Shekaru tara da suka gabata, shugaban zartarwa na kamfanin Google Sundar Pichai a karon farko ya yi alkawarin cewa kirkirarriyar basira za ta sanya bayanai su zama “abin samu ga kowa”, ba tare da duba ga harshen mutum ba.
Ya ci gaba da maimaita wannan alkawari tun wancan lokacin, yana sanya zakuwa a duniya cewa fasahar zamani za ta kawar da shinge tsakanin yaruka tare da samar da dama iri guda wajen samun ilimi da bayanai ga kowa.
Amma ga wadanda ke magana da yarukan Afirka sama da 2,000, wannan alkawari ya nisanta daga gare su
Har yanzu miliyoyin mutane a nahiyar na samun manhajojin AI da ke inganta ayyukan noma, ilimi, da rayuwar yau da kallum da ba sa iya magana da yarukansu.
Bincike ya bayyana cewa ChatGPT - da ke da masu amfani miliyan 800 a mako guda a fadin duniya yana fahimtar jimloli 10 zuwa 20 ne kawai a harshen hausa, harshen da sama da mutum miliyan 94 ke magana da shi.
Lamarin haka yake ga sauran yarukan da ke da dimbin masu magana da su kamar Yaruba, Igbo, Swahili, da Somali, wadana dukkan su ba su da kyakkyawan wakilci a manhajojin AI duk da miliyoyin masu magana da yarukan.
To wai me ya sa ake manta wa ko yin biris da yarukan Afirka da dama a manhajoji ko tsarin Kirkirassiyar Basira na yau kuma me hakan yake nufi game da wa ke da mallakin makomar tsarin dijital?
Yaruka ‘marasa kayan aiki’
Ɗaya daga cikin manyan dalilan da ya sa ake ware harsunan Afirka daga AI shi ne abin da masu bincike ke kira "matsalar ƙarancin kayan aiki".
Game da wannan batu, “ƙarancin kayan aiki” na nufin ƙarancin bayanai a yanar gizo kamar su shafuka, litattafai, da rubutu a cikin wadannan yaruka.
Tunda yawancin tsarin harsuna (LLMs) sun dogara da ɗimbin bayanai irin su bayanan dijital don koyo da samar da matani, mafi yawan waɗannan bayanan na cikin Turancin Ingilishi (mafi yawa) ko a sauran harsunan duniya da ake magana da su a kasashen Yamma.
Hellina Hailu Nigatu, mai bincike ta NLP da ta mayar da hankali kan ƙananan harsuna a Jami'ar California, Berkeley, ta ce "Ma'auninmu na cigaba da tsari da manufofin bincike sun dogara ne akan abin da ke aiki da su ga harsunan Yammacin duniya."
Rashin bayanan horaswa ya bar nau'ikan AI kamar ChatGPT ko Gemini na gwagwarmaya don fahimta, samarwa ko kallo na ma'ana ga harsunan Afirka, komai yawan mutanen da magana da su.
"An kasafta harsunan Afirka a matsayin 'masu karancin kayan aiki' kuma yawanci ana cire su, ko ma idan an haɗa su, tsarin ba ya aiki da kyau a kansu," in ji ta TRT World.
“Wannan tsarin rarrabuwar ya kasa yarukan duniya zuwa "masu kayan aiki da yawa" da "masu matsalar kayan aiki" wanda hakan ne abinda fannin ya zaba yayin gudanar da ayyukan nasu,” in ji ta yayin tattauna wa da TRT World.
Tallafin masu zuba jari, nuna wariya da batun kashe kudade
Wani dalili na rashin samun wakilcin yarukan Afirka a fannin shi ne fifikon binciken cigaban AI a duniya.
Bincike ya nuna cewa sakamakon manyan harasa (LLM) ya dogara ne kan "Ra'ayoyin Yammacin duniya".
Kamfanonin fasaha na Yamma da cibiyoyin ilimi ne suka tsara galibin ƙa'idodin, waɗanda ke mayar da hankali kan harsunan da ke da mafi yawan bayanai a yanar gizo da kuma mafi yawan kashe kudade ga ‘yan yaruka ‘masu kayan aiki da yawa’.
Sakamakon haka, harsunan Afirka ba kasafai ake ba su fifiko don saka hannun jari ko ƙirƙirar sabon abu game da su ba.
Har ila yau, ƙarfafa kasuwanci na taka muhimmiyar rawa. Tunda dai nan da nan ba a samun dawowar kudin da aka zuba jari kan yarukan Afirka, sai ya zama kamfanoni ba su da karfin gwiwa sosai don sadaukar da lokaci da kayan aiki su inganta taimakon AI ga wadannan harsuna.
Kunshin bayanan da ake amfani da su wajen horar da tsarin Kirkirarriyar Basira ya sake karfafa wannan son kai da nuna wariya.
Ko da an shigar da harsunan Afirka, a mafi yawancin lokaci tsarin na ɗaukar zato da salon al'adun Yammacin Duniya, wani lokaci suna bayar da bayani a jirkice ko kokarin dabbaka ra’ayoyinsu.
Abubuwan da aka samo a binciken sun yi daidai da bincike mai zurfi game da son zuciya na algorithmic.
"Abin da muke gani a bincike shi ne ana samun amincewa da tsarin manyan yaruka kan yaruka da dama ba tare da yin la'akari da haɗarin shigo da son zuciya daga Turancin Ingilishi zuwa waɗannan yanayi na yaruka da dama, ko sakin lafiya daga tunanin nuna son zuciyar Ingilishi kan abubuwan da babu su,” in ji Nigatu.
Kazalika, akwai ƙalubalen fasaha a cikin yadda AI ke sarrafa rubutu, wanda ke sanya yawancin harsunan Afirka cikin ƙarin yin asara.
Bincike ya gano cewa yin amfani da rubutun da ba na Latin ba a cikin shahararrun kayan aikin AI, haƙiƙa na tsada fiye da amfani da Turancin Ingilishi ko na Faransanci.
Wannan na faruwa ne saboda manhaja na rarraba jimloli zuwa ƙananan sassa da ake kira "tokens" a Turance, kuma tana buƙatar ƙarin alamu don rubuta irin wannan jimla a cikin harsunan da ba sa amfani da haruffan Latin.
Wannan yana nufin masu amfani waɗanda ba za su iya biyan kuɗi kaɗan ba suna ƙara biyan kuɗi don aiwatar da adadin rubutu iri ɗaya, kuma galibi suna samun sakamako marasa inganci.
Nigatu ta jaddada cewa wadannan kalubale na nuna akwai rashin daidaito a tsakanin wadanda ke tsara wadannan abubuwa tun da farko.
Kamar yadda ta nuna, yana da mahimmanci cewa shin “wane ne ke yin binciken, wato ta yaya masu magana da waɗannan harsunan ke da hannu cikin abin da ake yi don harshensu.”
Yunkurin Afirka na inganta tsarin dijital
Dangane da wannan dan waken zagayen da ake yi w ayarukan Afirka a harka AI, wani shiri mai ban sha'awa na gudana don samarwa da harsunan Afirka wajen zama harkokin Kirkirarriyar Basira.
Shirin ‘African Next Voices’, wanda ya samu tallafin dala miliyan 2.2 daga gidauniyar Gates, ya kasance shirin samar da bayanai na AI mafi girma ga harsunan Afirka da aka samar ya zuwa yau.
Maimakon jiran zuwan Silicon Valley, masu bincike a fadin nahiyar sun dauki al'amura a hannunsu.
Kwararrun harshe sun riga sun nadi kalamai na awanni 9,000 a cikin harsuna 18 a Najeriya, Kenya, da Afirka ta Kudu, suna mayar da waɗannan maganganu zuwa madaidaitan bayanan dijital waɗanda masu haɓaka AI za su iya shigar da su cikin tsarin harshe.
Kashi na farko na wadannan bayanan, wanda aka fitar a wannan watan, ya nuna wani lokaci mai muhimmanci wajen dimokuradiyyantar da cigaban Kirkirarriyar Basira (AI).
Ife Adebara, babban jami'in fasaha a wata kungiya mai zaman kanta ta Data Science Nigeria, wacce ke jagorantar reshen Najeriya na wannan aikin, ya ce "Abin farin ciki ne sosai ganin irin cigaban da wannan zai kawo ga wadannan harsuna kebantattu, da kuma yadda hakan zai taimaka wa daukacin al'ummar da ke aiki a fannin fasahar harshe don Afirka."
Tawagar masu wannan aiki na mayar da hankali kan yarukan da suka hada da Hausa, Yarbanci, Igbo, da Naija, wadanda daruruwan miliyoyin mutane ke magana da su duk da haka kusan ba sa kan tsarin AI na yau da kullum.
Tsarin da Next Voices ke bi ya bayyana wani tsari na daban ga tattara bayanan harshe. Maimakon a goge ko watsi da bayanan dijital da ake da su kamar yadda kamfanonin Yammacin duniya ke yi, masu bincike na mu’amala kai tsaye da al’ummu daban-daban.
Lilian Wanzare, ƙwararriyar ilimin harshe a jami'ar Maseno da ke Kenya wadda ke jagorantar ayyukan Kenya, ta bayyana yadda ƙungiyarta ke nuna hotuna da ɗaiɗaikun mutane tare da tambayarsu su bayyana abin da suke gani a yarukansu na asali, da suka haɗa da Dholuo, Kikuyu, Kalenjins, Maasai, da Somali.
Wannan tsari nasu na fifita amfani da ingantacciyar hanyar tattara bayanai, amfani da yaren yau da kullum mai makon amfani da bayanai da aka rubuta aka ajje.
Wanzare ta ce "Akwai babban yunƙuri zuwa ga kunshin bayanai da aka mayar na gida, saboda tasirin ya fi aiki a kan mutane idan ya zama ya shafi bigiren da suke ko kayayyakinsu.”
A Afirka ta Kudu, Vukosi Marivate, masanin kimiyyar kwamfuta a Jami'ar Pretoria, yana jagorantar ƙoƙarin tattara bayanai na harsuna bakwai - ciki har da Setswana, isiZulu, isiXhosa, Sesotho, Sepedi, isiNdebele, da Tshivenda.
Tawagarsa tana aiki tare da rukunin ƙungiyoyi don ƙirƙirar tsarin yaren Kirkirarriyar Basira (AI) waɗanda kasuwancin fasaha za su iya habaka su daga baya.
Bayan nasarorin fasaha, shirin African Voice na bayyana samun sauyin falsafa kan yadda ya kamata cigaban AI ya kasance.
Yayin da yawancin kamfanonin fasaha ke ɗaukar harsunan Afirka a matsayin tunanin da za a magance kawai bayan an cika kasuwanni masu ribar gaske, wannan yunƙurin ya sanya su a matsayin batutuwa na farko da suka cancanci a sadaukar musu da kayan aiki da ƙwarewa.
By taking the initiative themselves, these communities are showing that the future of artificial intelligence can be shaped on their own terms, rather than waiting for Silicon Valley to decide who gets a voice.
Za a raba takaddun tsarin aikin tare da bayanai, wadanda za su baiwa masu bincike damar yin irin wannan aikin ga wasu harsunan da aka mayar saniyar ware a duniya.
Kungiyoyi kamar Masakhane sun riga sun gina hanyoyin sadarwa masu ƙarfi da ke mayar da hankali kan sarrafa harshe na asali, suna nuna abin da zai yiwu lokacin da ƴan Afirka suka haɓaka harsunan Afirka, ga 'yan Afirka.
Ta hanyar daukar matakin da kansu, waɗannan al'ummomin suna nuna cewa za a iya tabbatar da makomar Kirkirarriyar Basira kan tsarin da suka samar, maimakon jiran Silicon Valley su bayyana waye zai zama mai bakin magana.