SIYASA
6 minti karatu
Ko Ƙasashen Yammacin Duniya sun yi gaggawa wajen rufe kofar tattaunawar nukiliyar Iran?
Tare da dawo da takunkumai cikin gaggawa, kasashen E3 sun tura Iran zuwa bango. SHin za su iya samun matsaya kafin wa’adin kwanaki 31 ya kare?
Ko Ƙasashen Yammacin Duniya sun yi gaggawa wajen rufe kofar tattaunawar nukiliyar Iran?
Za a iya dawo da takunkumai idan Iran ta gaza dawo tattaunawa da IAEA. / Reuters
11 awanni baya

Daga Sabena Siddiqui

A wani muhimmin lokaci a harkokin diflomasiyya na duniya, Faransa, Birtaniya da Jamus a wannan makon sun dakatar da tattaunawa mai muhimmanci da Iran a Geneva ba tare da cim ma matsaya ba.

Kasashen da aka sani da lakabin E3, dukkan su ukun sun koma yin kira ga kakaba takunkuman Majalisar Ɗinkin Duniya a kan Iran don tilastawa kasar da ke al’umma mafiya yawa ‘yan Shi’a ta yi cikakken aiki da shirin sanya idanun hukumar IAEA kan cibiyoyinta na nukiliya.

A wata wasika, Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya sanar da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya game da "rashin bin ka'ida" na Iran a karkashin JCPOA, da kuma cewa suna daukar matakan da za su tabbatar da aikin nukiliyar Iran bai ci gaba ba.

Sai dai ya ce kofar kasashen Turan uku a bude suke don tattaunawa a cikin kwanaki 30 kafin takunkumin ya fara aiki.

Har zuwa ranar 18 ga Oktoba na cikar wa’adin yarjejeniyar da aka cim ma, ana sa rai da fatan Iran ta amince da bayar da damar gudanar da cikakken binciken hukumar ta IAEA da kuma shiga tattaunawa da Amurka.

Amma bayan wata guda, za a maido da takunkumin da ya shafi bangarorin harkokin kudi, banki, tsaro makamashi na Iran.

Me kasashen E3 suka cim ma?

Ko da yake Moscow da China suna adawa da wannan matakin kuma Iran ta yi barazanar "za a ga mai zai biyo baya", mutum na mamakin ko E3 sun yi amfani da wannan taron ne kawai saboda sashen yarjejeniyar da ake kira 'sunset clause' - kamar yadda kuma aka kira tsarin ‘snapback’ - dã ya ruguje.

A takaice dai tattaunawar ta wargaje ne kawai kafin a cim ma wata nasara ko kuma a tattauna matakan karfafa gwiwa.

Kodayake E3 sun yi amfani da dabaru a matsayin damarsu ta ƙarshe don yin aiki, Turai na iya zama a wadda ba ta cikin wannan batu gaba daya bayan wannan mataki. Kuskuren matsin lamba ba dabara ba ce, E3 sun yi dauki matakin shiga tattaunawa kafin bin hanyoyin diflomasiyya.

Kuma akwai hatsarin cewa wannan matakin zai zama kaikayi koma kan mashekiya.

Idan manufar E3 ita ce mayar da Iran kan teburin tattaunawa, tuni Tehran ta yi Allah wadai da matakin a matsayin "mara tushe" kuma "ba bisa ka'ida ba" tare da gargadin dakatar da hadin gwiwa da IAEA. Maimakon samun mika wuya daga Iran, E3 na iya tunzura kasar gaba.

Wadannan tattaunawa da E3 sun zama dama mai kyau don daidaita batun ta hanyar diflomasiyya, amma ga dukkan alamu damar sake farfado da Shirin Haɗin Gwiwa na (JCPOA) ya ruguje.

Bayan wani lokaci, an zargi Iran da karya yarjejeniyar nukiliya ta hanyar habaka sinadarin Uranium da kashi 60 cikin dari, matakai kadan ga kashi 90 cikin 100 da ake bukata don samar da makamin nukiliya. Ana zargin Iran na da isassun kayan da za a iya samar da bama-bamai shida.

Da take neman a cire takunkumin baki daya, Iran ba ta son tattaunawa da Amurka kan lamarin, don haka E3 sun tuntube ta a matsayin masu sanya hannu kan yarjejeniyar JCPOA da kuma yin tattaunawa da dama kamar yadda suka yi.

Amma rashin haƙuri, ba zato ba tsammani Amurka da Isra'ila suka matsa lamba don ganin sun lalata cibiyoyin nukiliyar Iran a watan Yuli, wanda ya kai ga fafata yaƙin kwanaki 12 tsakanin Tehran da Tel Aviv.

A wannan makon, masu bincike kan makaman nukiliya sun koma Iran a karon farko tun bayan harin da Amurka da Isra'ila suka kai, amma Iran ta ce komawar masu sanya idanun na IAEA ba yana nufin dawo da cikakken hadin gwiwa da su ba.

Ko takunkuman na da tasiri?

A zahiri, barazanar takunkumi na iya zama mai ƙarfi da tasiri a bayyane, kuma mai karfin gaske a kwanakin farko na yarjejeniyar JCPOA, amma ba lallai ta zama mai amfani ba a yau.

A nazarin manufofinsu na  2022 na Cibiyar Washington, Henry Rome, babban mai bincike da Louis Dugit-Gros, malami mai ziyara, sun rubuta cewa takunkumin tattalin arziƙi a ƙarƙashin tsarin na iya zama mai tazara idan aka kwatanta da takunkuman da Amurka ta kakaba mata, kuma ƙila sun zama "madannan tsaiwar gaggawa" ta diflomasiya kawai maimakon ingantaccen tasiri don yin tataunawa.

Kuma ko da yake ba za ta iya dakatar da Iran ba, za a dauki tsarin dawo da takunkuman a matsayin "tabbatacciyar alamar cewa tattaunawar ta ruguje".

Bayan haka, ba za a iya komawa ga JCPOA ba, kuma duk sasantawa da ayyukan da aka yi don cim ma yarjejeniyar nukiliyar sun tafi a tutar babu, da kuma kokarin da aka yi na farfado da ita a 'yan shekarun da suka gabata.

Wannan yanke shawara na gaggawa na iya haifar da mafi munin rikici a alakar Iran da kasashen Yamma. Tayar da batun ba tare da wata madaidaicin hanyar diflomasiyya ba na iya dagula lamarin, kuma ba tare da tabbatar da bin ka'idojin IAEA daga bangaren Iran ba.

Bayan haka, masu tsattsauran ra'ayi a gwamnatin Tehran na iya amfani da sabunta takunkumin a matsayin uzuri don tabbatar da ci gaban nukiliyar da ba a iya sanya idanu a kan ta ba.

Har ila yau, Iran za ta iya mayar da martani ta hanyar ficewa daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT).

A cewar Kungiyar Magance Rikicin Kasa da Kasa, Tehran na iya zabar hanyar kawo karshen yarjejeniyar 1974 da IAEA wacce ke tantance ma'auni na sa ido kan makaman nukiliya.

Kuma a karshe, mai yiwuwa Tehran ta kara dogaro da wasu abokan hulda kamar Rasha da China, tare da ci gaba da karkata kasuwancinta daga tsarin biyan kudi na kasashen yamma don mayar da takunkumin ya zama marar amfani.

Ta hanyar kusantar Moscow da Beijing, Iran za ta sami karin kuzari don karfafa alakar makamashi, tsaro da tattalin arziki, tare da rage karfin ikon Turai da ma sama da haka.

A ci gaba da aiki don toshe damar dawo da takunkuman na gaggawa, Moscow da China sun yi ta yada wani daftarin kuduri tsakanin mambobi 15 na Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya don tsawaita yarjejeniyar har zuwa 18 ga Afrilun 2026.

A kokarin su na samar da karin lokaci ga Tehran, sun yi yunkurin warware takunkumin ta hanyar yin kira da a dakatar da 'duk wani mataki da za a dauka'.

Amma ba za a iya yin watsi da tsarin da za a yi amfani da shi ba da zarar an tabo shi, kuma takunkumin da ke kunshe cikin kudurori shida na Majalisar Dinkin Duniya da aka dakatar zai fara aiki a ranar 18 ga Oktoba, kuma yarjejeniyar JCPOA ta 2015 za ta kawo karshe.

Ta hanyar matsa lamba sosai, Turai na iya sauko da abin da ya rage na tsarin raunin JCPOA. Samun Rasha da China a tafiyar na iya zama dabarar da ta fi dace wa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us