Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, Muhammad Sani Bello ya ce ba wanda aka kama zuwa yanzu dangane da harin da aka kai wa ayarin motocin tsohon Ministan Shari’a na Nijeriya, Abubakar Malami.
CP Bello ya shaida wa manema labarai bayan wani taron tsaro da gwamnan jihar ya yi, cewa lamarin da ya faru a kewayen unguwar GRA, yana da alaƙa da wasu ‘yan daba ne masu alaƙa da wata ƙungiyar siyasa.
Kwamishinan ya ƙara da cewa, wasu ‘yan siyasa ma suna karya dokar hana amfani da jiniya da kuma yin yaƙin neman zaɓe ba tare da izini ba.
Ya bayyana cewa an samar da matakan tsaro domin tabbatar da bin doka da oda, yayin da ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su kwantar da hankalinsu.
Ya jaddada cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kuma duk wanda aka samu da laifi za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban ƙuliya.
A ranar Litinin ne wasu da ake zargin ‘yan daba ne suka kai wa ayarin motocin Malami hari, a daidai lokacin da rahotanni ke cewa mutane da dama sun koma jam’iyyar haɗaka ta ADC da tsohon Ministan Shari’ar ke daga cikin manyan jagororinta.
Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan da Malami ya shiga Kebbin don yin wata ta’aziyya.
Ganau sun ce an lalata motoci kusan 10 na ayarin Malamin, sannan an jikkata wasu magoya bayansa da dama.
Malami, wanda ya riƙe muƙamin Ministan Shari’ar Nijeriya daga shekarar 2015 zuwa 2023, ys shaida wa ‘yan jarida cewa harin na adawar siyasa ne.