NIJERIYA
3 minti karatu
Sojojin Nijeriya 'sun kashe fiye da 'yan bindiga 100' a wasu hare-hare a Zamfara
Bisa rahoton, iya zanga-zanga ta samu a matsayin amfani da sojojin a matsayin amfani da sojojin
Sojojin Nijeriya 'sun kashe fiye da 'yan bindiga 100' a wasu hare-hare a Zamfara
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga fiye da 100. / Others
11 Agusta 2025

Sojojin Nijeriya sun kashe fiye da ‘yan bindiga 100 a wani hari ta sama da kasa da suka kai a ƙarshen mako, kamar yadda wani rahoton sa ido kan rikici da aka shirya wa Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana, wanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani a ranar Litinin.

Kungiyoyin ‘yan bindiga sun dade suna addabar al'ummomi a arewa maso yamma da tsakiyar Nijeriya, suna kai hare-hare a ƙauyuka da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa, da ƙona gidaje bayan sun kwashe dukiyoyin mutane.

Harin sojojin a jihar Zamfara mai fama da rikici ya faru ne "da sanyin safiyar" ranar Lahadi a karamar hukumar Bukkuyum, inda jiragen yaƙi tare da hadin gwiwar sojojin ƙasa suka kai farmaki kan wani taron 'yan fashi fiye da 400 a sansaninsu na daji na Makakkari.

Rahoton ya bayyana cewa harin sojojin "na iya zama martani ga hare-haren 'yan fashi da makami, musamman garkuwa da mutane, da aka yi a jihar a watan da ya gabata," yana nuna alaka tsakanin raguwar ayyukan soji a jihar da karuwar hare-haren 'yan fashi.

A ranar Juma'a, kauyen Adabka da ke Bukkuyum ya fuskanci wani hari na 'yan fashi da ya yi sanadiyar garkuwa da mazauna kauyen da kuma kashe jami'an tsaro 13.

Rahoton ya ce 'yan fashin sun shirya kai hari kan wani ƙauyen manoma lokacin da "sojojin sama da na ƙasa suka yi kwanton ɓauna a sansanin 'yan fashi, suka kashe fiye da 100."

Kakakin rundunar sojojin Nijeriya bai mayar da martani ga tambayar da kamfanin dillancin labarai na AFP ya yi masa ba.

Yaduwar Rikici

Matsalar 'yan fashi da makami a Nijeriya ta samo asali ne daga rikici kan filaye da hakkin ƙasa tsakanin makiyaya da manoma, amma yanzu ta koma wani irin ta'addanci, inda kungiyoyi ke cin karensu babu babbaka a al'ummomin karkara da ba sa samun isasshiyar kariya daga gwamnati.

Satar shanu da garkuwa da mutane sun zama manyan hanyoyin samun kudi a yankunan karkara da ke fama da talauci. Kungiyoyin kuma suna karbar haraji daga manoma da masu hakar ma'adinai na yankunan.

Rikicin yana kara ta'azzara matsalar rashin abinci mai gina jiki a arewa maso yamma yayin da hare-haren ke tilasta mutane barin gonakinsu, a wani yanayi da sauyin yanayi da kuma rage tallafin Ƙasashen Yamma suka kara dagulawa.

Duk da tura sojoji don yakar kungiyoyin 'yan ta'adda tun daga shekarar 2015 da kuma kafa wata rundunar sa-kai ta jihar Zamfara shekaru biyu da suka gabata, rikicin ya ci gaba da wanzuwa.

A watan Yuli, sojojin Nijeriya sun kashe akalla 'yan bindiga 95 a watamusayar wuta da hare-haren sama a jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us