Shin ƙirƙiro gundumomin ci-gaban yankuna zai kawo ci gaba a Nijeriya?
NIJERIYA
3 minti karatu
Shin ƙirƙiro gundumomin ci-gaban yankuna zai kawo ci gaba a Nijeriya?Gwamnoni suna ƙirƙiro gundumomin ci gaba ne saboda yana da matukar wahala a halin yanzu a ƙirƙiro sabbin kananan hukumomi saboda sai an gyara kundin tsarin mulkin Nijeriya wanda hakan jan aiki ne.
Gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya sanar da ƙirƙiro wasu gundumomin ci gaba (LCAs) a ƙarshen watan jiya. / Others
17 awanni baya

Wannan na daga cikin muhawarorin da ake tafkawa a Nijeriya tun bayan da Gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya sanar da ƙirƙiro wasu gundumomin ci-gaba da ake kira Local Council Development Areas (LCAs) a ƙarshen watan jiya.

Gwamnan ya sanya hannu kan dokar da majalisar dokokin jihar ta yi wacce ta ƙirƙiro gundumomin ci-gaba guda 13 a kan ƙananan hukumomi 11 da dama can jihar take da su.

Yanzu jihar tana da jimillar ƙananan hukumomi da gumdumomin ci-gaba guda 24 ke nan.

Bayan sanya hannu a kan dokar, gwamnan ya ce ƙirƙiro gundumomin ci-gaban zai sauya yadda ake tafiyar da gwamnati a jihar. Ya ce yanzu gwamnati ta ƙara zuwa kusa da jama’a, inda za ta fi jin koke-koke da bukatunsu.

Sannan gwamnan ya ce sabbin gundumomin za su kawo ci-gaba ga al’ummomi daban-daban da kuma Jihar Gombe baki daya.

Da ma can akwai wasu jihohi a fadin kasar da suka ƙirƙiro gundumomin ci-gaba da niyyar kai gwamnati kusa ga jama’a.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ne ya fara ƙirƙiro gundumomin ci-gaba lokacin da yake gwamnan Jihar Legas tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, inda hakan ya jawo taƙaddama mai zafi tsakaninsa da Shugaban Kasa na lokacin wato Olusegun Obasanjo, wanda sakamakon hakan ya riƙe kudin kananan hukumomi da gwamnatin tarayya take aika wa Jihar Legas a lokacin.

Bayan wani hukunci na Kotun Ƙolin Nijeriya da ya amince da gundumomin ci-gaba da Tinubun ya ƙirƙiro a Legas ne ya sa jihohi kamar Osun da Ekiti da Ondo da Adamawa da Nasarawa da kuma Taraba duk sun bi sahun Legas ɗin wajen ƙirƙiro gundumomin ci-gaba daga bisani.

Gwamnoni suna ƙirƙiro gundumomin ci-gaba ne saboda yana da matukar wahala a halin yanzu a ƙirƙiro sabbin kananan hukumomi saboda sai an gyara kundin tsarin mulkin Nijeriya wanda hakan jan aiki ne.

Yayin da wasu suke yaba wa jihohin da suka yi wannan sabon tsari, wasu suna ganin za a iya fuskantar kalubale wajen neman hanyar da za a samo kuɗaɗen gudanar da wadannan sabbin gundumomin ci-gaba da aka ƙirƙiro musamman a jihohin da ke yankin arewacin kasar, tun da galibin jihohin suna dogara ne kan kudin da gwamnatin tarayya take aika musu a kowane wata.

Hakan na faruwa ne a dadai lokacin da Kotun Kolin Nijeriya ta umarce a riƙa bai wa wa kananan hukumomi kudadensu kai-tsaye, ko da yake har yanzu galibin jihohin kasar ba su fara yin hakan ba.

A baya jihohin da suka ƙirƙiro sabbin gundumomin suna samun kuɗaɗen gudanar da su ne daga asusun haɗaka na ƙananan hukumomi na jiha, sai dai yanzu da kotu ta umarci gwamnatin tarayya ta rika biyan kananan hukumomi 774 da ake da su a kasar kuɗaɗensu kai-tsaye.

Wasu suna ganin wannan zai haifar da kalubale ta fuskar kuɗaɗen gudanarwa daga wadannan sabbin gundumomi da aka ƙirƙiro a Gombe da wasu jihohin kasar.

Hakan zai iya zama ƙalubale ne saboda kundin tsarin mulkin kasar ƙananan hukumomi 774 kawai ya san da zamansu, kuma bai san da zaman sabbin gundumomin ci-gaba da aka ƙirƙiro ba.

Masana suna ganin ya zama wajibi ga gwamnonin da suka ƙirƙiro gundumomin ci-gaba da su mayar da hankali wajen ƙirƙiro sabbin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da za a riƙa amfani da su wajen gudanar da su, maimakon ci-gaba da dogara kacokan kan kason kuɗaɗen da ake samu daga gwamnatin tarayya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us