NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun ce sun kashe ‘yan ISWAP da dama a Borno
Cikin ‘yan makonnin nan dai an yi ta samun rahotannin hare-haren da ‘yan ta’adda ke kai wa sansanonin sojoji a yankin.
Sojojin Nijeriya sun ce sun kashe ‘yan ISWAP da dama a Borno
Boko Haram, wadda ke kai hare-hare a Nijeriya tun daga shekarar 2009, ta yi sanadin mutuwar dubban mutane da raba miliyoyi da muhallansu. / Nigerian army
9 Yuni 2025

Rundunar Sojojin Nijeriya ta ce ta kashe ‘yan ta’adda da dama a cikin wasu jerin hare-haren sama da na ƙasa da suka kai sansanonin ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP da ke Nzalgana, a ƙaramar hukumar Gujba da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Nijeriya.

Wata sanarwar da rundunar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ta ce hare-haren da sojojin suka ƙaddamar da sanyin safiyar Litinin 9 ga watan Yuni sun yi sanadin mutuwar wani babban kwamandan Boko Haram a ƙauyukan Ngorgore da Malumti, Ameer Malam Jidda.

Duk da cewa sanarwar ta sojoji  ba ta yi ƙarin bayani game da jerin hare-haren ba, Zagazaola Makama, wani bai ba rahoto game da laumaran tsaron a yankin, ya ruwaito cewa sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar  AK47 da harsasai da kuma babur daga hannun kwamandan da aka kashe.

Sai dai kuma sanarwar ta sojojin ta bayyana cewa sojojin sun sake samun ƙarin makamai da gawarwakin ‘yan ta’adda a Abadam bayan arangamar da suka yi da ‘yan ta’addan kwanan nan a Mallam Fatori.

Cikin ‘yan makonnin nan dai an yi ta samun rahotannin hare-haren da ‘yan ta’adda ke kai wa sansanonin sojoji a yankin.

Kazalika sojojin ƙasar su ma suna kai hare-hare ta sama kan sansanonin ‘yan ta’addan a yankin domin su hana su iya kai irin hare-haren da suke kai wa kan sojoji.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us