KASUWANCI
2 minti karatu
Farashin ƙwallon kaɗanya ya faɗi warwas a Nijeriya bayan ƙasar ta dakatar da fitar da shi
Farashin ya ragu zuwa Naira 800,000 ($521) kan kowane ton a ranar Alhamis, wanda ya yi ƙasa da kashi 33 cikin ɗari daga farashin da aka sayar kwanaki kaɗan da suka gabata.
Farashin ƙwallon kaɗanya ya faɗi warwas a Nijeriya bayan ƙasar ta dakatar da fitar da shi
Burkina Faso, Ghana, Mali, Ivory Coast da Togo na daga cikin ƙasashen da suka taƙaita fitar da ƙwallonm kaɗanya / Getty Images
15 awanni baya

Farashin ƙwallon kaɗanya, wanda ake amfani da shi a kayan kwalliya da kuma kayan zaƙi, ya fadi a Nijeriya bayan gwamnatin ƙasar ta shiga sahun sauran ƙasashen Yammacin Afirka wajen hana fitar da shi ƙasashen waje.

A cewar Rildwan Bello, Shugaban kamfanin Vestance da ke Legas, wanda ke bibiyar farashin kayayyakin gona ya ce farashin ya ragu zuwa Naira 800,000 ($521) kan kowane ton a ranar Alhamis, wanda ya yi ƙasa da kashi 33 cikin ɗari daga farashin da aka sayar kwanaki kaɗan da suka gabata.

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa an sanya haramcin watanni shida ne domin “tabbatar da isasshen kaya ga masu sarrafa shi a cikin gida da samar da ayyukan yi, da kuma kare harkar da mata ne suka fi rinjaye wajen tattara shi da kashi 95 cikin 100.”

Sai dai Bello ya ce, duk da cewa manufar gwamnatin ƙasar mai kyau ce, hakan zai haifar da matsalolin kuɗi ga manyan ‘yan kasuwa da ke fitar da shi, waɗanda yanzu za su iya samun matsala musamman ga waɗanda suka samu kwangilar fitar da shi.
“Fitar da shi waje ce ke sa kasuwar ta yi armashi. Abin da ake buƙata a cikin gida bai kai kai adadin wanda ake samu ba,” in ji shi.

“Kirkirar masana’antu ba abu bane da ake yi a cikin dare ɗaya. Ba za ka iya kafa masana’antar sarrafawa cikin wata biyu kawai ba.

Itatuwan da ke bada ƙwallon kaɗanya suna girma a hankali kuma asalinsu daga Afirka ta Yamma ne. Nijeriya na samar da ton 500,000 a duk shekara, in ji bayanan gwamnati. Sauran manyan masu samarwa sun hada da Burkina Faso, Ghana, Mali, Ivory Coast da Togo, waɗanda duka suka taƙaita fitar da shi domin ƙarfafa sarrafa cikin gida.

Tun bayan hawan Tinubu a watan Mayun 2023, shugaban na ta ƙoƙarin fara samar da ayyukan yi ta hanyar taƙaita sayar da albarkatu zuwa ƙasashen waje. Ya ce, wannan haramcin zai taimaka wajen daidaita matsalar da Nijeriya ke da ita inda take samar da kusan kashi 40 na kwallon kaɗanya, amma tana da kashi kasa da 1% na kasuwar duniya mai darajar dala biliyan 6.5.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us