kuɗin mota ya sa mutane suka zaɓi baje hajojinsu a shafukan sada zumunta, kuma ga alama ba ƙaramin ciniki suke yi ba.

Hakan ta sa dole masu saye da sayarwa suke rububin saka data don cin moriyar tafiya da zamani. 

Abu na biyu da Injinya Yakubu ya yi nuni da shi, shi ne tsananin son samun labarai a kafofin sadarwar intanet.

Wannan abu ya jawo gasa da gogayya mai tsanani tsakanin kafafen watsa labarai tsofaffi da masu tasowa, inda kowa ke son jan hankalin masu bibiya, yayin su masu bi da kallon shafukan suke kashe kuɗi wajen sayen data don jin ƙwaf.

Abu na uku a cewar masanin shi ne ƙaruwar content creators da influencers, da kuma azabar son tsegumi irin na masu amfani da shafukan sada zumunta.

Kusan duk sati ba a rasa wasu zafafan labarai da za su yi tarandin, ko dai waɗanda suka shafi addini ko siyasa ko Kannywood ko zamantakewa da dai sauransu.

Son kallo da raha

A irin wannan lokaci za ka ga kowa so yake ya ji me ake ciki a arewa ko duniya, ya zaku ya hau onlayin ya ga update, ya yi laikin, ko kwamen ko downloading, ko ma ya saki nasa update din tun da shi ba dan Facebook Lite ba ne.

Akwai kuma ‘yan ba ruwanmu, masu kallon abu su yi murmushi su wuce gaba. To ko su din ma ana zukar datarsu, balantana masu downloading da masu streaming series a YouTube.

 Masana harkokin sadarwa da ilimin aikin jarida na dijital sun ce akwai wani tsoro da masu amfani da intanet musamman shafukan sada zumunta suke da shi, wanda ake kira ‘Fear of Missing Out’, wato tsoron kar a yi babu ni. Irin wannan tsoro kan sa mutane su ji ko ta yaya sai sun sayi data sun ga irin wainar da ake toyawa.

 Idan aka duba batun tattalin arziki na mutane da ƙasa baki ɗaya kuwa, to wannan abu gagarumin cigaba ne da ke haɓaka kuɗaɗen shiga na al’umma da ƙasa.

Naira tiriliyan biyu da biliyan 530 din da ‘yan Nijeriya suka kashe a sayen data da kiran waya na kamfanoni biyu cikin wata shida kacal, yana nuni da irin gagarumar rawa da fannin sadarwa ke takawa a rayuwa da tattalin arzikin Nijeriya.

Injiniya Yakubu Kasim ya ce duk wani mai ruwa-da-tsaki a harkar sadarwa yana samun riba a cikinta. Wato ba a MTN da Airtel ɗumbin kudaden suke zama ba.

Ita ma gwamnati tana samun makuɗan kuɗaɗen shiga da kamfanonin nan ke biyanta a kan kowane cinikin sayen data da na kiran waya.

Tattalin arziƙi 

Idan aka zo batun tattalin arzikin ɗaiɗaikun mutane kuma, masu kasuwanci a intanet da content creators da influncers na daga gaba-gaba wajen samun maɗaukakiyar riba ta hanyar sayen data da suke yi suna wallafa bidiyoyi da hotuna da rubuce-rubuce da tallata hajojinsu, waɗanda mu kuma muke rububin sayen data don mu kalli abin da suka sa, ko da wanda ba zai amfane mu ba kai-tsaye.

Ga content creators da masu kasuwanci da influencers da kafafen watsa labarai, lamari ne na neman tara followers da ma samun riba daga abin da ake kira monetization, don haka duk yadda suka dama haka masu sayen data ke shanyewa.

Don haka a wannan gaɓar, ko dai ka yi ƙwazo ka gano yadda za ka ribaci wannan zamani na takanoloji ta yadda za ka saka data ka samu riba, ko kuma ka zama ci-zaune a harkar, sai dai wasu su saka content kai kuma jikinka na rawa ka sayi data ka kalla. Su da kamfanonun data da gwamnati da samun riba kai da kallo, kamar yadda Injiniya Yakubu ya faɗa.

Ina son duk wanda ya kalli bidiyon nan ya gaya mana, shin kana amfani da damar da zamani ya zo da ita ka samu riba a amfani da data ko kuwa sai dai kawai ka sayi a ci riba da kai?

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us