Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya yi maraba da hukuncin da wata kotu a kasar Finland ta yanke wa mai fafutukar kafa kasar Biafra, Simon Ekpa, inda ya ce masu daukar nauyin ta'addanci za su fuskanci hukunci, ba tare da la'akari da inda suke ba.
Kotun gundumar Päijät-Häme da ke birnin Lahti na kasar Finland ta yanke wa Ekpa hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa samun sa da laifin ta’addanci.
Kotun ta samu Ekpa da laifin shiga ayyukan ta’addanci.
A cewar mai gabatar da ƙara, laifukan sun shafi ayyukansa na sake kafa kasa mai cin gashin kanta a yankin Biafara na Nijeriya.
Jim kadan bayan yanke hukuncin, Janar Musa ya bayyana hukuncin a matsayin wata gagarumar nasara a yakin da duniya ke yi da ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.
An bayyana hakan a wata sanarwa da Daraktan yada labarai na rundunar, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar.
A cewar sanarwar, Musa ya ce hukuncin ya tabbatar da cewa babu wani mutum ko kungiyar da ke daukar nauyin ta’addanci a Najeriya da za ta samu mafaka a wani yanki na duniya.
“Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Janar Christopher Gwabin Musa ya bayyana goyon bayansa ga hukuncin da kotun gundumar Päijät-Häme ta kasar Finland ta yanke a yau, inda ta yanke wa Simon Ekpa hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa samun sa da laifin ta’addanci,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa “Janar Musa ya bayyana hukuncin a matsayin wata gagarumar nasara a kokarin da duniya ke yi na yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi, yana mai bayanin cewa hukuncin ya karfafa ka’idar cewa wadanda ke tayar da tarzoma da kuma bayar da kudade don daukar nauyin ta’addanci za su fuskanci hukunci a duk inda suke a fadin duniya.”
Ya yaba wa jami’an tsaron Nijeriya, tare da jami’an diflomasiyyar kasar, saboda bayar da hujjojin da suka taimaka wajen yanke hukuncin.
A ra’ayin Janar Musa, sakamakon ya nuna karfin ikon haɗin gwiwar kasa da kasa wajen fuskantar barazana da ke zuwa daga ketare.
Babban Hafsan Hafsoshin Sojin na Nijeriya ya kuma jaddada shirin rundunar sojin kasar na ci gaba da yin aiki tare da kawayensu na duniya domin wargaza kungiyoyin ‘yan ta’adda tare da yin kira ga ‘yan Nijeriya da su yi taka-tsan-tsan tare da tallafa wa ayyukan tsaro da ake ci gaba da yi na yaki da masu tayar da kayar baya da ‘yan -aware.