SIYASA
2 minti karatu
Gertrude Torkornoo: Shugaba Mahama ya kori Alƙaliyar Alƙalan Ghana daga aiki
Shugaban ya sauke alƙaliyar ne bayan an same ta da laifin yin amfani da matsayinta wajen aikata ba daidai ba.
Gertrude Torkornoo: Shugaba Mahama ya kori Alƙaliyar Alƙalan Ghana daga aiki
A shekarar 2023 ne Gertrude Torkornoo ta sha rantsuwar kama aiki a matsayar alƙaliyar alƙalan ƙasar / Ghana News Agency
12 awanni baya

Shugaban Ghana John Mahama ya sauke alƙaliyar alƙalan ƙasar Gertrude Araba Esaaba Sackey Torkornoo, daga muƙaminta nan-take.

Shugaban ya sauke alƙaliyar ne bayan an same ta da laifin yin amfani da matsayinta wajen aikata ba daidai ba.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewa Shugaba Mahama ya ɗauki matakin ne bayan ya dogara kan sashe na 146(9) na kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1992.

Wannan ya biyo bayan samun sakamakon binciken kwamitin da aka kafa a ƙarƙashin sashe na 146 (6) na kundin tsarin mulkin ƙasar domin bincike kan ƙorafin da wani ɗan ƙasar ta Ghana mai suna Mista Daniel Ofori ya shigar a kan alƙaliyar alƙalan.

Wata sanarwa da Mista Felix Kwakye Ofosu, mai magana da yawun shugaban ƙasar kuma ministan sadarwar gwamnati ya sanya wa hannu a Accra, a babban birnin ƙasar  ta ce shugaban ƙasar ya ɗauki wannan matakin ne bayan kwamitin ya tabbtar da dalilin cire ta daga muƙaminta.

Ranar Litinin ne dai Shugaban ƙasar ya karɓi rahoton kwamitin da ya yi nazari kan ƙarar neman a kori alƙaliyar alƙalai Gertrude Araba Esaaba Sackey Torkornoo.

Maisharia Gabriel Scott Pwamang na kotun ƙolin ƙasar da ya jagoranci kwamitin ne ya gabatar da rahoton kwamitin ga shugaban ƙasar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Accra.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us