An rantsar da kwamandan dakarun RSF Mohamed Hamdan Dagalo a matsayin shugaban gwamnatin adawa a Sudan.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, gamayyar ƙawancen da RSF ke jagoranta, ta ce Dagalo ya sha rantsuwar kama aiki a Nyala, babban birnin Jihar Darfur ta Kudu da ke yammacin Sudan.
Ta ce an rantsar da Abdelaziz Adam al-Hilu a matsayin mataimakin Dagalo, tare da mambobin majalisar shugaban ƙasa mai kujeru 13.
A ranar 26 ga watan Yuli ne gamayyar ƙungiyoyin suka sanar da kafa gwamnatin haɗin gwiwa, ƙarƙashin jagorancin Dagalo.
An sanya hannu kan yarjejeniyar siyasa a Kenya
A watan Fabrairu, RSF da wasu ƙungiyoyin ƙawancenta da dama suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar siyasa a Kenya domin kafa gwamnatin adawa a Sudan, matakin da mahukunta a Khartoum suka yi Allah wadai da shi.
A ranar 14 ga watan Agusta, Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi watsi da kafa wata gwamnati mai kama da juna a yankunan da ke hannun RSF a matsayin cin zarafi ga 'yancin kai da ƙasa da kuma yankin Sudan baki ɗaya.
Tun a watan Afrilun 2023 sojojin Sudan da dakarun RSF suke ta gwabza yaƙi wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 20,000 tare da raba aƙalla mutum miliyan 14 da muhallansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumomin yankin.
Bincike daga jami'o'in Amurka ya ƙiyasta adaɗin waɗanda suka mutu ya kai kusan 130,000.